Ticker

Shin Ya Hallata Nayi Istimnâ'i Don Gudun Aikata Zina?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam barka da war haka ya akaji da jama'a, to Allah ya saka da alkhairi... Don Allah malam inada tambaya kamar haka: mu fatake ne mukanje mu siyo wasu kaya a wasu kasashe to gaskiya bama tafiya da matan mu saboda yanayin tafiyar da wahalar ta da kuma dalilin yara agida shi yasa muke Barin su a gida. to gaskiya malam wani lokaci sha'awa tana damun mu sosai kuma wallahi irin garuruwan da muke zuwa basu ɗauki zina a bakin komai ba ko kana tafiya sai mace tazo ta sameka da niyyar aikata zinar... To yanzu malam idan mutum ya yi istimna'i a irin wannan yanayi don kar ya fada cikin aikata zina yana da laifi? Don Allah a ɓoye ID dina... nagode Allah yasaka da alkhairi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wabarakatuhu.

Lallai Malaman Musulunci sunyi saɓani dangane da ainahin hukuncin yin Istimna'i ga mutumin da yake cikin larura ko kuma yanayin da zai iya janyo masa yin zina.

Mafiya yawa daga cikin Mazhabobin Musulunci Kamar Maluman Mazhabin Malikiyyah da Shafi'iyyah sun ce HARAMUN NE yin istima'i akowanne halin da mutum yake cikinsa.

Maluman Mazhabar Hambaliyyah da Hanafiyyah sune suka ce idan Mutum ya kasance matafiyi, Ko kuma wanda aka kulleshi a kurkuku, ko kuma cikin wani yanayi wanda ba ya tare da Matarsa kuma yana tsoron afkuwar fitinar zina akansa, to suka ce ya halatta yayi.

Domin Imamu Ahmad yace an ruwaito cewa wasu daga cikin Sahabbai sunyi alokacin Yakokinsu da tafiye tafiyensu.

Kamar yadda Ibnul Ƙayyim ya hakaito daga Ibnu Aƙeelin acikin littafinsa mai suna BADA'I'UL FAWA'ID Juzu'i na 4 shafi na 129-130. yayi bayani dalla dalla akan mas'alar amma daga karshe Ibnul Ƙayyim ɗin ya kawo maganar Ibnu Aƙeelin inda yake cewa : "Abinda yafi inganci ni awajena shi ne rashin halaccin yin istima'in. domin kuwa Annabi ya shawarci wanda sha'awa take damunsa kuma bashi da halin yin aure, yace masa ya rika yin azumi. Da ace akwai wani halastaccen abu wanda zai yiwu, to da Annabi ya fadeshi anan".

Abinda yafi kyau gareku shi ne kuji tsoron Allah ku kawar da idanunku daga kallon haram ɗin, ko kuma ku rika daurewa kuna tafiya da matayenku, ko kuma ku rika aurar wasu matayen acan tunda garin ya riga ya zama wajen zuwanku yau da kullum.

Ka sani cewa Istimna'i Wasu Maluman suna cewa Halal ne, wasu sun ce Makruhi ne, amma mafiya yawan Maluma sun ce HARAMUN ne. Kuma Allah ya umurci Muminai su rintse idanuwansu kuma su kiyaye al'aurorinsu daga dukkan fasadi. Allah ya sawwake.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments