Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
TATSUNIYAR DILA DA BIRI
Gatanan -
gatananku
An yi wani biri mai girma da ƙarfi, wanda yake ganin
babu wanda ya yi ƙarfinsa a wancan zamani, don haka ba ya tsoron kowa kuma ba ya tsoron komi,
koyaushe ya ci abinci ya ƙoshi sai ya ce “Allah ya kawo tashin hankali” shi kuma
malamin daji wato dila wannan maganar tana damunsa, koyaushe biri ya yi ta, har ma dila yakan kwatse shi ya ce “kai dai Allah
ya sawwake, tashin hankali ba kyau”. To wannan maganar tana ɓata ma biri rai har
ta tunzura shi! Da zarar dila ya ce haka sai biri ya
ji kamar ya mutu saboda zuciya, sai ya sake cewa “in ka san inda tashin
hankalin yake mu je ka kai ni” wannan maganar kuma ta dami malamin daji,
koyaushe biri ya yi masa ita sai dai ya haƙura ya haɗiye don haushi, da
mamakin yadda har wani zai yi ta neman tashin hankali! Daga nan sai dila ya yi
alkawalin nuna ma biri inda tashin hankalin yake, koyaushe suka ga juna babu
wata magana sai ita.
Wata rana dila ya fita wajen
yawace-yawacensa sai ya cimma magasa, wato inda ‘yan farauta suke gasa namun
dajin da suka farauto, ya lura da irin wulakancin da mafarauta suke yi wa
dabbobin da suka kaso, wani a feɗe shi a cire fatar, wani a tsire shi, wani a babbake har fatar, wani kuma a
yi masa gunduwa-gunduwa, da sauran nau’o’in cin mutunci iri-iri, wasu ma sai su
cire wani abu su jefar da wani abu, ga kuma makamai iri-iri sun aje gefe, ga
wani ƙamshin nama yana tashi, yara suna tariyar man da ke darara daga irin waɗannan dabbobin da ake gashi! Malamin dawa bai taɓa ganin iri tashin
hankalin da ya wuce wannan ba.
Bayan
ya dawo sai suka haɗu da biri, sai biri
ya yi irin addu’ar da ya saba, shi kuma dila sai ya ce “ka shirya zan kai ka
gobe”, ai da jin haka sai zumuɗi biri yake yi, kafin lokacin da dila ya sa masa har
yana cewa “wayyo ni biri zan haɗu da abin da nike nema” wato tashin hankali. Tun kafin
safiya ta waye sai biri ya iske dila ya ce “tashi mu je”, shi kuma malamin daji
ya ce wa biri “yi haƙuri mi kake tauna na baka na zuba?” Dila ya sani cewa
sai can da yamma ne tashin hankalin ya fi tsanani (wato lokacin gashi) don haka
bai yi wani uzuri ba, sai da ya ga lokaci ya matso sannan ya shiga gaba biri na
biya har ya kai shi gindin inuwar gashi, wato innuwar iccen da mafarautan ke
gashi idan sun dawo daga farautar! Biri ya ce “to ina tashin hankalin yake?”
Sai dila ya nuna masa kofatai da fatu da kanun waɗanda ake jefarwa, sai biri ya yi
tsaki mts! Ya ce, “wannan shi ne tashin hankalin?” Sai dila ya ce “ai wannan kaɗan ka gani, abin da
za a yi, ka hau wannan iccen ka laɓe zuwa an jima zaka ga tashin hankali”
Ɗaram, sai biri ya haye sama, da ma hawan bishi ga biri
gado ne, shi kuma dila ya ce “sai mun haɗu in sha labara”. Ya bar wurin da nisa
saboda tsoron kar tashin hankalin ya rutsa da shi. Biri sai waige-waige yake yi
don ya ga ta
inda tashin hankalin zai ɓullo, da an jinjima
sai ya yi tsaki ya ce “wai har yanzu tashin hankalin bai zo ba?”
Can da la’asar sansanya, sai biri
ya fara jin kiɗan mafarauta yana tashi, idan kiɗin ya matso sai ya tsaya har dai
aka iso gindin wannan bishiyar gashin, inda birin
yake jiran don ya ga bala’i. Biri ya fara ganin ana sauke matattun dabbobin da
aka kaso, daga ciki har da waɗanda ya sani domin akwai wani biri wanda ya fi shi girma! Sai jefar da su ake
yi tim! Tititim! Titim! Biri na ganin haka sai ya ƙara
fakewa, ya karyo wani reshen bishiyar ya kare idanunsa don kar
a gane shi!
Mafarauta
tare da yaransu sai fiɗa suke yi, suna
zagin wasu namun waɗanda aka sha wahala
wajen kamunsu, musamman wannan goggon birin! Bayan sun gama fiɗa sai ake haɗa gwami[1]. wuta ta
kama sai aka fara gashi, biri yana dai sama abin duniya ya dame shi, babu halin
ya sauko don ya san ko yaransu bai tsere ma da gudu, balle manyan! Ƙamshi
sai tashi yake yi, a janye wannan a sa wannan har dai suka gama, suka kwashi
kayansu suka yi gaba. Da biri ya ga sun tafi ba a bar kowa ba sai yara masu
nawar gashi, sai ya buɗe fuskarsa ya fara
karyo ‘yan itatuwa ta jefo su ƙasa, idan ya jefa cikin wuta sai
yaran su ɗauke su aje gefe,
har wani ya ɗaga kai sama ya ga
biri, sai ya fara ihu yana cewa kai jama’a ku dawo biri a sama, to da ma manyan
ba su yi wani nisa ba, sai suka shiga dawowa, sai da suka taru sai aka fara
harbin biri da kibau, wasu su yi jifa da duwatsu, wasu da sanduna! Idan ya yi
tsalle a wannan reshe ya koma wancan. Can sai wani ya sami biri ga ciki da
kibiyarsa, sai kuwa birin ya faɗo ƙasa tim! A buga a buga har dai ya
gudu da kibiya soke ga cikinsa.
Ko
da dila ya hangi biri aguje sai ya mayar da gaba Gabas ya fara sallah, har ya
iso, yana wata irin ƙyaƙya[2], yana
kama kibau ya girgiza shi ya busa iska yana faɗuwa yana tashi, amma dai dila bai
damu ba sallarsa kaɗai yake yi, said a
ya ga biri ya fara laushi sai ya sallame, da biri ya gay a sallame sai ya fara
murna, shi kuwa dila sai ya tashi ya ƙara kabbarawa. Da
ya fajimci biri ya fara galabaita sai ya sallame sallar, ya riƙa
masa suka cire kibau. Daga nan sai malamin daji ya ce “Allah ya raba mu da tashin
hankali” sai biri ya yi farat ya ce “amin malam – amin malam”,
Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya
tsamo ni.
Tambayoyi
1.
“Kowa ya ƙi ji ba zai ƙi gani ba” tattauna
wannan karin magana kamar yadda take a wannan tatsuniya.
2.
Mene ne tashin hankali
a cikin wannan tatsuniyar?
3.
Waɗanne irin darusa ne aka koya daga
wannan tatsuniyar?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.