Published in KADAURA, Journal of Hausa Multidisciplinary Studies, Vol. 1. No. 4, January, 2018, page 02 – 17. Special Edition, ISSN: 2536-7609, Kaduna State University.
Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa a Jami’o’in Arewacin Nijeriya: Ƙalubale ga Tsarin Koyo da Koyarwa a Ƙarni na 21
English Rendition as, Deterioration of Hausa Culture in Northern Nigerian Uniɓersities: A Challenge Facing Teacher – Education in the 21st Century
Dr. Bashir Aliyu Sallau
Department of Nigerian Languages
Umaru Musa Yar’adua University
Katsina – Nigeria
Tsakure
Cigaban kowace al’umma yana da matuƙar alaƙa da irin yadda wannan al’umma ta yi riƙo ga kyawawan al’adunta. Haka kuma, biyayya ga kyawawan al’adu na taimaka wa al’umma ta zauna lafiya da samun bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa. Al’ummomi daban-daban a wannan duniya ta yau waɗanda suka riƙe kyawawan al’adunsu na daga cikin waɗanda suke zaune lafiya da bunƙasar tattalin arziki. A ɗaya ɓangaren kuwa, watau al’ummomin da suka yi watsi da kyawawan al’adunsu suka ɗauki marasa kyau na daga cikin al’ummomin da suke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi a yau.
Gabatarwa
A al’adance iyaye ne suke fara koya wa ‘ya’yansu tarbiyya mai kyau, daga baya kuma sai malaman makaranta ta Islamiyya ko ta zamani su ɗora a kan ta farko yadda yaro zai koyi halaye ingantattu, masu kyau yadda zuri’arsa da al’ummarsa za su yi alfahari da shi. Sannu a hankali sakamakon shigowar baƙi da ire-iren al’adunsu, musamman Turawa da suka kawo ilimin boko da kuma kafa Jami’o’i a sassa daban-daban na Tarayyar Nijeriya, sai matasa suka fara kwaikwayon wasu munanan al’adu suka watsar da kyawawan al’adu waɗanda suka gada iyaye da kakanni. Sakamakon watsar da kyawawan al’adunmu da matasa suka yi an sami babbar ɓarna wadda ta haifar da taɓarɓarewar al’adu da rashin bin doka da rashin biyayya ga manya da sauransu, musamman a Jami’o’i. Dangane da haka, burin wannan takarda shi ne ta yi nazari don fito da yadda al’adun Hausawa suka taɓarɓare a Jami’o’in Arewacin Nijeriya da kuma ire-iren ƙalubalen da wannan al’amari ya haifar wa harkar koyo da koyarwa a wannan Ƙarni na 21.
1.0 Waiwaye a kan Al’adun Hausawa
Masana irin su Ibrahim, 1982 da Bunza, 2006: ɗɗɓ, ɗɗɗii, sun gabatar da bayanai dangane da asali da ma’anar kalmar al’ada. A dunƙule kalmar al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. Ta la’akari da haka, a iya cewa dukkan al’ummomin da suke zaune a Tarayyar Nijeriya kafin shigowar Turawan Mulkin Mallaka suna da ire-iren al’adunsu mabambanta. Ire-iren waɗannan al’adu ne suke zama jagora ga kowace al’umma dangane da abubuwan da suka dace a yi da kuma waɗanda ba su dace a yi ba. A wasu fannoni ana samun wasu wuraren da al’ummomi suke yin haɗaka a kan wasu al’amura waɗanda suka shafi yadda suke gudanar da harkokin al’adunsu, musamman ta fuskar tarbiyya da aure da haihuwa da mutuwa da zamantakewa da sauransu. Daga cikin waɗannan fannoni na al’ada za a tarar mafi yawanci al’ummomi suna koya wa ‘ya’yansu yin cikakkiyar biyayya ga abin da suke bautawa da koya musu sana’o’insu na gargajiya da ƙulla danƙon zumunci da gaskiya da riƙon amana da biyayya ga shugabanci da taimakon juna da kara da nuna alkunya da sauransu.
2.0 Tarbiyya a Wajen Hausawa
Tun lokaci mai tsawo da ya gabata kafin shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa al’ummar Hausawa suke gudanar rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya. Wannan kuwa ya faru ne saboda suna da kyakkyawan tsarin tarbiyya wanda ya ba kowa damarsa yadda wani ba ya shiga cikin harkar da ba ta shi ba. Wannan dalili ne ya sa ko da addinin Musulunci ya shigo ba a fuskanci wasu manyan matsaloli ba dangane da halin zamantakewar wannan al’umma. Matuƙar ana son kwalliya ta biya kuɗin sabulu a tsarin koyo da koyarwa, to ya dace a koma wa tsarin tarbiyya Hausawa ta gargajiya da ta addinin Musulunci.
2. 1 Matsayin Tarbiyya Wajen Gina Ingantacciyar Al’umma
Dukkan al’ummar da take son ta zauna lafiya, kuma ‘ya’yanta su sami ci gaba mai ɗorewa, dole ne ya zama tana da wasu ingantattun matakai na tarbiyya waɗanda za su taimaka wa wannan al’umma ta zama ta gari. Tun kafin zuwan wannan zamani al’ummar Hausawa suna da ire-iren waɗannan matakan tarbiyya waɗanda suka taimaka wa wannan al’umma ta zama ta gari abin koyi ga maƙwabta na kusa da ma na nesa. Waɗannan matakan tarbiyya sun haɗa da kiyaye dokokin addini, da biyayya ga shugabanci, da gaskiya da riƙon amana, da sadar da zumunci da taimakon juna da aiki tuƙuru.
2.1.1 Kiyaye Dokokin Addini
Hanyar bauta wa wani abu wanda mutum yake tsammanin shi zai biya masa buƙatun rayuwa na yau da kullum shi ne addini. Addinin farko na mutanen ƙasar Hausa shi ne addinin gargajiya watau bautar iskoki ko mutanen ɓoye. Addinin gargajiya ya faru ne ta bin wasu hanyoyi da mutane suka ƙirƙiro wa kansu ta bautar waɗansu abubuwa don cim ma biyan buƙatunsu. Kafin Hausawa su karɓi addinin Musulunci suna matuƙar kiyaye dokokin addinin gargajiya. Wannan dalili ne ya sa a wancan lokaci da ya gabata da wuya ka sami Bahaushe yana yin ɗaya daga cikin waɗannan:
Ƙarya, idan Bahaushe ya yi ƙarya abin da yake bauta wa zai yi masa hukunci mai tsanani.
Sata, idan Bahaushe ya yi sata Uwar Gona za ta kashe shi.
Budurwa ba ta yin lalata (Zina). Idan budurwa ta yi lalata a ranar bikin ta abin da ake bauta gidansu zai yi mata hukunci mai tsanani. Misali, duk da kasancewar a al’adar Hausawa ba a yi wa budurwa aure sai ta kai shekara goma sha takwas ko fiye da haka, watau an tabbatar da ta balaga, an yarda idan saurayi yana neman auren budurwa ya je tsarince wurinta, watau ya kwana gidansu a ɗaki ɗaya da ita bisa shimfiɗa ɗaya, ko ita ta je gidan saurayin nata su kwana tare, amma duk da haka al’ada ba ta yarda ya ko taɓa jikinta ba, balle ma har ya aikata wani abu da ita ba, watau ya yi lalata (zina) da ita ba. Idan ya kuskura ya taɓa ta ko ya yi ƙoƙarin yin lalata da ita, to ya shiga uku ya lalace, don kuwa duk wannan yanki nasu ba zai ƙara samun budurwar da za ta yarda da shi ba. Wannan dalili ne zai kai shi ga rasa matar da zai aura, daga ƙarshe dole ya gudu ya bar ƙasar baki ɗayanta yadda ba a za a sake jin labarinsa ba. Ire-iren waɗannan mutane ne za a tarar sun je wasu garuruwa inda ba wanda ya san su a garin. A wasu lokuta har su mutu ba a sanin daga inda suka zo wannan ƙasa. Wannan hukunci ga namiji ke nan.
Ita budurwa kuwa idan ta kuskura ta yi lalata (zina) tana fuskantar hukunci mai tsananin wanda a wani lokaci yana iya zama dalilin mutuwar ta. Wannan hukunci ya danganta da abin bautar gidansu. Da farko abin da ake fara yi shi ne, za a kira ta a tambaye ta, ko ta san ɗa namiji? Idan ta amsa da cewa ta san ɗa namiji, shi ke nan ta jawo wa kanta da dukkan zuri’arta abin kunya, sai kuma a rage yawan dukiyar aurenta. Idan kuwa ta amsa da cewa ba ta san ɗa namiji ba, daga nan sai iyayenta su bi hanyar da suka gada ta tsafi don gane gaskiyar abin da ta faɗa. Idan aka gane ƙarya take yi tsafin gidansu zai yanke mata hukunci mai tsanani musamman ya kashe ta. Ga misalin ire-iren yadda ake gane budurwa ta san ɗa namiji ko ba ta san shi ba kafin a yi mata aure a al’adar Maguzawa da kuma irin hukunci da suke yanke wa ‘ya’yansu mata waɗanda ba su kai budurcinsu ba dangane da abubuwan da suke bauta wa na gargajiya.
(i) Masu Bautar Aljanin Magiro
Maguzawan da suke bautar wannan tsafi sun ɗauka aljanin yana zaune a dutsin Kwatarkwashi. A Kwatarkwashi arnan Suna ne suke bautar wannan gunki, haka kuma akwai wasu arnan a wasu sassan ƙasar Katsina da suke bautar wannan tsafi. A ƙasar Katsina a ƙauyen Kunkunna da Makanwaci da Tamna da Maikada da Daulai cikin ƙaramar Hukumar Safana. Haka kuma a ƙauyukan Barza da Gerecen-Arna da Aidun Gadaje cikin ƙaramar Hukumar Ɗanmusa akwai arnan da suke yin irin wannan bauta ta tsafin Magiro. Domin yin wannan bauta, suna samun bishiyar tsamiya ko marken da yake da duhuwa da sarƙaƙƙiya. Waɗannan arna na samun yashi mai laushi da kyawo su zuba a gindin wannan tsamiya ko marke, sai kuma su kawo baƙin zane da baƙin rawani da baƙar hula da baƙar riga da baƙin wando dukkansu na saƙi sai a ɗaɗɗaura su wurin wannan tsamiya. Daga nan, sai a sami tulunan giya biyu a ajiye gindin wannan tsamiya ko marke, sai kuma a yanka baƙin bunsuru a gindin tsamiyar. Dukkan wanda ya ga waɗannan alamomi zai fahimci akwai wani abu da ke faruwa a wurin, kuma ana gargaɗin mutane da su yi nesa da wurin don ba mai zuwa wurin sai wanda yake kula da tsafin ko wani daga cikin zuri’arsa. Ana tsorata mutane da cewar, dukkan wanda ya je wurin, idan ba waɗannan mutane ba, dukkan abin da ya same shi ya kuka da kansa.
Mabiya tsafin Magiro sun ɗauka wannan aljani na kare su daga dukkan bala’o’i, kuma yana biya masu dukkan buƙatun da suka nema daga gare shi. Haka kuma, suna ikirarin cewa, dukkan wanda yake da shakka kan gaskiyar tsafinsu suna iya nuna masa ta hanyar kiran aljanin. Akwai dalilan da kan sa a kira aljanin Magiro waɗanda suka haɗa da idan ana biki gidan mabiyansa, yana zuwa don ya bayyana wa jama’a da mahaifan wannan yarinya da za a yi wa aure ba ta yi lalata (zina) ba a lokacin da take budurwa. Hanyar da ake gane haka shi ne, a ranar da za a ɗaura wa yarinyar aure, tun da asuba sai mahaifanta su kira ta, sai a ajiye turmin daka a tsakiyar gidansu ta hau kansa ta zauna. A wannan lokaci ne za a kira wannan aljani na Magiro. Da ya iso gidan, sai ya yi ta zagaya gidan kamar iskar guguwa, ya kuma yi ta yin ruri kamar bajimin sa. Idan wannan yarinya ta taɓa yin lalata, sai ya kashe ta. Idan kuwa ba ta taɓa yi ba, sai ya yi ta zagaye-zagayensa har ya gama ba abin da zai sami wannan yarinya. Ko kuma, idan ya rage saura kwana ɗaya a yi bikin, sai a sami baƙin ɗan’akuya da jan zakara da goran giya a kai su wurin da ake yin tsafin Magiro. Idan gari ya waye, sai a je wurin a duba. Idan an tarar ɗan’akuyan da zakaran sun mutu, kuma goran giya babu kome cikinsa, alama ce wadda take bayyana cewa wannan yarinya ba ta yi lalata ba, Magiro ya yi maraba da ita ke nan. Idan kuwa aka tarar ɗan’akuyan da zakaran, kuma ba a taɓa goran giya ba, alama ce wadda take bayyana wannan yarinya ba ta kai budurcinta ba, Magiro bai yi maraba da ita ba ke nan, sai ya kashe ta. Daga nan, sai iyayenta su yi ta murna saboda ɗiyarsu ta kai budurcinta. Daga nan, sai a ɗauki wannan yarinya a kai ta ɗakin mahaifiyarta inda za a yi sauran al’adun da suka dace a yi mata don kai ta gidan miji (Ibrahim, 1982: 172).
(ii) Masu Bautar Uwar Gona
Su kuma Maguzuwa masu bautar tsafin Uwar-Gona a lokacin da ‘yarsu budurwa za ta yi aure, hanyar da suke bi don su gane cewa wannan yarinya wadda za a yi wa aure ta yi lalata ko ba ta yi lalata ba ita ce, sai a sa waɗanda za su auri wannan yarinya su kawo ɗan’akuya. Daga nan sai a samo turamen daka uku, a kuma samo mutane uku, sai a jera turame biyu kusa da kusa, sai a sanya turmi na cikon ukun a gefen waɗannan turame biyu. Daga nan, sai mutane biyu daga cikin mutanen nan uku su hau kan turmi ɗaya - ɗaya, shi kuma na cikon uku sai ya hau kan ɗaya turmin. Sai a kawo wannan ɗan’akuya a ba waɗannan mutane biyu waɗanda suke kan turame biyu da suke kusa – kusa. Ɗaya ya riƙe ƙafafun gaba, shi kuma ɗayan ya riƙe ƙafafun, shi kuma wanda yake kan ɗayan turmi na cikon uku, sai a kawo masa wani takobi na tsafi wanda aka ajiye ba a amfani da shi sai irin wannan rana. Lokaci da ya amshi wannan takobi, sai ya sari wannan ɗan’akuya da shi. Idan wannan yarinya ba ta san ɗa namiji ba, sari ɗaya zai yi wa wannan ɗan’akuya ya raba shu biyu, shi ke nan sai iyaye da abokan arziki su yi ta murna, ‘yarsu ta kai budurcinta. Idan kuwa wannan yarinya ta san ɗa namiji ko sara nawa ya yi wa wannan ɗan’akuya ba zai yi masa ko ƙwarzane ba balle ya raba shi biyu. Daga nan, nan take wannan yarinya za ta faɗi ta mutu.
(iii) Masu Bautar Tsafin Kurmawa
Maguzawan da suke bautar tsafin Kurmawa waɗanda ake samu a ƙasar Katsina da Kano da Zamfara, a lokacin da za su yi wa ɗiyarsu budurwa aure, idan an tambaye ta ce ba ta san ɗa namiji ba, sai a samo ɗan kwikwiyo da rago a yanka su, a feɗe naman a kuma yayyanka su a haɗe su wuri ɗaya a soya. Bayan ya naman ya soya, sai a kira wannan yarinya a ba ta naman ta ci. Idan ba ta san ɗa namiji ba, duk lokacin da za ta ɗauko tsokar naman ta ci, sai ta ɗauko ta ragon, za ta ci har ta ƙoshi ba abin da zai same ta. Idan kuwa ta san ɗa namiji ba za ta bambance naman kare da na ragon ba, sai ta haɗa su ta yi ta ci har sai ta ƙoshi. Daga nan sai ta faɗi ta mutu nan take. Idan kuwa a lokacin da aka tambaye ta, ko ta san ɗa namiji? Ta amsa da cewa ta sani, sai a ba ta wannan kwikwiyo ta riƙa yawo da shi, don bayyana wa jama’a ba ta kai buturcinta ba, sannan kuma a rage yawan dukiyar aurenta. Wannan dalili ne, ya sa Hausawa yin karin maganar da ke cewa, ‘sharri kwikwiyo ne mai shi yake bi’.
(iv) Masu Bautar Tsafin Maƙera
Su kuwa Maguzawan da suke bautar tsafin Maƙera waɗanda su ma ana samun a ƙasar Katsina da Kano da Zamfara, a lokacin da za su yi wa ‘yarsu budurwa aure, idan ya rage saura kwana ɗaya a ɗaura mata aure, sai a kira ta a tambaye ta ko ta san ɗa namiji? Idan ta amsa da cewa ba ta san ɗa namiji ba, sai a samo jan zakara. Daga nan, sai a ɗebo jar dawa a sami mata uku ko huɗu, sai a kamo wannan zakara a sanya shi ƙarƙashin turmin da ake daka, a zuba wannan jar dawa cikin wannan turmi, sai waɗannan mata su yi ta dakan wannan dawa har sai sun mayar da ita gari. Lokacin da suke dakan wannan dawa wannan zakara na ƙarƙashin turmin da suke dakan. Idan wannan yarinya ba ta san ɗa namiji ba, duk tsawon lokacin da aka ɗauka ana dakan wannan dawa ba abin da zai sami zakaran, hasali ma, washegari ranar da za a ɗaura auren wannan yarinya, zakaran ne zai fara cara da asuba don tayar da mutanen wannan gida daga barci. Idan kuwa wannan yarinya ta san ɗa namiji, da safe idan aka ɗaga turmin da aka sanya zakaran za a tarar ya rududduge ya saje da ƙasa, ana ganin haka, ita kuma wannan yarinya tana faɗuwa nan take ta mutu (Ibrahim, 1982: 173 - 175).
Kamar yadda aka yi bayani a sama, waɗannan hanyoyi ne al’ummar Hausawa kafin su karɓi addinin Musulunci suke hukunta waɗanda suke aikata lalata (zina), wannan ne ya sa a wancan zamani suka zauna lafiya ba yawan zinace-zanace aka kuma sami sauƙin tafiyar da shugabancin al’umma ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba. Yanzu kuma, za mu duba irin hukuncin da addinin Musulunci ya yi umurnin a yanke wa waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki. Da farko za mu duba cikin Alƙur’ani Maigirma, cikin sura ta 17 Aya ta 32, inda Allah, Maigirma da ɗaukaka Yake cewa:
Yanzu kuma, za mu duba irin hukuncin da addinin Musulunci ya yi umurnin a yanke wa waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki. Da farko za mu duba cikin Alƙur’ani Maigirma, cikin sura ta 17 Aya ta 32, inda Allah, Maigirma da ɗaukaka Yake cewa:
“Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya” (Gumi, 1979: 419).
Karɓar addinin Musulunci da Hausawa suka yi ya ƙara jaddada waɗannan dokoki.
2. 1. 2 Biyayya ga Shugabanci
Shugabanci yana nufin yi wa al’umma jagora a halin zamantakewarsu na yau da kullum. A nan duk wanda aka ba ragamar tafiyar da mulkin al’umma, nauyi ya hau kansa na tsare lafiyarsu da dukiyarsu da mutuncinsu. Su kuma waɗanda ake shugabanta haƙƙinsu ne su ba wanda yake shugabancinsu haɗin kai, da bin umurnin sa ta hanyar bin doka da oda, da yi masa biyayya don ya sami sauƙin tafiyar da mulkinsu cikin kwanciyar hankali. A ƙasar Hausa shugabanci yana tafiya kamar haka:
Ø Gidan Gandu
Ø Unguwa
Ø Ƙasar Dagaci
Ø Ƙasar Hakimi
Ø Ƙasar Sarki (Usman, 1972:176)
A kowace masarauta akwai ‘yan majalisar wannan sarki, su ne suke taimaka wa wannan sarki da shawarwarin aiwatar da mulkin wannan ƙasa cikin nasara da adalci. Waɗannan ‘yan majalisa sun haɗa da waziri da alƙali da magatakarda da ma’aji ko ajiya da sarkin fada da shamaki da shantali da galadima da Sarkin gida da sauransu. Karɓar addinin Musulunci da Hausawa suka yi, ya ƙara jaddada yin biyayya ga shugabanci. Wannan dalilin ne ya sa addinin Musulunci ya shimfiɗa yadda za a gudanar da mulkin adalci ga kowace al’umma yadda za a zauna lafiya, kuma wannan al’umma ta sami dauwammen ci gaba da zama lafiya.
2.1.3 Gaskiya da Riƙon Amana
Gaskiya na nufin yin dukkan wani abu wanda zai bayyana zahirin yadda wannan abu yake, watau ba ragi ba ƙari. Riƙon amana kuma na nufin adana wani abu na dukiya ko sirri wanda a lokacin da bukatar shi ta taso a bayar da shi kamar yadda aka bayar. Idan kuma wani sirri ne ba za a sanar da kowa ba, daga kai sai wanda ya sanar da kai. Kafin zuwan wannan zamani an san Hausawa da bin gaskiya da riƙon amana ga dukkan al’amuransu na rayuwa. Karɓar addinin Musulunci da Hausawa suka yi ya ƙara jaddada bin gaskiya da riƙon amana.
2. 1. 4 Sadar da Zumunci da Kara da Alkunya
Sadar da zumunci da kara da alkunya al’amura ne waɗanda al’ummar Hausawa suke ba matuƙar muhimmanci, don kuwa lokaci bayan lokaci ‘yan’uwa da abokan arziki kan riƙa ziyartar juna don gaisawa da ganin halin da suke ciki. Kafin su tafi ziyartar ‘yan’uwa da abokan arziki sukan riƙa wani abu su kai masu, ana yin haka gwargwadon ƙarfin arzikin mutum. Wasu kuma, saboda rashin abin da za su kai ba za ya hana su yin zumuncin ba, suna zuwa wurin ‘yan’uwansu domin su ga halin da suke ciki ba dole sai sun kai musu wani abu ba. Shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa ya ƙara jaddada waɗannan ayyuka na alheri, watau sadar da zumunci.
2.1.5 Taimakon Juna da Aiki Tuƙuru
Domin tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum cikin sauƙi, al’ummar Hausawa suna bin tafarkin rayuwa irin ta cuɗan-in-cuɗe-ka, watau taimakon-kai-da-kai. Ta wannan fuska, idan abin arziki ya sami ɗan’uwa, ko abokin arziki, ko wanda ake zaune tare da shi a wannan ƙauye ko unguwa ko gari, misali aure ko haihuwa, sai duk a taru don taya shi murna. A lokacin bikin, za a yi ta kawo masa gudummuwa wadda wasu kan kawo hatsi ko abinci ko kuɗi ko sutura da sauransu don dai a taimaka wa wannan ɗan’uwa, ko abokin arziki gudanar da wannan hidima ba tare da ya wahala ba. Haka kuma, suna aiki tuƙuru don neman na kai.
3.0 Muhimmancin Ilimi ga Al’umma
Cigaban kowace al’umma a wannan zamani ya ta’allaƙa da irin tsarin ilimin da ake amfani da shi wajen koyo da koyarwa. Wannan dalili ne ya sa ake tsara muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen koyo da koyarwa. Misali, a Tarayyar Nijeriya, masana da manazarta ta fuskar koyo da koyarwa a lokuta daban-daban sun fitar da tsare-tsaren ilimi na fannoni da matakai daban-daban. Maƙasudin yin haka shi ne, a samar wa al’umma da ingantaccen ilimi wanda zai kawo zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.
Bugu da ƙari, Tarayyar Nijeriya tana cike da al’ummomi waɗanda suke da harsuna da al’adu da addinai mabambanta. Wannan dalili ne ya sa masana da suke tsara ilimi na wannan ƙasa suke la’akari da waɗannan bambance-bambance yadda ba wanda zai yi ƙorafin an taushe masa hakkinsa. Dalilin haka ne, a wajen tsara ilimi, masana da al’ummomin da za a kafa makarantu a wajensu suke haɗa kai, su tsara ilimin yadda zai tafi daidai burinsu.
3. 1 Burin Jami’o’in Arewacin Njeriya
Domin neman amincewar waɗanda suke son samun gurbin karatu a manyan makarantu da Jami’o’in da suke a Arewacin Nijeriya, ana bayyana burin da ake son a cimma. Misali, babban burin da Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta Katsina ta sa a gaba shi ne: “Ta zama ɗaya daga cikin mashahuran Jami’o’in Tarayyar Nijeriya, wadda take da ingantaccen tsarin koyo da koyarwa yadda za a iya ƙirƙirar abin da zai kawo wa al’umma cigaba. Ta zauna lafiya da al’ummomin da aka kafa Jami’ar a yankinsu kasancewarsu waɗanda za su taimaka musu wajen gina ingantacciyar tarbiyya. Burin wannan Jami’a ne ta yaye ingantattun ɗalibai, masu ɗinbin ilimi da tsoron Allah da aiki tuƙuru da ƙwazo, waɗanda za su iya warware wa kansu dukkan matsalolin rayuwa na Ƙarni na 21, su kuma dogaro da kansu ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙiren da za su taimaka a bunƙasa ƙasa ta hanyar amfani da ilimin kimiyyar sadarwa, sannan kuma su sami damar ƙara faɗaɗa iliminsu”.
Bisa la’akari da wannan buri ne, a lokacin da ɗalibi ya kammala Jami’a, Majalisar Dattawa ta Jami’ar take ba ɗalibin takardar sheda wadda take bayyana cewa: Bisa la’akari da cika Ƙa’idojin Ilimi da Tarbiyya na wannan Jami’a, Majalisar Dattawa ta Amince a ba ɗalibin Digiri a Fannin da ya yi karatu da kuma darajar digirin.
Idan muka nazarci wannan buri za mu ga bai yi saɓani da tsarin tarbiyyar Hausawa ba kamar yadda aka bayyana su a bayanan da suka gabata.
3. 2 Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa a Jami’o’in Arewacin Nijeriya
Taɓarɓarewar al’adun Hausawa na nufin watsi da nuna halin ko-in-kula ire-iren waɗanda malamai da ɗalibansu suke yi wa kyawawan aƙidu da muradu da tarbiyyar Hausawa a Jami’o’in Arewacin Nijeriya. Kamar yadda bayanai suka gabata, al’ummar Hausawa suna alfahari da kyawawan al’adunsu waɗanda suka taimaka musu samun cigaba kafin wannan zamani. Shigowar Turawa ƙasar Hausa da kawo ilimin zamani ya taimaka wajen taɓarɓarewar al’adun Hausawa a wannan zamani.
Kiyaye dokokin addini shi ne babban ginshiƙin tarbiyyar Hausawa, amma sakamakon shigo da wata sabuwar rayuwa wadda ta bayyana dukkan wanda ya shiga Jami’a yana da ‘yancin cin gashin kansa, saɓanin koyarwar al’adar Hausawa da ta addinin Musulunci. Irin wannan ‘yanci ya taimaka matuƙa wajen sauya tunanin wasu matasa na yin abin da suka ga dama ba tare da la’akari da irin tarbiyyar da aka ba su a gidajensu ba. Wannan babban ƙalubale ne ga tsarin koyo da koyarwa a Ƙarni na 21.
- Biyayya ga shugabanci ya yi rauni sosai a Jami’o’i don kuwa wasu ɗalibai ba ruwansu da dukkan malamin da ba ya ɗaukar su darasi.
- Wasu ɗaliban ba su da gaskiya don kuwa a ko wane lokaci dama suke nema wadda za ta biya musu bukatunsu.
- Akwai ɗaliban da ba su da zumunci. Da zarar sun kammala karatu shi ke nan labari ya ƙare.
- Mafi yawancin ɗalibai ba su da ƙoƙarin yin aiki tuƙuru da zai kai su ga samun sakamako mai kyau.
3. 3 Ƙalubalen da ke Fuskantar Koyo da Koyarwa a Jami’oin Arewacin Nijeriya a Ƙarni na 21
Sakamakon taɓarɓarewar al’adun Hausawa a Jami’o’in Arewacin Nigeria tsarin koyo da koyarwa na fuskantar babban ƙalubale waɗanda suka haɗa da:
ü Mafi yawancin ɗalibai ba sa dagewa su yi aiki tuƙuru domin samun ilimin da ya kawo su. Wannan matsala ta haifar da bayar da na goro ga wasu riɓaɓɓun malamai don a ba ɗaliban sakamakon da ba su cancanta ba a lokacin jarrabawa ko aikin gida ko ƙaramar jarrabawa ta gwaji. Wasu kuma na amfani da dabaru iri-iri don satar jarrabawa.
ü Haka kuma wasu ɗalibai musamman mata suna zubar da mutuncinsu ga wasu malamai don a ba su sakamakon da ba su cancanta ba.
ü Wasu malaman kuma na amfani da damar da suka samu ta zama malamai a jami’a su riƙa cin zarafin ɗalibai mata ta hanyar tilasta musu biya musu buƙatunsu don su ba su sakamakon da ba su cancanta ba. Su kan kuma tilasta wa ɗalban maza da wasu matan kawo musu na goro, watau abubuwan da suka shafi kuɗi da sauran abubuwan more rayuwa don su ba su sakamakon da ba su cancanta ba.
ü Wasu ɗalibai da malamai na shiga ƙungiyoyin asiri kamar na tsafe-tsafe da sauransu don samun biyan bukatunsu na rayuwar duniya. A ire-iren waɗannan ƙungiya wasu ɗalibai na shigar su don samun yadda za su yi amfani da tsafi su ci jarrabawa ko su sami kuɗi ko mallakar wata mace wadda ba tasu ba. Haka kuma, wasu malamai na shiga ire-iren waɗannan ƙungiyoyi don su sami ɗaukaka da abin duniya ko mallakar wata mace wadda ba tasu ba.
ü Ƙarya na daga cikin ƙalubalen da tsarin koyo da koyarwa ke fuskanta a Ƙarni na 21. Wannan kuwa ya faru ne saboda mafi yawancin ɗalibai maƙaryata ne.
ü Saboda waɗannan matsaloli da aka lissafa a bayanan da suka gabata, an fahimci cewa, mafi yawancin Jami’o’in da suke a Arewacin Nijeriya suna ba ɗalibai shedar kammala karatu wadda ba su cancanta ba a Ƙarni na 21. Wannan ya bayyana a zahiri tsarin koyo da koyarwa a Jami’o’in Arewacin Nijeriya na fuskantar babban ƙalubale wanda ya zama tilas a nemo hanyar da za a bi don fitar da jakai cikin duma.
4. 0 Shawarwari
Bisa la’akari da yadda wannan al’amari ya yi ƙamari, ya zama dole a ba da shawarwari waɗanda za su taimaka a daidaita al’amarin.
v Ya zama dole masu tsari ilimi su riƙa la’akari da kyawawan al’adun al’ummar da za a kafa makaranta ko jami’a a yankinsu. Sannan kuma a tilastawa malamai da ɗalibai koyi da waɗannan al’adu.
v A ƙara tilasta wa malamai da ɗalibai bin dokokin ƙasa da na jami’a yadda za a sami cikakken zama lafiya. Ya zama dole a riƙa ba ɗalibai cikakkken horo da wayar musu da kai a kan kyawawan al’adun al’ummomi daban-daban.
v A ƙara wa ɗalibai ƙarfin guiwar dagewa su yi aiki tuƙuru don cimma burin da ya kawo ɗalibin wannan Jami’a.
v A ƙara faɗakar da ɗalibai mata muhimmanci kara da alkunya da tsare mutunci yadda za su cimma burin da ya kawo su Jami’a ba tare da wani ya ci zarafinsu ba.
v A ƙara jawo hankalin ɗalibai su tsare gaskiya su kauce wa ƙarya.
v Sharuɗɗa biyu suke ba da damar ba ɗalibi sakamakon kammala jami’a: Samun horo wanda ya kai shi ga cin jarrabawa, da kuma samun sa mai ladabi da biyayya da ɗa’a. A Ƙarni na 21 an fi mayar da hankali a kan na farkon. Ya zama dole a kula da na biyun. Dukkan ɗalibin da ba shi da ɗa’a bai cancanci a ba shi sakamakon kammala jami’a ba.
v Malamai su sani ɗalibai amana ce aka ba su, ya zama dole su kula da su kamar yadda suke kula da ‘ya’yansu. Dangane da haka, ya zama dole su zama masu gaskiya da riƙon amana, su kauce wa dukkan abin da zai zubar musu da mutuncinsu a kan idanun ɗalibansu.
5. 0 Kammalawa
Dukkan al’amari na duniya wanda yake fuskantar matsaloli, yana da matuƙar muhimmanci a duba shi da idon basira yadda za a kawo gyaran da zai taimaka wa al’umma ta sami zaman lafiya da dauwamammen cigaba. Ilimi na daga cikin abubuwan da suke taimaka wa al’umma ta sami cigaba, matuƙar yana fuskantar ƙalubale ya zama dole a duba. Sakamakon taɓarɓarewar al’adun Hausawa a Jami’o’in Arewacin Nijeriya, tsarin koyo da koyarwa na wannan yanki na fuskantar ƙalubalen da ake yaye ɗaliban da ba su cancanci a ba su shedar kammala karatun da ake ba su ba.
Manazarta
Bargery, G. P. (1993) A Hausa – English Dictionary and English – Hausa Vocabulary, Zaria, ABU Press.
Bunza, A. M. (2008) “Religion and the Emergence of Hausa Identity: (An Inƙuiry into the Early Traditional Religion in Hausa land)”, being a paper presented at an International Conference titled: “Hausa Identity: Religion and History”, organised by AHRC and ESRC held at University of East Anglia Norwich.
Dobie, A. B. (2009) Theory into Practice: An Introduction to Literary Criticism, Second Edition, USA, Wadsworth, Cengage Learning, Michael Rosenberg Publishers.
Ibrahim, M. S. (1982) ”Dangantakar Al’ada da Addini:Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Mahadi, A. (1996/1997) “Colonial/Neo-Colonial Education and the Underdeɓelopment in Nigeria. Zaria: Ahmadu Bello University Inaugural Lecture Series.
Radcliffe-Brown, A. R. (1971) Structure and Function in Primitiɓe Society. London: Cohen & West Ltd, Broadway House, Carter Lane.
Sallau, B. A. , “Tarbiyyar Hausawa a Matsayin Ginshiƙi na Samar da Ingantacciyar Al’umma”, (2013) with English rendition as “Hausa Moral Behaɓiour as a Pillar of Building a Better Society”, being a paper published from proceedings of a Three Day 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organised by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano, from 14th – 16th January, 2013, Page 708 – 727.
Sallau, B. A. , “Negligence of Traditional Occupations as Contributory Factor in Youth Unemployment in Northern Nigeria”, an article published in Journal of African Culture and International Understanding, No. 7 January – March, 2014, a UNESCO Category 2 Institute at the Olusegun Obasanjo Presidential Library, Abeokuta, Nigeria, page 26 – 31.
Sallau, B. A. , “Supernatural Forces In Hausa Trado-Medical Practices” (A Wanzanci Balance Sheet), (2014) being a paper presented at the 8th MICOLLAC 2014 International Conference on Languages, Literatures and Cultures, organised by the Department of English, Faculty of Modern Languages and Communication, Uniɓersiti Putra Malaysia, Serdang, at Rainbow Paradise Beach Resort, Tanjung Bungah, Penang Malaysia, from 12 – 14 August 2014.
Smith, M. G. (1957) "The Hausa System of Social Status" in Africa Vol. ƊƊƁII. No. 1.
The New International Webster’s Comprehensiɓe Dictionary of the English Languages, (2004) Deluɗe Encyclopedia Edition, Naples Florida, USA. Trident Press International, Typoon International.
Tsiga, I. A. (2014) “One Hundred Years of Karatun Boko: Education, Language and Ɓalue Change in Hausa Land, Address Deliɓered at the Presentation of the Book, Ruwan Bagaja in Perspectiɓes: Eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose (1933-2013), Umaru Musa Yar’adua University, Katsina.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.