Shin Kaffara Ɗaya Tana Isar Wa Rantsuwa Da Yawa?
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wabarakatuhu,
malam meye hukuncin wanda ya yi rantsuwa akan ba zai aikata wani abu ba sai
daga baya da aka ba shi hakuri sai ya aikata, kuma a baya ana bin shi azumin
kaffara, shin kowace rantsuwa zai yi mata azumin kaffara ko ya zai yi? Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ɗan uwa duk wanda ya yi
rantauwa da Allah a kan cewa ba zai aikata wani aiki ba sai daga baya ya
fahimci aikata hakan ne ya fi alheri kuma ya aikata, to hukuncinsa shi ne zai
ciyar da miskinai guda goma, ko ya ɗinka masu tufafi duka su goman, ko ya ƴantar
da wuya (wato bawa ko baiwa), wannan shi ne kaffarar rantsuwa, kamar yadda aya
ta 89 da ke suratul Má'ida
ta tabbayar:
لَا يُؤَاخِذُكُمُ اللَّهُ بِاللَّغْوِ فِي أَيْمَانِكُمْ وَلَٰكِنْ يُؤَاخِذُكُمْ بِمَا عَقَّدْتُمُ الْأَيْمَانَ ۖ فَكَفَّارَتُهُ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَاكِينَ مِنْ أَوْسَطِ مَا تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ رَقَبَةٍ ۖ فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ ۚ ذَٰلِكَ كَفَّارَةُ أَيْمَانِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ ۚ وَاحْفَظُوا أَيْمَانَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa a cikin
rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a
kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da
kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa ´yantãwar wuya. Sa'anan
wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. Wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan
kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana
muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa.
Idan mutum ya yi rantsuwa fiye da sau ɗaya a kan ba zai aikata wani aiki guda ɗaya ba, sai kuma ya aikata shi, to kaffara
ɗaya zai yi wa duka waɗannan rantsuwa, amma idan ya yi rantsuwa
fiye da ɗaya, a
kan mabambantan abubuwa, misali ya ce "wallahi ba zan ci tuwo ba",
"wallahi sai na yi karatu", "wallahi zan hau doki" sai kuma
ya ƙi
aikata su duka, to zai yi kaffara guda uku kenan, kowace rantsuwa tata kaffarar
daban.
Duba Majmu'u Fatáwá na Ibn Baz 23/145-146.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.✍🏻
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.