Bayanin da Prof. Bunza ya yi a BBC da safe yana kan hanya sosai. Muna gode Allah da yab ba mu Hausa.
Wata uku da suka wuce a wani dandali wasu sun yi ta sukar wannan ranar don wandanda suka kafa ta wai ba asalin Hausawa ba ne. Ina kira ga masu raya ranar da kar su yi kasa a gwiwa. A tarihin duniya, shi harshe in ya bunkasa ba sai dan asalinsa ke raya shi ba. Haka kuma tarihin harshen Hausa shi ma ya nuna.
Ga kasidata ta bara don taya murna da harshen da ya dinke mu a wannan sashi na Afrika.
—————
HARSHEN HAUSA
1. A yau duniya ke bukin tuna Hausa
Muna gode Allah da yab ba mu Hausa.
2. A harshen bakake gaba dai ka duba
Na farko na biyu za ka kirga da Hausa.
3. Yawan yaduwa haka nan kama baki
Da saukin fadi babu yare ya Hausa.
4. Sa’annan da karbo kalaman wadansu
Ya sanya a nasa su zamto na Hausa.
5. A gun Larabawa ya karbo kidaya
Altinin, Laraba, Alhamis ka ji Hausa.
6. A gunmu Fulani ya karbo su Goggo
Da Kawu da Baffa da Yaya a Hausa.
7. Wajen Yoruba nan ya samo su keke
Da kwano, sule, har da sisi a Hausa.
8. A gun Ingilishi ya karbo su mota
Da canji, da tebur da layi a Hausa.
9. Mu gode wa harshen da yat tattaro mu
Ya maishe mu jinsi guda “Onye Hausa”.
10. Da Barno, Filato kaza Adamawa
Idan an gane mu a ce mana “Hausa”.
11. Idan an kira mu Bahaushe mu amsa
Da karfi mu ce musu tushenmu Hausa.
12. Idan dan’arewa kake kar ka musa
A Nijeriya ba ka gata ya Hausa.
13. Gama Hausa ta ba ka harshen kalami
Da danginka duk masu zance da Hausa.
14. Siyasa, kusanci, zumunci da dina
Gaba daya mun tattare inda Hausa.
15. Fa Hausa zare ne na dinke mutane
Arewa gaba dai fa turkenmu Hausa.
16. Ga mai hankali kuwa ya zama tilas
Ya taso ya caffa ya girmama Hausa.
17. Ya koya ya koyar da harshen kasarmu
Ya ce wa diya: kun ga gatanku Hausa.
18. Ku koye shi haikan ku zam sarrafa shi
Rubutu da wake ku zam yi da Hausa.
19. Ku zurfafa ilmi ku nemo a nesa
Ku kawo ku yada cikin mu da Hausa.
20. Ta’ala Aliyu yana yin du’a’i
Ka karfafa dankon zumunci na Hausa.
21. Ka karo fahimta da so har da yarda
Tsakanin mazauna kasarmu ta Hausa.
22. Ka bunkasa ilmi kaza arzikinta
Talauci ya kaura mu wala a Hausa.
23. Masifar akida, kabila, ta’adda
Ka k’are, mu zauna amana a Hausa.
24. Ga duk wanda ke da’awar raba kanmu
Ka sa ya ji kunya, ka tsarshe mu Hausa.
25. Ka karo salati bisa Annabinmu
Ka sa mu cikin mabiyansa na Hausa.
Dr. Aliyu U. Tilde
Bauchi
26 Agusta 2022
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.