Sarkin Noman Garin Magaji

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

     Sarkin Noman Garin Magaji

    Sunan sarkin noman Garin Magaji shi ne Majiro, Garin Magajin wani gari ne a cikin Æ™aramar hukumar mulkin Sabon birni ta jihar Sakkwato.    

       

    G/Waƙa : Da hanzarin noma nis san ka,

       : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

       : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

     

    Jagora : Ban hana yaro ba sai wuya ta,

       : hana mashi,

       : Rana tana da zahi.

    ’Y/Amshi  : In ba a daure ba ba ka jin,

       : Damma sun zo gida.

       : Da hanzarin[1] noma nis san ka,

       : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

       : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

      

    Jagora : Tadana[2] baƙin ka Majiro,

    ’Y/Amshi : Tahi sake dabara Amali,

       : Na gumza garkar gida,

       : Da hanzarin noma nis san ka,

       : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

       : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

        

     Jagora : Allah ya maida aure aure,

       : Allah ka bar ma kowa É—a nai,

       : DuÉ— É—an da kag ga an haihwa ma,

    : In dai akwai yawancin rai,

    : Sai ka ga É—anai shi zan jiÆ™an ka.    

    ’Y/Amshi : Duw wanda kag ga yai jika,

      : Ya Tsuhwa[3] shi.

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

     

     Jagora : Gwazza ku Æ™ara aure,

     ’Y/Amshi : Kaw wata rana a shirga[4] baÆ™i,

         : Ba matan tuwo,

            

     Jagora : Lalle gwarza[5] ku Æ™ara mata,

     ’Y/Amshi : Kaw wata rana a shirga baÆ™i,

      : Ba matan tuwo,

            

     Jagora : Mai mata guda ina kad darÉ“e,

      : Kazan kamar abokin gauro,

      : Dur randa ba ta nan,

     ’Y/Amshi : Ko waz zaka shiyak ka,

      : Ba ka cewa É—ebo mai ruwa,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

     

     Jagora : Ta tahi ta bag gida da kewa,

      : Ranan ko ka sawo dawo,  

    ’Y/Amshi : Damu sai an yi mai,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

         : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

         : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

     

    Jagora : Ban hana yaro ba,

          : Sai wuya ta hana mai,

         : Rana tana da zahi,

       ’Y/Amshi : In ba a daure ba,

         : Ba ka jin damma sun zo gida,

             

         Jagora   : Sarkin noman Garin Magaji,

      ’Y/Amshi : Kai muka dubi kamar,

           : Watan sallah in ya hito,

         : Da hanzarin  noma nis san ka,

         : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

         : Mu gaida Kartau mai gulbin hura,

       

    Jagora : Ga sarkin noma za shi gona,

          : Ga jakki goma sha biyar ya koro,

          : Duk kowane da taki,

         : Ga kwando ya ciko da taki,

          : Ya É—auka ya azo ga kainai,

          : Ga kalme ya saÉ“o da gitta,

        : Ga kwashe ya riÆ™o ga hannu,

        : Ga juji ya lago gaba nai,

        : Ga juji ya lago ga baya,

        : Ni dai na dabugo[6] gaba nai,

        : Ban san kan inda ya nuhwa ba,

        : Kuma nij jirkito shi baya,

        : Ban san kan inda yan nuhwa ba,

        : Kuma nij jirkito...,

        : Dub bai tanka ba ya yi shu,

        ‘Y/Amshi    : Duk ya cika hanya,

        : Kama da tantebur ta yo hawa.

        : Da hanzarin noma nis san ka,

         : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

                : Mu gaida Kartau[7] mai gulbin hura.

    Jagora     : Sullata nome karkara,

     ‘Y/Amshi     : Tahi duÆ™e ga daji,

        : Irin shanun nan hwarhwaru.

        : Da hanzarin noma nis san ka,

        : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

        : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

     

    Jagora      : Dojindo mai dakan Æ™asa,

        ’Y/Amshi     : Tahi gilme[8] ga daji,

        : Kamar ana tuÆ™in jirgin ruwa,

        : Da hanzarin noma nis san ka,

        : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

        : Mu gaida Kartau mai gulbin hura,

     

    Jagora : Rana mai sa mutun la’ari gona,

         : Aiki ya barkace mai,

         : Rana mai kai mutun ga saiÉ“i[9] daji,

         : Har rai shi É—ora gumu,

         : In dai na kai duma ga gona,

         : Gwazza cilas ku sake Hausa,

         : Ina gaba Gwazza suna biya ta,

         : Ka ga Æ™ato shina jiÉ“i,

         : Cilas ka ga Æ™ato yana huka,

         ’Y/Amshi : Cilas ka ga hancin mutum,

      : Da tarsone ya zalzalo,

         : Da hanzarin noma nis san ka,

        : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

        : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

     

    Jagora : Ban hana yaro ba,

        : Sai wuya ta hana mai,

        : Rana tana da zahi,

    ‘Y/Amshi : In ba a daure ba ba ka jin damma,

        : Sun zo gida,

        : Da hanzarin noma nis san ka,

        : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

        : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

     

    Jagora : ÆŠaukab bashi yana da ciwo,

         : Kuma ganoma[10] na da zahi,

         : Kalmen ga noma tambaÉ—aÉ—É—e,

         ‘Y/Amshi  : Kowas saba da shi,

         : Ana raina mai gaskiya,

         : Da hanzarin noma nis san ka,

         : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

         : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

     

    Jagora : Noma mun kai cikin gumi nai,

         : Bisa da zahi Æ™asa da zahi,

         : Ga yunwa ga jiÉ“i da rana,

         : Ga Gwazza sun shigo ga gona,

         : Ga mata sun taho suna dubin,

         : Wada Æ™atta ka gwabce kuyyai,

         : Abi kuyya a lukkume[11] ta,

         : Abi kuyye a sasume su,

         : A yi kuyye kamar rihewa.

    ‘Y/Amshi   : Kowace kuyya kamar gadar,

          : Mota an mulmulo,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

       

        Jagora    : Ba wada za kai ka ratsa gona,

          : Kuyye sun zan kama da Juna,

          : Ba wada zaka yi ka Æ™etare su,

    ‘Y/Amshi   : Sai ka bi raÉ“in su,

          : Ko kana samun kwana gida,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

       

        Jagora    : Ban hana yaro ba,

          : Sai wuya ta hana mai,

          : Rana tana da zahi,

         ‘Y/Amshi    : In ba a daure ba ba ka jin,

          : Damma sun zo gida,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida  rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura,

      

       Jagora     : Yaro bai san kahon-kaho ba,

          : Kuma bai san caÉ“on-caÉ“o ba,

          : Kuma bai san gumin-gumi ba,

          : A kai jubuha[12] ba ka da hatsin ci,

          : Ba kada komi cikin ruhewa[13],

          : Bisa ruwa Æ™asa ruwa,

         : Sannan ga noma bata tashi,

          : Sannan ciwon cikin,

          : Maza yake.

        ‘Y/Amshi    : Sai ka ga Æ™ato da shi da mai,

          : ÆŠakinai an yi shu,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

      

       Jagora     : Ban hana yaro ba,

          : Sai wuya ta hana mai,

          : Rana tana da zahi,

        ‘Y/Amshi    : In ba a daure ba ba ka jin,

          : Damma sun zo gida,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

      

        Jagora    : Ba wada za kai ka ratsa gona,

          : Kuyye sun zan kama da juna,

          : Ba wada zakai ka Æ™etare su,

        ‘Y/Amshi      : Sai kabi raÉ“in[14] su,

          : Ko kana samun kwana gida,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

       

        Jagora    : Ban hana yaro ba,

          : Sai wuya[15] ta hana mai,

          : Rana tana da zahi,

         ‘Y/Amshi   : In ba a daure ba ba ka jin,

         : Damma sun zo gida,

       

        Jagora    : Yaro bai san kahon-kaho ba,

          : Kuma bai san caÉ“on-caÉ“o ba,

          : Kuma bai san gumi-gumi ba,   

          : A kai jubuha ba ka da hatsin ci,   

          : Ba ka da komi cikin ruhewa,

          : Bisa ruwa Æ™asa ruwa,

          : Sannan ga noma bata tashi,

          : Sannan ciwon cikin,

          : Maza ya kai,

       ‘Y/Amshi     : Sai ka ga Æ™ato da shi da mai,

          : ÆŠakinai an yi shu,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i[16],

       : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

       

        Jagora    : Ban hana yaro ba,

          : Sai wuya ta hana mai,

          : Rana tana da zahi,

         ‘Y/Amshi   : In ba a daure ba ba ka jin,

          : Damma sun zo gida,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

      

       Jagora     : Kaya ba ginin la’arin ganwo[17],

          : Zama da macce ba tsabacci,

          : Akwai wuya akwai ban haushi,

          : Ta na yi ma abin ganganci,

          : Ka hanÆ™ure ka mai sai banza,

        : Ka hanÆ™ure takaici,  

          : In ba ka tanka ba ka ji tsoro,

     ‘Y/Amshi : In ka tanka ta É—ora ce ma tsinannen

    : maza,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

      

        Jagora    : Matar raggo kina da haushi,

          : Yunwa ta kwalkwale kin rame,  

          : Har kin bak kama da mata,

          : ÆŠan kunkurun[18] kamar na mi ya ke?

         ‘Y/Amshi  : ÆŠan kunkurun kamar biri na,

          : Tonon gujiya,

          : Da hanzarin noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

      

        Jagora    : Amali kiÉ—i babu wanda ban yi ba,

          : Bakin cin hwara dukiyata,

          : Na ci awaki da raguna da dawaki,

          : An ba mu dukiyar raÆ™umma,

          : Am ba mu hadda shanu,

          : Sauran mota a hwara sai man,

          : Komi ka ba ni duk cikin Æ™ari ne,

         ‘Y/Amshi     : Komi kab bani duk cikin Æ™ari kay yi

    : man,

          : Da hanzarin noma nis san ka.

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

      :Jagora    : Amali zuga ba wadda,

          : Ban yi ba,

          : Bakin dai tamu hwara Hausa,

      : Na sa an É—auki doguwa ta zanna,

          : Domin a tara gero,

          : Na sa an É—auki aljana an Æ™ara,

          : Domin a hau da suna[19],

          : Na sa an É—auke aljana na kauce,

          : Na bam mutun da kaya,

          : Wani ya É—auki zakuma[20] ya tushe,

          : Ta zanne zuciya tai,

          : Ni ban É—auka ba,

         ‘Y/Amshi    : Wanda yaÉ— É—auka shi ac ciki.

          : Da hanzarin[21] noma nis san ka,

          : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

          : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

       Jagora:    : Albarkacin alu mai saje,

         : Albarkacin sahabi,

         : Kartau Allah ya ba ka albarkassu,

         : Mu ma mu samu albarkassu,  

         : Kahin[22] mu cimma albarkakka,

         : Da mu da kai da sauran taro,

         : Allah ka sa muna dacewa,

      ‘Y/Amshi    : Bagudu[23] indai kana da,

         : Alheri sai mun gani,

         : Da hanzarin noma nis san ka,

         : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

         : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

     

       Jagora     : Mamman Tukur waliyin Allah,

         : Allah shi ba ka albarkatai,

         : Mu ma mu samu albarkatai,

         : Kahin mu cimma albarkakka,

         : Da mu da kai da sauran taro,

         : Allah ka sa muna dacewa,

         : In dai kana da alheri,

        ‘Y/Amshi    : Bagudu in dai kana da,

         : Alheri sai mun gani,

         : Da hanzarin noma nis san ka,

         : Taho gida rana ta hwaÉ—i,

         : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.



    [1]  Sauri

    [2]  Tanada, wato ya yi tanadin wata kyauta da zai ba baÆ™insa.

    [3]  Tsufa

    [4]  Yin abu da yawa, cikawa.

    [5]  Manoma

    [6]  Dubi na mamaki

    [7]  Suna ne na wani mutum wanda wasu suke yi masa idan su ga yana da Æ™oÆ™ari wajen noma.

    [8]  Karkace

    [9]  Yin wasu ‘yan surutai kamar sambatu

    [10]  Kodago, yin noma a gonar wani don a biya ka.

    [11]  DunÆ™ulewa, rufewa

    [12]  Lokacin yawan ruwan sama kamar watan Ogas.

    [13]  Rumbun ajiyar hatsi.

    [14]  Gefe

    [15]  Zafin rana da wahalar aikin noma.

    [16]  Idan rana ta yi Yamma har ta É“ace ba a ganinta.

    [17]  Gammo don É—aukar kaya.

    [18]  Ƙugu/kwankwaso.

    [19]  Wata tad ace ake yi idan ana son manomi ya yi fice kowa ya san shi ga maganar noma. A taÆ™aice dai ta zama ya tara kayan gona da yawa waÉ—anda ya noma.

    [20]  Sunan aljana ne.

    [21]  Wanda yake noma ba tsayawa ko yawan hutawa har ya yi aiki da yawa.

    [22]  Kafin- mawaÆ™in ya yi amfani ne da Karin harshen Sakkwatanci.

    [23]  Wanda bai tsoron wahala.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.