Ticker

Takaitaccen Tarihin Alhaji Sani Dan’indo

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Sani Ɗan’indo

An haifi Alhaji Sani Ɗan Indo a shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da hamsin da biyar (1955) a garin Gusau, a wata unguwa da ake kira bakin kasuwa lungun malamai, sunan mahaifinsa Aliyu Ɗangiɗe, Sunan mahaifiyarsa Hafsatu, asalin mahaifinsa ɗan Sokoto ne, mahaifiyarsa kuma ‘yar Gusau ce. Sani Ɗan Indo ya yi makarantar primary a Model Primary da ke Kanwurin Gusau, kuma ya je makarantar gaba da primary wato Sambo Secondary School duk a cikin garin Gusau. Haka zalika ya yi makarantar Allo a makarantar Malan Isah da ke Lungun Malamai, duk a cikin garin Gusau. Tun yana ƙarami ya fara bin mawaƙa domin sha’awarsa ta waƙa, Alhaji Sani Ɗan’indo bai gadi kiɗa da waƙa ba ga tsohonsa domin malam Aliyu mahauci ne, kuma Ɗan’indo bai sami wata matsala gareshi ba a kan wannan hanya da ya zaɓar wa kansa ta waƙa a matsayin sana’arsa da yake neman abinci da ita.

Wanda ya fara bi a matsayin maigidansa shi ne Ali Gadanga. Ya fara waka (1976) daga baya har ya zama babban mawaƙi da duniya ta sani. Ya auri matarsa ta farko a garin Gurusu ta cikin (Bukkuyum) sanadiyar waƙar da ya yi ma mahaifinta ne sai mahaifinta ya ba shi ita, sunanta Suwaiba. Daga nan kuma ya tashi ya koma Tureta ta ƙasar Sakkwato duk dai a sanadiyar yawace-yawacen waƙar. Daga nan kuma ya koma Kano da zama duk dai a kan waƙar. Ya yi waƙoƙi masu yawa a lokacin rayuwarsa waƙarsa ta farko da ta fara shahara ita ce “Waƙar Macukule” domin ita ce ta ƙara fitar da shi aka ƙara sanin shi.

Ya auri mata uku ne a rayuwarsa waɗanda suka haɗa da, Suwaiba wadda ita ce wanda ya fara Aure, sai kuma Lami da Aisha da ya aura daga baya.

Yana da ɗiya guda shidda (6) maza biyu waɗanda su nem Zubairu da Hassan, su kuma matan su huɗu ne, da Zara’u da Aisha da Hussaina da kuma Hadiza,

Yana da yara da yawa da suke yawon waƙa da su, waɗansu kan bar ƙungiyar waƙar ko kuma su sake wata hidimar ko su rasu. Waɗanda aka fi sani daga cikinsu su ne Ɗan Ige, da Sa’adu, da Lauwali, da Ummaru, da Wababe, da kuma Garba Abu.

Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Sani Ɗan’indo

Shi Garba Abu shi ne ɗan ƙarami daga cikinsu, kuma shi ne ke da ƙaramar murya wanda yake yi wa Sani Ɗan Indo amshi a waƙoƙinsa. Kuma shi ɗan asalin garin Boɗinga ne ta jihar Sakkwato.  ya rasu yana da shekara 22-25 bai yi Aure ba.

Alhaji Sani Ɗan Indo ya yi waƙoƙi da yawa kamar irin su; Macukule, Ɗan Indo mutumin gaskiya, Waƙar Soja. Waɗannan waƙoƙin su ne suka fi shahara daga cikin waƙoƙinsa, duk da cewa ya yi waƙoƙi da dama ta ɓangaren noma da sauransu.

Wani abu da ya bambanta Alhaji Sani Ɗan’indo da sauran mawaƙa shi ne kayan kiɗansa. Bayan kalangunansa da kuntuku har da kwalba yake haɗawa ana kaɗawa ana ƙara wa waƙar armashi.

Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Sani Ɗan’indo

Mawaƙin Alhaji Sani Ɗan Indo ya rasu a ranar 8 Febrainu 2016 ya rasu a cikin Birnin Kano bayan ya dawo daga wani biki da aka gayyace shi a garin Jigawa. Waƙarsa ta ƙarshe ita ce waƙar da ya yi ma Sarkin Haɗeja.

Ya rasu yana da shekara sittin da ɗaya (61), bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Post a Comment

0 Comments