Salau Na Maimuna

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Salau Na Maimuna

    Salau na Maimuna mutumen garin Ma’azawa ne, riÆ™on Batamna a Æ™aramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Noma ne aikinsa don har ya yi bukin dubu, Amali ya yi masa waÆ™ar ne saboda shaharar tasa.

     

    G/Waƙa : Wuce maza bisa noma,

    : Kulkin horon jema,

    : Na Sada ka yi ma aikin,

    : Gona jiÉ—am maiki.

     

          Jagora: Wuce maza bisa noma,

    : Kulkin horon jema,

    : Na Sada ka yi ma aikin,

    : Gona jiÉ—am maiki.

         ‘Y/Amshi: Wuce maza bisa noma,

       : Kulkin horon jema,

    : Na Sada ka yi ma aikin,

    : Gona jiÉ—am maiki.

     

        Jagora: Salau na Maimuna,

        ‘Y/Amshi: Allah ya hore ma aiki.

     

        Jagora: Mijin Damore da Tcito,

        ‘Y/Amshi: Zango[1] zaÉ“en Allah.

     

         Jagora: Mijin Damore da Tcito.

          ‘Y/Amshi: Zango zaÉ“en Allah.

     

       Jagora: Wani miki ya warke,

       ‘Y/Amshi: Wani miki[2] ta tashi.

     

       Jagora: Wani Anne ya kwanta.x2

       ‘Y/Amshi: Wani Anne ya tashi.x2

     

       Jagora: Su wane ba su da aiki,

       ‘Y/Amshi: Sai dai kabrab bashi.

    : Wuce maza bisa noma,

       : Kulkin horon jema,

    : Na Sada ka yi ma aikin,

    : Gona jiÉ—am maiki.

     

       Jagora: Ku dai jiddun[3] bashi,

       : Ku dai jiddun bashi,

       ‘Y/Amshi: Sai bashi ya ci ku.

       : Wuce maza bisa noma,

       : Kulkin horon jema,

    : Na Sada ka yi ma aikin,

    : Gona jiÉ—am maiki.

     

       Jagora: An sai ragon suna,

       : An koma an sai sa,

    : Kuma dai ba ko sisi,

    : Hag geron an iba,

    : Kuma dai ba ko ahu[4].

       ‘Y/Amshi: GoÉ—iya aka dubi,

    : Ta kai jikka ukku.

    : Wuce maza bisa noma,

       : Kulkin horon jema,

    : Na Sada ka yi ma aikin,

    : Gona jiÉ—am maiki.

     

       Jagora: Gona ce nis shikke,

       : Yad duÆ™a yan nome,

       : Nik koma wajjen can,

       : Ni iba nis sara,

       : Yad duÆ™a yan nome,

       : Nik koma wajjen nan,

       : Ni iba nis sara,

       : Yak koma yan nome.

       ‘Y/Amshi: Abin da kai mani,

    : Aikin noma bai kai can ba.

    : Wuce maza bisa noma,

       : Kulkin horon jema,

    : Na Sada ka yi ma aikin,

    : Gona jiÉ—am maiki.

     

       Jagora: Kulkin horon jema,

       : Na Sada ka yi ma aikin,

       : Gona shiÉ—am maiki.

       ‘Y/Amshi: Wuce maza bisa noma,

       : Kulkin horon jema,

    : Na Sada ka yi ma aikin,

    : Gona jiÉ—am maiki.



    [1]  Wani irin gero ne mai doguwar zngarniya.

    [2]  Ciwo/ rauni.

    [3]  Koyaushe.

    [4]  Kwabo da É—ari kenan, abin nufi dai ba a biya kuÉ—I ba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.