Ticker

Sauya Maudu’in Huɗuba Saboda ’Yan Siyasa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, ina hukuncin limamin Jumma’a yana kan yin huɗuba game da ‘Jin Tsoron Allaah’, amma ganin wani ɗan siyasa ya shigo sai ya sauka daga kan maudu’insa na ‘Jin Tsoron Allaah’, ya koma yabon wannan ɗan siyasan, tare da yi masa ‘campaign’?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

[1] Da farko dai Liman shi ne: Babban mutum, shugaba, ja-gora kuma wanda ake koyi da shi a cikin maganganunsa da ayyukansa na addini da rayuwa. Wajibi ne shi kansa ya san wannan, mabiyansa kuma su san haka. Kuma lallai ne Liman ya kare mutuncinsa da martabarsa a idon jama’a ta hanyar barin yin roƙo, ko bara, ko tumasanci ga mawadata da sarakuna da yan siyasa a fili ko a ɓoye.

Mu kuma mabiya sai mu tashi da gaske mu taimaka masa ta dukkan hanyoyin da suka kamata don tabbatar da hakan, kamar ta bayar da gudunmawarmu na kuɗi don gudanar da masallatanmu na Jumma'a da sauransu.

[2] Sannan Liman ya riƙa yi mana bayanin duk wani abin da ka iya shige mana duhu game da ayyukansa da maganganunsa, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Salam) a cikin Sahih Al-Bukhaariy ya bayyana wa Sahabbansa guda biyu da suka gan shi tare da wata mace a cikin dare, cewa: Matarsa ce Safiyyah! A ƙarshe kuma ya ƙara da cewa:

إِنَّ الشَّيْطَانَ يَجْرِي مِنِ ابْنِ آدَمَ مَجْرَى الدَّمِ

Tabbas! Shaiɗan yana gudana a jikin ɗan Adam ta magudanar jini.

Sannan mu kuma, mu riƙa yi masa kyawawan zato a cikin maganganu da ayyukansa waɗanda ba mu gane ba.

[3] Amma game da sauya maudu’in huɗuba, wannan ba matsala ba ce, tun da da ma shi Limamin ne yake rubuto, ko yake tsaro maudu’insa. Ba wani ko wasu daga cikin masallata a bayansa ne suke tsara masa ba. Don haka, idan ya ga yiwuwa ko samuwar yanayin da ta sa ya sauya maudu’in kuma sai ya sauya, wannan babu komai in Shã Allahu.

Watarana Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cikin huɗuba a masallacin Jumma’a sai wani mutum ya shigo, ya nemi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya yi addu’a, saboda halin tsanani da al’umma suke ciki na rashin ruwan sama a lokacin. A nan take sai kuwa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ɗaga hannu ya roƙi Allaah:

اللَّهُمَّ أَغِثْنَا! اللَّهُمَّ أَغِثْنَا!!

Ya Allaah! Ka ba mu ruwa! Ya Allaah! Ka ba mu ruwa!!

Manufa a nan: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya bar abin da yake yin huɗubar a kansa, a lokacin da ya ga muhimmancin abin da mutumin ya nema.

Kodayake a iya cewa, ai shi wannan limamin babu wani daga cikin musulmi da ya neme shi da ya sauka daga kan maudu’insa?

Amma za a iya amsawa da cewa: Haka ne, sai dai kuma tun da dai har shi da kansa Limamin ya ga muhimmancin yin hakan a wannan lokacin, sannan kuma dayake babu wani dalili a shari’ance da ya hana shi sauya maudu’in, ba za a hana shi yin hakan ba. Ko da kuwa dukkan mutane ko yawancinsu ko waɗansunsu ba su ga hakan ba. wallahu A'alam.

[4] Magana a kan ’yan siyasar dimokuraɗiyya kuwa: Malamai sai sun yi taka-tsantsan game da su. Amma matuƙar dai su shugabanni ne kuma musulmi, to aƙidar mu ita ce: A girmama su, kuma a mutunta su da gwargwadon irin matsayin da Allaah Taaala ya ba su, ko da kuwa fasiƙai ne, ko kuma ma azzalumai. Kar a wulaƙanta su, kar a raina su, ko a ɗauki matakin yin fito-na-fito da su. Yin hakan ya fi kama da tafarkin ’yan bidi’ar RAAFIDAH (shi’a) da KHAWAARIJ (boko-haram) ne.

Maimakon haka, sai a riƙa yi musu kyawawan addu’o’in da suka kamata, kuma a ba su haƙƙoƙinsu na biyayya, da yi musu ɗa’a a cikin abin da bai saɓa wa dokokin shari’ar Musulunci ba. Idan kuma sun danne, ko sun hana mu haƙƙoƙinmu, to sai mu bi hanyoyin da suka kamata domin neman su, kamar ta yawaita addu'o'i ga Allaah Ta'aala cewa, ya ba mu.

[5] A taƙaice dai, duk sadda Limaminmu wanda muka yarda da shi a matsayin jagoranmu a addini ya ga dacewar ya faɗi wata magana ga wani shugaba musulmi ɗan siyasar dimokuraɗiyya da muke ciki a yanzu, da kyakkyawar manufar yin nasiha, kuma da irin kalmomin da suka dace, kuma ba su kauce wa ƙaidar sharia ba, bani ganin hakan wani mummunan abu ne, in Shã Allãhu.

Amma da zai same shi a keɓe shi da shi a wani wuri don yin hakan da shi ya fi, don gudun haifar da rashin fahimta, ko samar da ruɗani a cikin mabiya.

Idan kuma hakan ba ta samu ba, sai a yi abin da ya sawwaƙa, kamar yadda Abu-Saeed Al-Khudriy (Radiyal Laahu Anhu) ya yi ga Sarkin Muslumi nasiha a fili, a masallacin Idi.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments