TATSUNIYAR DILA DA KURA

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Tatsuniyar Hausa

    TATSUNIYAR DILA DA KURA

    Gatanan - gatananku

    Wani dila ne ya sami wani gidan Fulani ya riÆ™a zuwa kullum yana shan Æ™wan zabbi, koyaushe haka yake yi, saboda haka ya fara yin kashin wannan shagalin! Ita kuma kura tana yawonta sai ta fara ganin kashin dila, da ta sunsuna sai ta ji wani irin Æ™amshi, don haka sai ta lashe! Ai kuwa sai ta cigaba da yawo don ta nemi wannan kashin, idan ta samu sai ta riÆ™a cinyewa, har ta raya a ranta cewa duk mai yin wannan kashin Allah kaÉ—ai ya san irin shagalin da yake yi. Ta ce “Ubangiji Allah ya haÉ—a ni da mai yin wannan kashin.

    TATSUNIYAR DILA DA KURA

    Daga nan sai kura ta fara fakewa tana son ta gamu da mai yin wannan kashin, ai kuwa sai ga dila ya gitta ta wurin, har ya sake yin irin wannan kashin. Sai nan take kura ta fito ta ce ashe kai malamin daji kai ne kake yin kashin nan? Bayan ta cinye wannan sai ta ce ma dila “malam Æ™aro kashi”, Dila ya Æ™ara kashin, kura ta lashe, ta sake cewa ya Æ™ara, haka dai suka cigaba da yi har dila ya kai baya iya yin wani kashin! Sai kura ta ce da shi sai ya kai ta inda yake shan wannan shagalin da har yake irin wannan kashi mai daÉ—in É—anÉ—ano. Dila bai tsaya wata gardama ba saboda sanin halin kura sai ya shiga gaba kura ta bi shi, bai tsaya ba sai gidan Fulani inda yake shan Æ™wai.

                Dila yana ganin Æ™wai sai ya ce: 

    “Na ga kwarkwatatta wurin É—ibar kwamma”

              Sai kura ta ce:

    “Kwashangyalat, aje shi nan, ni na aje shi

    Dole sai dila ya bar ma kura ƙwan ta shanye! Ana haka duk lokacin da dila ya ga ƙwai sai kura ta ce nata ne, dole dila ya bar mata ta shanye. Dila dai bai sha ƙwai ko guda ba. Ana cikin haka sai dila ya hangi ƙwai a cikin kogon itace, sai ya ce:

    “Na ga kwarkwatatta wurin É—ibar kwamma”

    Sai kura ta ce:

    “Kwashangyalat, aje shi nan”

    Sai kuwa kura ta ce ai dama ita ta ce a aje mata shi a nan, rayuwar dila ta É“aci sosai, kura ta hana shi ya yi kalaci!

    Kura ta duba cikin kogo ta ga Æ™wai, ta kara kanta amma kash! Kan kura ya Æ™i shiga kogon! Sai ta roÆ™i dila ta ce malamin daji a yi man addu’a don kaina ya shiga cikin kogon nan. Sai ya ce to, ya yi mata burga, ya samo wani ganye mai yauÆ™i, ya shafa wa bakin kogon, sannan ya ce kura ta gwada a gani, aza kan kura ke da wuya sai dila ya dawo bayanta ya daddage ya tura ta har kan ya shige, daga nan sai ya É—ebo yashi ya goge yauÆ™in nan da ya sa, sannan ya koma baya ya É—auko gangarsa ya fara kiÉ—in farauta! Sai kuwa ya sake murya ya ce “kai jama’a ku yo gaba ga dila cikin Æ™aya!” Ya kuma sake murya yana cewa kai dilan mi ga kura kogo! Ai kuwa sai dila ya sami faskare lafiyayye ya fara jibgar kura, kura ta yi duk irin yunÆ™urin da take yi ta fito kanta ya Æ™i fita, shi kuwa dila sai kiÉ—i yake yi yana jibgar kura tana zawo.

    TATSUNIYAR DILA DA KURA

    Sai can kura ta fizga kanta da Æ™arfi ta fito da shi duk fatar kanta ta kware, ai kuwa bata tsaya wata-wata ba sai ta arce a guje ta nufi gidanta. Shi kuma dila ya bi ta ‘yar kurÉ—e ya riga ta gidan, ko da ta zo sai dila ya ce yau mun sha kashi! Kura ta ce ai naji lokacin da ake cewa mi muke yi da dila a cikin Æ™aya ga kura kogo? Ita ba ta san dila ne ya doke ta ba. Sai dila ya ce sai an jima, ya tafi ya bar kura tana jinyar dukan da ta sha, da kuma kwarewar da kanta ya yi.

    Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

    Tambayoyi

    1.                  Ko kun yarda cewa shagali na sa a yi kashi mai daÉ—i?

    2.                  Wane sakamako kura ta samu a kan zaluncin da ta yi wa dila?

    3.                  WaÉ—anne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.