Ticker

Salihu Mai Buhu

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Salihu Mai Buhu

 G/ Waƙa: Mazan jiran damana sale,

: Salihu Maibuhu, Sale jan zaki.

 

  Jagora: Ai noman dawa ne ga jan zaki,

: Salihu Maibuhu Sale jan zaki,

: Dodo mai kuɗi,

: Mazan jiran damana Sale

: Salihu Maibuhu Sale janzaki.

 

  Jagora : Ai Gyalange akwai manoman da,

: Amma ba kamas Sale Ɗan Mamman,

: Salihu Maibuhu maigidana ne,

: Gayari akwai manoman da yay yaɗa,

: Amma ba kamas Sale Ɗan Mamman,

: Salihu Maibuhu maigidana ne.

 

  Jagora : Tambuwal akwai manoman biɗad dawa,

: Amma ba kamas Sale Ɗan Mamman,

: Salihu maibuhu maigidana ne,

: Ai Salihu Maibuhu maigidana,

: Daji ba kasada mai bada mamaki,

: Mai noman dawa bai ga rana ba,

: Ai na sanya matan gidan Sale,

: Na ce mai gadi ina Sale,

: Salihu mai buhu na wurin aiki.

 

 Jagora : Ku kai mu ga gonar Sale Jan zaki,

: Ketare godabe[1] Yamma tai dai-dai,

: Ko ba tambaya kig ga gonatai,

: In dai kig ga gonasshi ke gane,

: Ai tsattsaf wuri babu gona kamar ta shi,

: Ƙi gudu sa gudu sale jan zaki,

: Mai noman dawa ne da labara,

: Na dai roƙi sarkin da as sarki,

: Malikil mulki Lillahi ya  ba ni,

: Man tasha’u Lillahi na roƙa,

: Sarkin nan da ba’a san zaginai ba,

: Sarkin nan da bai mantuwa ba ne,

: Bai haihwa ba,

: Balle a haihe shi.

: Bai yara ba,

: Balle a yare shi.

 

Jagora : Malikil mulki mai magani Allah,

: Sarkin jinƙai ruwa inda bayi nai,

: Allah ka taimaki mai buhu sale Jan zaki,

: Ai ka bashi abinda duk Sale yan nema,

: Gumu munata guga da ɗanlisu[2],

: Ni daga wanga burtattki dangi.



[1]  Titi/hanya.

[2]  Sheɗan kenan wanda yakan shagaltar da mutane.

Post a Comment

0 Comments