Tarihin Muhammadu Hambali Junju

    An haife shi a 1936 a Junju da ke Æ™asar Nijar. Ya fito daga tsatson zuriyar Shehu Ahmadu Baba, shahararren Waliyyi, Æ™asaitaccen masani na Jami'ar Tumbuktu, wanda ya gadi sarauta da malanta. 
    Ya fara binciken kalmomin fasaha da kimiyya na Hausa a yayin da ya ke É—alibta daga 1960 zuwa 1961 a Jami'ar Dakar da ta AlÆ™ahira. 
    Ya kammala digirin da na uku a Kasko cikin watan Yuli na 1967 da gagarumin yabo. An wallafa littafinsa na farko a 1968.
    Ya yi aiki a Jami'ar Kiki daga 1972 zuwa 1974. A Jami'ar Ahmadu Bello kuwa daga 1974 zuwa 1979 da kuma 1982 zuwa1984. Ya jagoranci Cibiyar Nazarin Hausa da ke Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato a 1984. Ya gabatar da ayyuka masu tushen kansu bila adadin. Ƙwararre ne a fagen mallakar harsuna fiye da ƙima da suka danganci rayayyu da ma waɗanda suka gushe.
    Ya jagoranci tarurrukan ƙasashen duniya game da kalmomin kimiyya da ilimin fasaha na Hausa.
    Masani ne gaya a fannin ilimin ƙabilu da ilimin ɗan'adam da ilimin halin zaman jama'a da al'adu da magungunan Afirka da nazarin harshen Masar. Kaɗan ke nan daga cikin tarihinsa. Neman ƙarin bayani a tuntuɓi ƙwararru a wannan fage kamar Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau da Farfesa Ibrahim Malumfashi da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza.
    Daga
    Dr. Adamu Rabi'u Bakura
    Tarihin Muhammadu Hambali Junju:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.