Ticker

Ranar Hausa Ta Duniya - Tsokaci

Hausawa al'umma ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya. Da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Al'umma ce mai ɗimbin yawa, sun bazu a cikin ƙasashen Afirka, da ƙasashen Larabawa, kuma a al'adance masu matukar hazaƙa ne, aƙalla akwai sama da mutane miliyan hamsin waɗanda harshen Hausa shi ne asalin yarensu. A tarihi ƙabilar Hausawa na tattare a salsalar birane wato alkarya. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno, da kuma Fulani, a ƙarni na 19 Hausawa suna amfani da Doki ne domin yin sifiri da balaguro. Mutane kimanin sama da miliyan 50 ne ke magana da yaren hausa a Najeriya, Nijar, Arewacin Gana da kuma wasu al’umma daga yankin Kaolack a senigal har zuwa khartum dake ƙasar sudan, Asalin inda zuri'ar hausawa take shine garin Kano, Katsina da Sokoto.Asalin hausawa maguzawa ne, amma sun shafe daruruwan shekaru da karbar addinin musulunci ƙarƙashin mulkin sarakunan Haɓe, wanda suka daina yin bori da tsubbace-tsubbace, zuwan Shehu Usman Ɗan Fodio ne yasa ya kawar da mulkin wadannan sarakunan na ƙasar hausa, ta hanyar yaƙar Hausawa da sarakunansu na haɓe a Gobir, Zazzau da wasu yankunan ƙasar hausa. Wanda wannan juyin mulkin ne yasa Usman Ɗan Fodio ya kafa Daular Fulani a Hausa Fulani a ƙasar hausa, kuma Hakan yasa masarautun ƙasar hausa sun kasance a ƙungiyar Tuta ɗaya na Usman Ɗan Fodio. Hausawa suna kiran al’adunsu da al’adan gargajiya, wacce suke yi duk shekara, ko a talabijin ko Bidiyo, ko kuma aikace cikin al’amuran yau da kullum. Na daga cikin rubutun hausawa, suna yin rubutu ne asali da Ajami, rubutu ne da haruffan larabci amman a luggar hausa, kuma suna rubutawa ne a fallen takarda.
Kafar Intanet Ɗin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

Aminu Musa 
26082023
RanarHausataduniya

Post a Comment

0 Comments