Shehu Na Bunguɗu

    Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    1.1.1 Shehu Na Bunguɗu

     

    G/Waƙa: Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

      Jagora: Za ni ga malan Shehu na Bunguɗu.

    ‘Y/ Amshi: Komi kac ce Daudu yi ma akai.

     

    Jagora: Tahi daji banda zaman gida

    ‘Y/Amshi: Kowa aje damma shi ka zama kurun

     

    Jagora: Ya tahi daji banda zaman gida

    ‘Y/ Amshi: Kowar rasa damma baya zama kurun.

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Ga Dauran Garba na Amadu

    ‘Y/ Amshi: Rani mai bushe irin haki.

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

     Jagora: Kowai yi muna rowa mun sani,

    : Kowai yi muna kyauta mun sani.

    ‘Y/ Amshi: Kowa nab bamu sani mukai.

     

    Jagora: Kowa yai niyyar bamu hwaɗi mukai

    ‘Y/ Amshi: Kowai niyyab bamu hwaɗi mukai.

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

    .

    Jagora: Za ni ga malan Shehu na Bunguɗu.x2

    ‘Y/ Amshi: Komi kac ce Daudu yi ma yakai.x2

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Sani Mahwara ban rena ma ba,

    ‘Y/ Amshi: Ga alheri wanda yakai muna,

    : Albarkas Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Sani Mahwara na halin girma,

    ‘Y/ Amshi: Ga alheri wanda yakai mana,

    : Albarkas Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Tahi gona banda zaman gida,

    ‘Y/ Amshi: Yanzu ga aiki dole saki sukai.

    Jagora: Ya tahi daji baya zaman gida,

    ‘Y/ Amshi: Yanzu ga aiki dole saki sukai.

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Ko ana hwari bamu bak ka zama ba.x2

     ‘Y/ Amshi: Ko hwari akai duƙa ka ta noma,x2

    : Yanzu ga aiki dole saki sukai,

     

      Jagora: Zani ga malan Shehu na Bunguɗu.x2

    ‘Y/ Amshi: Komi kac ce Daudu yi ma yakai.x2

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Yara ku ja kaya mu yi Bunguɗu.x2

    ‘Y/ Amshi: Am ce malan Shehu yana kira.x2

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Ya aje dawa ya aje gero.x2

    ‘Y/ Amshi: Ya aje naira Shehu na Bunguɗu.x2

     

    Jagora: Gaya da kuɗɗi gaya da kyawo.x2

    ‘Y/ Amshi: Gaya da ilmi Shehu na Bunguɗu.x2

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Waɗan Maru su da waɗan Gusau.x2

    ‘Y/ Amshi: Lokacin yunwa ta ƙuma, 

    : Kowar rasa damma,

    : Sai ya yi Bunguɗu.x2

     

    Jagora: Kowar rasa damma,

    : Sai ya yi Bunguɗu,

    ‘Y/ Amshi: Kowar rasa damma,

    : Sai ya yi Bunguɗu,

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Aminu Mai injin na gode.

    ‘Y/ Amshi: Alheri wanda yakai mana,

    : Albarkar Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Malan Aminu Mai injin na gode.

    ‘Y/ Amshi: Alheri wanda yakai mana,

    : Albarkar Shehu na Bunguɗu.

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

      Jagora: Tahi gona Shehu na Bunguɗu.

    ‘Y/ Amshi: Ka aje damma Shehu na Bunguɗu,

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Malan Aminu Mai injin na gode.

    ‘Y/ Amshi: Don alheri wanda yakai mani,

    : Albarkar[1] Shehu na Bunguɗu.

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Yara mu ja kaya[2] mu yi Bunguɗu.x2

    ‘Y/ Amshi: Am ce malan Shehu yana kira.x2

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

    Jagora: Zani gidanai Shehu na Bunguɗu.x2

    ‘Y/ Amshi: Komi kac ce Daudu yi ma yakai.x2

     

    Jagora: Damana da rani ba ya zama gida.x2

    ‘Y/ Amshi: Ya riƙe aiki Shehu na Bunguɗu.x2

     

    Jagora: Kullun[3].x2

    ‘Y/ Amshi: Ya riƙe aiki Shehu na Bunguɗu.

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.

     

      Jagora: In ya tahi gona Shehu na Bunguɗu.x2

    ‘Y/ Amshi: Sai in sallah ta isa zaya yi.

    : Koma gona ka biɗo hatci

    : Mai kalme Shehu na Bunguɗu.



    [1]  Saboda/domin ƙauna.

    [2]  Kayan kiɗi.

    [3]  Kowace rana.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.