Tatsuniyar gizo da mata mai sa.

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Tatsuniyar Hausa

    Tatsuniyar gizo da mata mai sa.

    Ga ta nan, ga ta nan ku

    Wata rana wata mata tana tallar santa, amma idan mutum ya saya biyan shi ne, idan shekara ta zagayo ya faɗi sunanta. Wanda ya karɓi san idan shekara ta gewayo ya kasa tuna sunan nata, to za ta jefa shi cikin ruwan gulbi[1] ya mutu.

    Matar nan ta dinga  bi rariya-rariya, lungu-lungu, titi-titi, tana shela, tana cewa, “ku sai sa, ku sai sa”. Da mutum ya kira ta, ta faÉ—a masa yadda za a biya san, sai ya fasa. Ana cikin haka, sai Gizo ya sami labari, kuma aka gaya masa sharuÉ—É—an karÉ“ar sa, sai ya amince. Mata mai sa ta ba Gizo san, sannan kuma ta shaida masa sunanta, wato “Allazi take matar Lazi amanu”. Gizo ya tafi da sa gida yana murna.

    Tatsuniyar gizo da mata mai sa.

    Da isar sa ya faÉ—a wa matarsa ƘoÆ™i yadda aka yi har ya sami Æ™aton sa. Ya kuma ce “ke ce ba ki da mantuwa, don haka ki riÆ™e sunan tsohuwar nan da kyau”.

    A halin da ake wannan zance, da ma can Gizo ya yi sabuwar amarya wato abokiyar zaman Ƙoƙi, amma kuma bai son ta sosai, sai kawai aka gaya mata ta riƙe sunan matar nan, ba tare da ta san wani abu game da sa ba.

    Gizo ya yanke sa ya sa ƘoÆ™i ta soye shi raÉ—au, amma ya jaddada mata cewa, “ba na son amarya ta ji ko Æ™amshin wannan nama”.

    Sai Ƙoƙi ta yi farin ciki domin an sosa mata inda yake yi mata ƙaiƙayi. Ta yi ta suyar nama har ta ƙare ƙaf. Da ya huce aka kai shi cikin ɗaki, suka yi ta shagalinsu ba tare da amarya ba. Da sannu-sannu nama ya ƙare.

    A kwana a tashi shekara ta zagayo, sai matar nan ta zo wurin Gizo wanda ya ɗauki alƙawarin faɗin sunanta. Haba ina! Gizo ya manta da sunan mata, ballantana sa da aka soye masa ya cinye. Ita ma uwargidansa Ƙoƙi ta mance da sunan matar. Sai kawai matar ta ja Gizo za ta kai shi rafi ta jefa. Tirƙashi!

    Tatsuniyar gizo da mata mai sa.

    Rana ke nan take ƙoƙarin ɓaci wa Gizo, babu abin da Ƙoƙi za ta iya yi sai kallo. Matar ta ja Gizo a ƙasa ta soma kama ƙafafun Gizo, ga shi kuma yana cikin tsananin wahalar jan da aka yi masa a ƙasa.

    Tatsuniyar gizo da mata mai sa.

    To ashe amaryar Gizo ba ta mance da sunan matar ba. Don haka, ta aiki yaro ta ce “ sheÆ™a da gudu ka gaya masa cewa ga yadda sunan matar yake. Sai yaro ya ruga aguje, ya cim ma Gizo, ruwa kuwa har ya kai ga kunkurunsa. Da isar sa bakin rafin, sai ya rera waÆ™a yana cewa:

    Kai Gizo, kai Gizo,

    Sunan matan nana

    Allazi take matar Lazi amanu

    Daga can sai Gizo ya ji wannan waƙa, sai ya yi farat ya caɓa, yana maimaita cewa:

    ‘Allazi take matar Lazi tsuliya’

    Haba, sai matar ta ƙara yin gaba da Gizo,

    wannan karon har ruwa yana kusa ya nutse shi. Shi kuma yaro ya daÉ—a cewa:

    Kai Gizo, kai Gizo,

    Sunan matan nana

    Allazi take matar Lazi amanu

    Sai matar nan ta saki Gizo, ya samu ya fito daga ruwan da sauri. Alla-alla Gizo yake yi ya iso gida. Da isowarsa, ya hau Ƙoƙi da faɗa yana cewa:

    “Ashe ƘoÆ™i ba ki sho na,

    Kika Æ™yale ni za a kashe ni”.

    Nan da nan yamutsi ya kaure tsakanin Gizo da uwargidansa Ƙoƙi, har ta kai ya sake ta, ya zauna da amaryarsa lafiya wadda ita ce ta nuna masa ƙauna ta cece shi daga halaka. Daga nan gizo ya gane cewa ba koyaushe wanda kake so yake son ka ba .

    Ƙungurus kankusu, ba don Gizo da amaryarsa ba da na yi ƙarya. Da ma ƙaryar ce na shimfiɗa maku.

    Tambayoyi

    1.                  Wane dalili ne ya sa jama’a da yawa suka Æ™i sayen san Tsohuwa?

    2.                  Mata nawa gizo yake da su? Ko yana yi masu adalci?

    3.                  WaÉ—anne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?




    [1]  Kogi.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.