𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, ance mace in tana sa yatsa
agabanta yana da illa to ya matsayin yake in mijinta ne yake sa mata. Kuma ance
idan mace ta biyawa kanta bukata yana jawo mata fitan tsutsotsi, in ya kasance
mijinta ne yake biyamata ta hanyar wasa da ita har ta fitar da maniyyi ba tare
daya sadu da ita ba, shin zata iya kamuwa da matsalar itama?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumussalamu warahmatullah.
Biyawa kai bukata (istimna'i) haramun ne bisa
nassin Alƙur'ani
mai girma. Allah Maɗaukakin
Sarki yana fadar siffofin bayinsa muminai mutanen kirki, sai ya ce:
وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ
Bayin Allah nagari Sune waɗanda dangane da farjinsu suke kiyayeshi.
(Suratul Mũminun 5)
إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ
Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen
dãmansu suka mallaka (kuyanginsu) to lalle sũ bã waɗanda ake zargi ba ne. (Suratul Mũminun 6)
فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ
Sabõda haka Duk wanda yanemi wata hanya ta biyan
bukatar sha'awarsa saɓanin
matarsa ko baiwarsa, toh shi yana cikin masu ketare iyakokin Ubangiji. (Suratul
Mũminun 7)
Sannan kuma biyawa kai bukata (Istimna'i) yana iya
janyo miki matsaloli ta fuskar lafiyarki. Kamar daskarewar maniyyi, ciwon mara
mai tsanani, rikicewar tunani, ciwon makanta, rikicewar jinin haila, fitar tsutsotsi
daga gabanki da sauransu.
Amma mijinki zai iya yi miki Ma'ana ya sanya
hannunsa yayi miki wannan wasa da farjin naki kodai atsakiyar lokacin da kuke
cikin jima'i ko kafin ku fara da kuma bayan kun gama, Kema kuma ya halatta kiyi
masa wasa da al'aurarsa. Malamai sunyi cikakken bayani akan ilmin jima'i da
yadda ake yinsa. Don karin bayani aduba IT HAFUS SADATIL MUTTAƘEEN na lmam alzabidy IHYA U ULUMID DEEN na
lmamul gazaly acikin kitabu adabin Nikahi.
Saboda haka idan mijinta ne yake mata hakan, yana
motsa mata babbar sha'awarta, ta yadda dukkan wata ni'ima da take tare da ita
zatayi waje, kuma ba mamaki daga bayan wannan wasannin zai nemeta (saduwa).
Amma idan ita ce da kanta take gamsar da kanta
haka, ba yadda zaiyiwu wannan maniyyin da sauran duk wata ni'imarta ta fita
waje, dole ne sai wata ta tsaye mata a gabanta, ta yadda wannan sauran da ya
tsaye mata, shi ne zai zame mata damuwa, mararta tana ciwo, kanta yana ciwo,
tsutsotsomi suna fita daga gabanta da dai sauransu.
Sannnan yana daga cikin irin hikimar mazan da basa
iya gamsar da matayensu, kafin kwanciyar Aure, suna amfani da wannan mathod ɗin ta yadda mace zata sami gamsuwa, sannan
kuma sai ya nemeta ɗin in
Shã Allahu.
Amma namiji baya wuce mijti 5 akan mace, shima zai
iya haddasa mata irin wannan damuwar.
Allah ta'ala yasa mudace
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.