Sarkin Noman Dange

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Sarkin Noman Dange

 G/Waƙa: Gwada[1] ma raggo kamun galma,

: Sarkin noma lokal Dange Ummaru.

 

Jagora : Allah gyara,

‘Y/ Amshi: Uban giji sarki mai gobe.

 

Jagora: Gwada[2] ma raggo kamun galma.

 ‘Y/Amshi: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Gwada ma raggo kamun galma,

: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Gwada ma raggo kamun galma,

: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Gwada ma raggo kamun galma.

 

Jagora: Dur ran maza ka kai gwarzo,

: Gidan ku ba raggo ba wohi.

‘Y/Amshi: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Hantsi ƙarin gayya.

 

Jagora: Ɗan Mamman yunƙura da ƙarhi.

‘Y/Amshi: Kasan da raggo duk bai ƙwazo.

 

  Jagora: Ɗan Mamman yunƙura da ƙarhi.

‘Y/Amshi: Ka tabbata raggo bai ƙwazo.

 

Jagora: Inji kuwaru yana cewa.

 ‘Y/Amshi: Noman kwabri ƙaton wohi,

: Sarkin noma lokal Dange,

: Ummaru Hantsi ƙarin gayya,

 

 Jagora: Inji kuwaru yana cewa.

  ‘Y/Amshi: Noman kwabri ƙaton wohi,

: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Hantsi ƙarin gayya,

: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Hantsi ƙarin gayya.

 

 Jagora: Muttala Amadu na gode ma.

  ‘Y/Amshi: Kulakka yai man hairan ƙwazo.

 

 Jagora: Muttala Amadu na gode ma.

  ‘Y/Amshi: Kulakka yai man hairan ƙwazo.

 

 Jagora: Hadda Haruna Daura na gode mai.

  ‘Y/Amshi: Kulak ka yai man halin ƙwazo.

 

Jagora: Haruna Daura ya kyauta man.

 ‘Y/Amshi: Kulak ka yai man halin ƙwazo.

 

Jagora: Baba Maniru yai man bajinta.

 ‘Y/Amshi: Kulak ka yai man halin ƙwazo.

 

Jagora: Baba Maniru yai man bajinta.

 ‘Y/Amshi: Kulak ka yai man halin ƙwazo.

 

Jagora: Ɗan goje Kaka wannan ya kyauta man.

 ‘Y/Amshi: Kulak ka yai man halin ƙwazo.

 

 Jagora: Kaka wannan ya kyauta man.

  ‘Y/Amshi: Kulak ka yai man halin ƙwazo.

 

  Jagora: Isah kaka na gode mai.

‘Y/Amshi: Kulak ka yai man halin ƙwazo.

 

  Jagora: Amadu Kwatta na gode mai.

‘Y/Amshi: Kulak ka yai man halin ƙwazo.

 

Jagora: Amadu Kwatta na gode mai.

 ‘Y/Amshi: Kulak ka yai man halin ƙwazo.

 

  Jagora: Na Sambo darni matasa saura maza.

‘Y/Amshi: Su barma yaƙin huɗa,

: Sarkin noma lokal Dange,

: Ummaru hantsi ƙarin gayya.

 

 Jagora: Na Sambo darni matasa saura.

  ‘Y/Amshi: Maza su bar maka yaƙin huɗa.

 

  Jagora: Na Sambo darni matasa saura.

  ‘Y/Amshi: Maza su bar maka yaƙin huɗa.

 

  Jagora: Na Sambo darni matasa saura.

‘Y/Amshi: Maza su bar maka yaƙin huɗa.

 

  Jagora: Na Sambo darni matasa saura.

  ‘Y/Amshi: Maza su bar maka yaƙin huɗa.

 

  Jagora: Na Sambo gyara Allah gyara.

‘Y/Amshi: Uban giji sarki mai gobe.

 

  Jagora: Sarkin ganye na gode mai.

‘Y/Amshi: Kulakka  yai man halin ƙwazo.

 

  Jagora: Sarkin ganye na gode mai.

‘Y/Amshi: Kulakka  yai man halin ƙwazo,

: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Hantsi ƙarin gayya.

 

  Jagora: Sarkin ganye lokal.

‘Y/Amshi: Kulakka  yai man halin ƙwazo,

: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Hantsi ƙarin gayya.

 

  Jagora: Muttala Amadu na gode mai.

  ‘Y/Amshi: Kulakka  yai man halin ƙwazo.

 

  Jagora: Muttala Amadu na gode mai.

‘Y/Amshi: Kulakka  yai man halin ƙwazo.

 

Jagora: Malan Sani  na gode mai.

‘Y/Amshi: Kulakka  yai man halin ƙwazo.

 

Jagora: Malan Abubakar shi na gode mai.

‘Y/Amshi: Kulakka  yai man halin ƙwazo,

: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Hantsi ƙarin gayya.

 

  Jagora: Malan Tukur shi ya kyauta man.

‘Y/Amshi: Kulakka  yai man halin ƙwazo.

 

Jagora: Na Hassan Tukur shi na gode mai.

‘Y/Amshi: Kulakka  yai man halin ƙwazo,

: Sarkin noma lokal Dange Ummaru,

: Hantsi ƙarin gayya.

 

  Jagora: Uban giji sarki mai gobe.

  ‘Y/Amshi: Wahabu gyara Allah gyara.

 

  Jagora: Wahabu gyara Allah gyara.

‘Y/Amshi: Uban giji sarki mai gobe,

: Sarkin noma lokal Dange

: Ummaru Hantsi ƙarin gayya.

 

  Jagora: Sai da kai aka ƙullin[3] noma,

: In bada kai ba a hwasa zaune.

‘Y/Amshi: Sarkin noma lokal dange ,

: Ummaru Hamtsi ƙarin gayya,

: Sarkin noma lokal dange,

: UmmaruHamtsi ƙarin gayya,

: Sarkin noma lokal dange,

: UmmaruHamtsi ƙarin gayya,

: Sarkin noma lokal dange Ummaru,

: Hamtsi ƙarin gayya.



[1]  Nunawa.

[2]  Nunawa.

[3]  Shirin/Maganar.

Post a Comment

0 Comments