Rasuwar Amali Sububu

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Rasuwar Amali  Sububu

    Amali ya rasu ranar wata Alhamis 3/11/1995, ya rasu ne a lokacin da yake da shekaru sittin da É—aya a Duniya a sakamakon wani haÉ—arin mota da ya samu bayan ya dawo daga wurin yawon kiÉ—insa, sun fito ne daga wani Æ™auye da ake kira Gangara wani Æ™auye na cikin yankin Isa ta cikin jihar Sakkwato. An ce sun shigo motar haya ne har da wata ‘yarsa wadda take aure a can ta biyo su ne domin ganin gida, a lokacin ne har ya karÉ“i É—anta wato jikansa ya riÆ™e. An ce a cikin wata mota a-kori-kura ne, lokacin da haÉ—arin zai faru sai É—ai ta ji ya ce riÆ™a É—anki-riÆ™a É—anki, tana riÆ™awa kuwa sai ya diro daga cikin motar ya faÉ—o! Allahu akbar! A sakamakon wannan ne ya cika. Ina roÆ™on Allah ya gafarta masa kurakuransa, amin.

    Daga cikin yaran Amali Abu Amali (ƙanensa) shi ne ya jagoranci tawagar kiɗan bayan rasuwarsa, wanda shi ma bai yi doguwar gora ba, ya rasu a ranar Alhamis 15 ga watan Rajab 1440 A.H. wanda ya yi daidai da watan Janairu 2019. Tun wancan lokacin har yanzu babu wani wanda ya sake jagorantar tawagar waƙar, amma dai ba a ɗebe tsammanin nan gaba a sami wani daga cikinsu ya ɗauka ba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.