Sardauna Ɗan Muhammadu

    Sardauna Ɗan Muhammadu

    Rubutawa: Umar S Ahmad (Chairman)

    Ba a kai maka ƙarya,

    Kana ba a kai maka wargi,

    Kwaj ja da kai jidali  ya same shi. 


    Amshi: Ubangijin ja gaba,

    Sardauna ɗan Muhamman Jikan Garba.


    Uban Zagi jikan Usmanu,

    Gohe ruwa mai wankin dauɗa.×2


    Ya iya Mota ƙwarai na Nasiru Ɗanmagyazo,

    Tsuntsu mai niyyat tashi.×2


    Amshi: Ubangijin ja gaba,

    Sardauna ɗan Muhamman Jikan Garba.


    Ɗan Hamza ka hi gonag gado,

    Kai ka ba mutun Doki,

    Da tufafi na ƙwaƙƙwarai tcadaddi,

    Randa yag ga dama,

    Sai ya yi kyauta da fan ɗari ba a tantance ba.


    Amshi: Ubangijin ja gaba,

    Sardauna ɗan Muhamman Jikan Garba.


    Ba a haye maka barde,

    Kana ba a hau maka ƙarya,

    Kwaj ja da kai jidali...

    Amadu kwaj ja da kai jidali ya same shi.


    Amshi: Ubangijin ja gaba,

    Sardauna ɗan Muhamman Jikan Garba.


    Ƙwairo mai ƙera waƙa,

    Ga Ƙwairo mai lasifika,

    Amman ya yi min jawabi,

    Sai nic ce Daudu ƙara launi,

    Kai haba Zacin kiɗi ku sa hwasali,

    In dai kun ka lissahwa,

    Sannan in ɗauka,

    In wallahwa in kai gun Mota.


    Amshi: Ubangijin ja gaba,

    Sardauna ɗan Muhamman Jikan Garba.


    Garba Gumel!

    Da kai aka dibarar ɗaukaw waƙa.


    Ubangijin jagaba...


    Garba Gumel!

    Da kai aka dibarar ɗaukaw waƙa.


    Amshi: Ubangijin ja gaba,

    Sardauna ɗan Muhamman Jikan Garba.


    Zuwan da kay yi Sakkwato Gohe,

    Wurin bikin Sakandaren Lardi,

    Mutanen Sakkwato na murna,

    Ba a gajiya da ganin ka,

    Balle ƙasaw waje,

    Shi Amadu ko na arewa kullum baƙo ne,

    Martaba' Usmanu garai,

    Inda yan nuhwa dun na murna.


    Amshi: Ubangijin ja gaba,

    Sardauna ɗan Muhamman Jikan Garba.


    Shugaban Nauzan Najeriya,

    Na Audu giwa sha masu,

    Gohe uban Mamman...

    Amadu! Gohe uban Mamman Nasir.


    Ubabgijin jagaba...


    Sarkin Zazzau Aminu yai...

    Sarkin Zazzau Aminu yai tarɓa mai kyawu.


    Daga Samuru an ka jero motoci,

    Hab bisa masabki nai,

    Da ƴan Say'ikul, da ƴan Basukur,

    Mutane naƙ ƙasa an jera zak kyau!

    Dawakin ƙwarai na gargajiya,

    Waɗanda an ka ɗauro ma sirdi.


    Amshi: Ubangijin ja gaba,

    Sardauna ɗan Muhamman Jikan Garba.


    Marigayi Alh. Musa Ɗanƙwairo


    Rubutawa: Malam Umar S Ahmad
    11-8-2020

    Daga:
    Zauren Makaɗa Da Mawaƙa

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.