Ticker

Sarkin Hura Audu Ɗan Kadi

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Sarkin Hura Audu Ɗan Kadi

 

 G/Waƙa: Mu zo gida,

: Nai mu gaishe shi,

: Sarkin hura,

: Audu Ɗan Kadi.

 

Jagora: Mu zo gida,

: Nai mu gaishe shi,

: Sarkin hura,

: Audu Ɗan Kadi.

‘Y/ Amshi: Mu zo gida,

: Nai mu gaishe shi,

: Sarkin hura,

: Audu Ɗan Kadi.

 

 Jagora: Shi dai bashi son,

: Kassuwa Audu,

: Kullun gida…

‘Y/ Amshi: Nai shiga daji,.

: Mu zo gida,

: Nai mu gaishe shi,

: Sarkin hatci,

: Audu Ɗan Kadi.

 

  Jagora: Badarawa akwai,

: ‘Yan mazan noma,

 ‘Y/ Amshi: Allah kaɗai,

: Shi ya hisshe shi.

: Mu zo gida,

: Nai mu gaishe shi,

: Sarkin hatci,

: Audu Ɗan Kadi.

 

  Jagora: Akawal danda,

: Shi Audu yab ba ni,

‘Y/ Amshi: Mai ba mu ge,

: Ro ina damu,

: Mu zo gida,

: Nai mu gaishe shi,

: Sarkin hatci,

: Audu Ɗan Kadi.

 

  Jagora: Shi bashi kyau,

: Ta da jan doki,

: Akawal,

 ‘Y/ Amshi: Danda shi Audu yab ba mu.

: Mu zo gida,

: Nai mu gaishe shi,

: Sarkin hatci,

: Audu Ɗan Kadi.

 

Jagora: Audu na Garba,

: Mai tambarin aiki.x2

 ‘Y/Amshi: Tambarin aiki.x2

: Mu zo gida,

: Nai mu gaishe shi,

: Sarkin hatci,

: Audu Ɗan Kadi.

 

  Jagora: Shi mai gudu,

: Audu yab ba ni,

 ‘Y/ Amshi: Allah ya ƙa,

: Ra ma jan zaki,

 

  Jagora: Yaro gahwara,

: Audu na daji,

: Shi bai zama,

‘Y/ Amshi: Sai wurin aiki.

 

  Jagora: Kullun,

‘Y/Amshi: Bai zama.

: Sai wurin aiki.

Post a Comment

0 Comments