Tatsuniyar Halilu Da Akilu

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Tatsuniyar Hausa

    Tatsuniyar Halilu Da Akilu

    Gatanan - Gatananku

    A wani gari an yi wasu yara ne su biyu babansu guda, amma ba uwarsu  guda ba, Sunan É—ayan Halilu shi kuma guda an ce masa Akilu. Akilu yana da shanu da yawa da kare, su kuma su Halilu ba su da ko ‘yar akuya! Wata rana sai mahaifiyar Akilu ta tambayi mahaifiyar Halilu ta ce “in faÉ—i in mutu kuna riÆ™e man É—ana amana?” Sai mamar Halilu ta ce “eh”, kamar wasa sai kuwa ta faÉ—i ta mutu! Bayan wani É—an lokaci, sai kishi ya taso ma uwar Halilu, ganin irin yadda Allah ya hore masa arziki bai ba É—anta ba. Ta yi ta yi ta ga ya koma baya, amma dai ina AÆ™ilu sai gaba yake ciga harkokinsa. Wata rana sai ta shinkafa da miya ta sa masa kitse da man shanu ta haÉ— da guba don ya ci ya mutu su huta! Akilu bai sani ba yana wurin kiyo, yana kiyonsa tare da karensa sai ya ji karen ya fara waÆ™a yana gaya wa Akilu yana cewa;

                “Kai Akilu zam-zam-zam

    Shinkafar gidanku zam-zam-zam

    Kar ka cita zam - zam -zam

    Kashe ka za a yi zam - zam -zam

    A anshe shanun zam - zam -zam

    Tatsuniyar Halilu Da Akilu

    A ba Halilu zam - zam –zam”.

    Da AÆ™ilu ya ji wannan bayanin sai ya ce ma karen “da gaske kake yi?” Shi kuma ya ce “eh” sai ya yi godiya, da lokacin tashinsa kiyo ya yi sai ya tashi ya koma gida, da isarsa sai matar ta ce  “AÆ™ilu zo ka ci abinci” sai ya ce “a’a na na Æ™oshi domin na ciyo daga gidan abokina”, sai ya shige É—akinsu ya kwanta har ya yi bacci, da safiya ta yi, sai ya tafi wurin kiyon dabbobimsa kamar yadda ya saba. Bayan fitarsa sai kishiyar uwar tasa da girka tuwo, shi ma aka sa kitse da man shanu aka sa guba! Yana can wurin kiyon sai karensa ya fara waÆ™a yana cewa:

    “Kai Akilu zam-zam-zam

    Tuwon gidan ku zam-zam-zam

    Kar ka ci shi zan-zan-zam

    Kashe ka za ai zam-zam-zam

    A anshe shanun zan-zan-zam

    A ba Halilu zan-zan-zam”.

    Tatsuniyar Halilu Da Akilu

    Sai AÆ™ilu ya dafa karen ya kuma tambaye shi ya ce “da gaske kake yi?” Karen ya ce “eh”, saboda jin haka sai ya yi dare bai dawo gida ba, yana komawa gida sai ya kwanta ya yi bacci abinsa, da safiya ta waye sai kishiyar uwar ta je wurin bokanta ta ce “maganin bai yi ba”, sai ya ce “ta koÉ—a wuÆ™a in dare ya yi AÆ™ilu ya kwanta yana barci sai ta yayyanka shi!” Lokacin da ya tafi wurin kiyo sai karensa ya fara waÆ™a a ciki yana faÉ—in:

    “Kai AÆ™ilu zan-zan-zam

    Inka koma gida zan-zan-zam

    Ka cire kayanka zan-zan-zam

    Ka sama halilu zan-zan-zam

    Ka cire nashi kasa gare ka zan-zan-zam

    Ka É—auke halilu zan-zan-zam

    Ka kai shi wurin kwanan ka zan-zan-zam

    Ka kwanta wurin kwanan shi zan-zan-zam”

    Tatsuniyar Halilu Da Akilu

    Yana komawa gida ya yi haka nan, ai sai ta yanke ɗanta, ta yi mai gunduwa-gunduwa ta zuba cikin buhu! safiya ta yi Aƙilu ya tsere babu abin da ya same shi. Ita kuma sai kuka da ihun baƙin cikin muguntar da ta yi wa kanta.

    Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

    Tambayoyi

    1.  Yaya dangantakar Halilu da AÆ™ilu take?

    2.  Wa ya riÆ™a ceton AÆ™ilu daga cin gubar da aka sa masa a cikin abinci?

    3.  WaÉ—anne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.