Musa me zai sa
ka kasa sako masa
Sani kam tasa
masar mai lassa ya sa
a ranar Hausa?
Ni fa na fasa
Sun sa ka kasa kasa
k'asa da sulsa.
Sulusa kwansa
Kai ka sa shi ya fasa
fansa ko ransa.
'Kusa sun kwasa
Abin kai ka ce gasa
Kwarkwasa sun sa.
Tabbas mun rusa
aniyar mesa da kasa
sa dai ci dusa.
Zamu buƙasa
harshen Hausa nan kusa
da Haikun Hausa.
Daga Taskar
Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960
A Kiyayi Haƙƙin Mallaka
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.