𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Ɗalibar makarantar koyon
aikin asibiti ce ta yi wa wata matar aure allura wadda daga baya ta gano yana
zubar da cikin da bai fi makonni uku ba, to shin wannan ɗalibar za ta yi kaffarar kisan kai kenan?
Sannan kuma ga shi tana fama da ciwon ‘ulcer’, ba za ta iya yin azumi ba? A
taimaka min da amsar wannan tambaya, menene mafita?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Wajibin da yake kan wannan ɗalibar da sauran ɗalibai irinta shi ne: Tun kafin ta yi wa
mara-lafiya allura ta san wace irin larura ce, adadi nawa ya dace ta yi, kuma
wace matsala ko ta’adi allurar ke haifarwa ga jiki? In da wannan ɗalibar ta ɗauki wannan matakin da farko to da wataƙila ba
ta shiga wata damuwa ba, kuma da ba ta buƙatu ga yin wannan tambayar ba, in Shã Allahu.
Sannan sahihiyar magana a wurin Malamai ita ce: Ba
a cewa mai zubar da ciki ta yi kisan-kai sai in ya kai lokacin da aka hura masa
rai, watau idan cikin ya kai watanni huɗu. Amma abin da bai fi makonni uku ba wannan ba za
a ce an yi kisan-kai ba, kodayake dai hakan ba abu ne da ya halatta ba a
shari’a, sai in akwai wata larura mai ƙarfi.
WALLAHU
A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.