Ticker

Rakumin Daji

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Raƙumin Daji

A garin Tsabre yake sunansa Musa mutumen gidan maƙera a ƙaramar hukumar Sabonbirni ta jihar sakkwato, Musa ya shahara ga noma sosai don haka Amali ya yi masa waƙarsa.

 

  G/Waƙa : Na taho in gaisai,

: Ya aika man,

   : Raƙumin daji,

: Bai zanna ba.

 

  Jagora: Na taho in gaisai,

: Ya aika man,

   : Raƙumin daji,

: Bai zauna ba.

 ‘Y/Amshi: Na taho in gaisai,

: Ya aika man,

   : Raƙumin daji,

: Bai zanna ba.

 

           Jagora: Musa ɗan Isah.

  ‘Y/Amshi: Noma sabo,

 

     Jagora: Ganɗo[1] mai tsaida ruwa.

     ‘Y/Amshi: Ɗanɗan Kande.

 

     Jagora: Gurbi mai ɗauke ruwa.

     ‘Y/Amshi: Ɗanɗan Kande.

 

     Jagora: A kai ni Tsauren sarki.

     ‘Y/Amshi: Musa na can.

 

       Jagora: A kai ni Tsauren sarki,

     ‘Y/Amshi: Musa na can.

 

    Jagora: Gidan maƙera an nan.

    ‘Y/Amshi: Ba samnan ɗa.

 

    Jagora: Ina ganin raggon ɗa,

: Nik kauce mai.

    ‘Y/Amshi: Saboda na san Allah ya ebe mai.

  : In gaisai,

: Ya aika man,

   : Raƙumin daji,

: Bai zanna ba.x2

 

    Jagora: Musa ɗan Isah.

    ‘Y/Amshi: Noma sabo.

 

    Jagora: Goje raƙumi kaka sai man.

: Shi nir roƙa.

    ‘Y/Amshi: Kai a sai ma doki,

: Shi ad daidai.

 

    Jagora: Goje raƙumin yaka sai man,

   : Shi nir roƙa.

    ‘Y/Amshi: Kai a sai ma doki,

: Shi ad daidai.

 

    Jagora: Ko ya sai man honda[2].

    ‘Y/Amshi: In hau rairai[3].

 

    Jagora: Ko ya sai man besfa.

    ‘Y/Amshi: In hau da ita,

  : In gaisai,

: Ya aika man,

   : Raƙumin daji,

: Bai zanna ba.

    

    Jagora: Na gaida Garba Garba Dauran,

    ‘Y/Amshi: Ya aika man,

: Ra ƙumin daji,

   : Bai zanna ba.

 

    Jagora: A kai ni Tsauren Sarki,

    ‘Y/Amshi: Musa na can.

 

    Jagora: Isah ka kai ni Sakkwato birni.

    ‘Y/Amshi: Domin manzo.

 

    Jagora: Sakkwato birnin Shehu.

    ‘Y/Amshi: Lalle[4] Jatau.

 

    Jagora: Gusau ta malan Sambo.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

 

    Jagora: Allah kai ni Kaduna.

    ‘Y/Amshi: Domin Manzo.

 

    Jagora: Allah kai ni Habuja.

    ‘Y/Amshi: Domin Manzo.

 

    Jagora: Yaro man kaza ne.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau[5].

 

    Jagora: Rana ta yi ya narke.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

 

    Jagora: Hanƙurin wuta sai ƙarhe.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

 

    Jagora: Wata tahiya sai mota.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

 

    Jagora: Amali mai ciki cike da kiɗi.

    ‘Y/Amshi: Ɗanɗan Dije.

 

    Jagora: Amali mai akwatin waƙa.

    ‘Y/Amshi: Ɗanɗan[6] Dije.

 

    Jagora: Mai cikin da yac cika da kiɗi.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

    Jagora: Gaban ga duk launi ne.

    ‘Y/Amshi: Lallai Jatau.

 

    Jagora: Cikin ga duw waƙa ce.

    ‘Y/Amshi: Lallai Jatau.

 

    Jagora: Ka ji abin da ni iya nis saba.

    ‘Y/Amshi: Lallai Jatau.

 

Jagora: Akawai kiɗin a kwai kuma

: waƙa.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

 

    Jagora: Noma dai karen gida yas sace.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

 

    Jagora: Ko shi ko muna iyakan namu.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

  : In gaisai,

: Ya aika man,

   : Raƙumin daji,

: Bai zanna ba.

    Jagora: A gaida Binta mai kasa marsa[7].

    ‘Y/Amshi: Ta kyauta[8] man.

 

    Jagora: Binta tsohuwa na gode.

    ‘Y/Amshi: Ta kyauta man.

 

    Jagora: Bagobira bisije.

    ‘Y/Amshi: Ta kyauta man.

 

    Jagora: A’i Buzuwa na gode.

    ‘Y/Amshi: Ta kyauta man.

 

    Jagora: Da Shehu baka kwana daji.

    ‘Y/Amshi: Ya kyauta man.

 

    Jagora: Da Shehu baka kwana daji.

    ‘Y/Amshi: Ya kyauta man.

 

    Jagora   : Dogo mai ganin ƙulewah[9]

: hanya.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

 

    Jagora: Dogo mai ganin iyakah hanya.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

 

    Jagora: Inji mutan Shagamu.

    ‘Y/Amshi: Lalle Jatau.

  : In gaisai,

: Ya aika man,

   : Raƙumin daji,

: Bai zanna ba.

 

    Jagora: Ina su mai kasa dawa,

    ‘Y/Amshi: Ya gode mai,

  : In gaisai,

: Ya aika man,

   : Raƙumin daji,

: Bai zanna ba.

 

    Jagora: Musa ɗan isah.

    ‘Y/Amshi: Noma sabo.

 

    Jagora: Ganɗo mai tsaida ruwa.

    ‘Y/Amshi: Ɗanɗan kande.

    Jagora: Ganɗo mai tsaida ruwa.

    ‘Y/Amshi: Ɗanɗan kande.

  : In gaisai,

: Ya aika man,

   : Raƙumin daji,

: Bai zanna ba.



[1]  Wani abu da ake tare/keɓe ruwa a rafi ko lambu..

[2]  Mashin ne na hawa, wanda ake tafiye-tafiye da shi.

[3]  Yashi.

[4]  Haka ne.

[5]  Ana yi wa Amali laƙabin Jatau ne saboda farar fatarsa.

[6]  Ɗa

[7]  Goro fari, wato tana sayar da goron ne ta hanyar kasawa ba zaɓi ɗaiɗai ba.

[8]  Bayar da kyauta.

[9]  Ƙarshe.

Post a Comment

0 Comments