𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum warahmatullah Malam muna godiya
da fatawoyi, Allah yabiya da gida Aljannah, Ina tambayane akan "mace zata
iya hana mijinta kwanciya da ita idan baya bata ci da sha da kulawa?"
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuh.
Ciyar da mata akan mijinta wajibi ne matukar yana
da halin ciyarwa, wannan kuma dalili ne kai tsaye daga Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi kamar yadda Amru ɗan Ahwas Al'jushamy Allah ya kara masa
yarda ya ruwaito wanda hadisin Imamun Nawawy ya kawo shi acikin littafinsa
RIYADUS-SALAHIIN a babi na 34 babin wasiyya ga mata hadisi na 276 wanda Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace ku kyautata masu a ɓangaren zamantakewa da kuma ciyarwa.
Asali ma saboda haka ne ma Allah maɗaukaki ya fifita maza akan mata, saboda
namiji shi ne yake da karfin da zai fita ya nemo abinci saboda haka ne ma Allah
maɗaukaki Acikin Al'ƙur'ani yake cewa:
الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ وَبِمَا أَنفَقُوا مِنْ أَمْوَالِهِمْ ۚ فَالصَّالِحَاتُ قَانِتَاتٌ حَافِظَاتٌ لِّلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ اللَّهُ
MA'ANA "Maza masu tsayuwa ne akan mata,
saboda abinda Allah Ya fifita sãshensu da shi akan sãshe kuma saboda abinda
suka ciyar daga dũkiyõyin su, To, sãlihan mata mãsu biyayyah ne, masu tsarẽwa ga
gaibi saboda abinda Allah Ya tsare"
To amma a harkar zamantakewa na rayuwa akan samu
wani lokaci da Allah yakan jarabci bawansa ta hanyar toshewan hanyar samun
abincinsa har yakaiga ya rasa abinda zai ciyar da iyalinsa acikin gida, kuma
bashi da yadda zaiyi to anan ke a matsayin ki na matarsa sai kiyi hakuri har
Allah ya kubutar daku daga wannan kangin domin shi Allah idan yanason bawansa
sai ya jarrabeshi, don haka idan har haka ne ya faru to a dika yin hakuri da
abinda miji ya kawo har Allah ya bada mafita, muna addu'a Allah madaukaki ya
buda kofar samun halal.
Ana kuma iya samun miji wanda yana da wadata amma
kuma iyalinsa suna cikin ƙunci
wato yana barinsu da yunwa, To koda ace haka ne yake faruwa bai halatta ba a
gareki idan ya nemeki a matsayin ki na matarsa kiƙi amince masa ba, domin kuwa Annabi tsira
da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tsawatar akan haka a wajaje da dama,
kamar yadda shima akace masa ya ciyar dake kuma zalunci haramun ne, Allah
dakansa ya hana yin zalunci kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi ya tabbatar mana da cewa shi zalunci, wani baƙin duhu ne a ranar tashin Ƙiyamah, Allah ya tsare mu.
Zamu ambaci hadisai kaɗan akan haramcin rashin amsa kiran mai
gida a lokacin daya bukaci matarsa a kusa dashi, Hadisi ya inganta daga
Abu-Hurairah Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gareshi yace "Idan mutum ya kira matarsa zuwa ga shimfidarsa,
sai taƙi ta
amsa masa to zata kwana (wato zatayi barci) tana cikin fushin Allah kuma
Mala'iku zasuyi ta tsine mata har ta wayi gari" wannan hadisin Imamun Nawawy ya kawo shi
acikin littafin sa Riyadus-Salahiin a babi na 35 babin da yake magana akan
Hakkokin Miji akan matar sa hadisi na 281.
Kinga wannan hadisin yana nuna wajibi ne idan miji
ya kirayi matarsa ta amsa masa, kai kuma mijinta ga wani hadisi da zamu ambata
maka daga Annabi Sannan kuma Hadisi ya inganta daga Mu'awiya ɗan Haidata Allah ya kara masa yarda yace,
nace ya Manzon Allah menene hakkin matar ɗayanmu akansa? Sai Annabi tsira da amincin Allah
su tabbata a gareshi yace "Ku ciyar da ita Idan kukaci, kuma Ku tufatar da
ita Idan kuma kukayi tufafi Sannan kada Ku dika dukansu akan fuskokinsu Sannan
kada Ku dika roka masu fushin Allah Sannan kada Ku dika bujire masu (wato kuna
yin hijra) sai dai acikin gida (wato rashin kwanciyar aure da ita)" Abu Dawud,
Riyadus-Salahiin hadisi na 277 A wata Riyawa daga Abu-Hurairah Allah ya kara
masa yarda yace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace
"Yana daga cikin cikon kamala na mumini zaku sameshi mai kyakkyawan hali,
Sannan kuma mafi alkhairi daga cikin Ku shi ne wanda yake mai alkhairi ga
Iyalensa" shima duba Riyadus-Salahiin hadisi na 278.
Don haka dai ke 'Yar uwa kiyi hakuri idan mijin ki
bashi dashi, domin ni nasani da ace gashi yau mai gidan ki ya kawo maki haramun
kinci kinyi kiba ranar Ƙiyamah
kuma ace gashi zaku tafi wuta🔥, to yafi ace kinyi hakuri kin kwana da
yanwa anan duniya da ace gobe Ƙiyamah
kun tsinci kanki a wuta🔥, don haka kuyi hakuri har Allah ya hore
maku, amma idan mijin ki yana da wadata amma baya azurta ku da abinda zaku ci
to anan ma ba'ace idan ya nemeki kada ki amsa masa ba, a'a kiyi masa Nasiha
idan kuma haka bazai yiwu ba to ki kaishi kara wajen magabata in Allah ya yarda
zasuyi masa Nasiha, ko kuma ki hadashi da malaman unguwar ku suyi masa Nasiha
in Allah ya yarda komai zai dai dai ta, ba a iya rayuwa idan babu abinci idan
haka yaki ya gyaru sai ta kaishi kotu, Allah ya tsare mu, Allah yasa mudace.
Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.