Sarkin Noma Ummaru

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Sarkin Noma Ummaru

    Ummaru sarkin noma ne na garin Kalgo a cikin Æ™aramar hukumar Sabonbirni ta jihar Sakkwato. Manomi ne wanda ya tara albarkar gona, don haka Amali  Sububu ya waÆ™e shi.

    G/Waƙa : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

     

       Jagora: Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

        ‘Y/Amshi: Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

     

      Jagora: Da munka shigo Kalgo,

    : Tunda hantci,

    : Kartau[1] na gonatai,

       ‘Y/Amshi: Shi ko Jatau yar rage mai,

       : Yal lunhwasa nan,

      : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

             Jagora: Da munka shigo Kalgo,

       : Tunda hantci,

       : Kartau na gona tai, 

        ‘Y/Amshi: Shi ko Jatau yar rage mai,

       : Yad dakanta nan,

      : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

     

       Jagora: Na gode ma,

    : Garba karo,

       : Ban raina ma ba,

        ‘Y/Amshi: Garba yau da hura tai,

       : Mun ka kara,

    : Ga nono ta sha,

      : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

     

       Jagora: Garba karo,

    : Godiya yakai,

       : Garba maji daÉ—in sarki.

        ‘Y/Amshi: Yau da hura tai mun kara,

       : Ga nono zalla,

      : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

     

       Jagora: Yak kwaÉ“i,

        ‘Y/Amshi: Ta ima daka,

    : Lalayya[2] an nan,

     

       Jagora: Yak kwaÉ“i,

    : Ta ima daka,

        ‘Y/Amshi: Kindirmo[3] an nan,

     

       Jagora: Garba ‘yak kwaÉ“i ta,

        ‘Y/Amshi: Ima daka,

    : Lolayya[4] an nan,

     

       Jagora: Ko da na cika,

    : Bakina da dawo[5],

        ‘Y/Amshi: Sai susab baya,

      : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

     

       Jagora: Jikan liman da BaÆ™o,

       : ÆŠan Hawwa da Alhaji,

        ‘Y/Amshi: Bukar magabata babu kure,

       : Garba MajidaÉ—i,

      : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

        

      Jagora: Maza ku yi noma,

       : Tara dame,

    : Shi ak kyan ku maza.

       ‘Y/Amshi: Da in ga manomi bai da dame,

       : Shi ab bulloso[6],

      : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

     

      Jagora: Maza ku yi noma,

       : Ku yi sutura,

       : Kuma ku aje gero.

     

       ‘Y/Amshi: Da in ga manomi baida dame,

       : Shi as shaÉ—ari,

      : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.

     

      Jagora: Ni da goÉ—iya tay yi magana,

       : Mamaki niy yi,

       : Tac ce mani noma abu ne,

       : Jatau mai Æ™warya,

       : Tac ce kai dai ad da dame?

    : Shin ko ko ni dai?

       : Nic ce ke dai ad da damen nan,

    : Ki zama tamna,

    : Tac ce Kartau ya yi guza,

    : Bai zan hwanko[7] ba,

        ‘Y/Amshi: Gidan Ummaru an tara dame,

    : Ya ebe haushi.

      : Koma gona,

    : Gak ka sake,

       : Noma sabo nai,

       : Sarkin noma,

    : Ummaru mai,

       : Albarkar hannu.



    [1]  Manomi

    [2]  Lumui-lumui, wato iya daka da kyawo.

    [3]  Kamantawa ya yi a nan, kindirmo nono kenan wanda aka burke tare da mansa, ba a Æ™ara ruwa ba.

    [4]  Daka mai kyawo da Æ™warewa.

    [5]  Gayan fura.

    [6]  Aikin banza.

    [7]  Wanda bai da arziki/samu.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.