Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Tatsuniyar Sarkin Raggaye
Gatanan - Gatananku
Wani mutum ne yake zaune a wani
gari, to shi mutumin bai da wani aikin fari balle na baƙi sai hutawa kawai,
kodayaushe sai dai ya yi ta zaman shan innuwa, idan wannan ta janye sai ya
tashi ya koma wata inuwar, babu wata innuwar garin da bai san da zamanta ba. Saboda haka sai
mutanen garin suka sa masa suna sarkin raggaye, wai shi baya iya aikin komai
kodayaushe sai biyar innuwa yana kwantawa don hutawa.
Wannan
halayya tasa ce ta sa kowa ya rena shi a cikin garin, har baya da ikon sa
bakinsa a cikin maganarsu! Da ya gaji da halin mutanen wannan garin nasu, sai
ya riƙa fita garin yana zuwa bayan gari, sai in dare ya yi ya
dawo, da safe idan ya tashi sai ya je cikin daji inda babu kowa ya sami inuwa
ya ci gaba da zaman raggancinsa, idan wannan inuwa ta ƙare
ya je wata. Wata rana sai ya je wata innuwa mai sanyi ta wata bishiya ya
kwanta, yana kwance har bacci ya kwashe shi, yana cikin bacci ashe akwai maciji
a kan bishiyar, sai maciji ya sauko ya ce “kai wannan bawan Allah don Allah
tashi ka shareman innuwata” sai ya ce “kai wannan maciji in ba wautarka ba? wa
ka taɓa jin ya sa ni
aiki?” “ba don gudun aikin na fito gari ba na dawo daji?” kuma kai yanzu har ka
isa ka sani aiki?” “Wallahi bani iyawa”
Sai
ya ce “don Allah ka taimaka ka share man wannan innuwar”, ya sake cewa “a a
wallahi ban iyawa, kai ba ka isa ka sa ni aiki ba”. Macijin dai ya yi ta
rarrashinsa har dai ya shawo kansa, sai ya fara share masa innuwar da ya kai inda
rana sai ya dawo, don kar ya ji zafinta, yana gama sharewa sai ya ce masa “to nagode, tunda ka
share man ni ma zan yi maka wata kyauta” sai macijin ya ba shi wata jaka ya ce
masa “yanzu ka koma gari duk wanda ya sake kwatsuwarka ka buge shi da wannan
jikar zai koma jaki”, “sai ka kama ka sayar da abinka”. Sai kuwa sarkin raggaye
ya karɓa ya ce “to nagode
Allah ya saka da alheri”, sai ya dawo cikin gari ya riƙa
zagayawa, a duk in da ya iske mutane suna gardama, sai ya zo ya tsumbula
bakinsa ya ce “kai ku tsaya ku tsaya”, sai wani daga cikinsu ya ce “kai yanzu
har ka isa ka ba mu umurni mu ji? don kana wa?” “Kai ma da kake sarkin raggaye
me ka amfana?” shi kuma sai ya ce “idan baka bari ba, yanzu ina mayar da kai
jaki” Sai mutumen ya ce “ho ɗan neman shawaraki! wa za ka mayarwa jaki?” ai kuwa sai
ya buga masa jakar! Sai kawai a ga ya fara komawa jaki! sai ka ji kawai mutum
yana kukan jaki “uugghhmm- uugghhmm-uhm-uhm” kawai sai a ga jaki ya tashi yana
kuka, shi kuma ya kame shi ya ɗaure.
Haka ya dinga yi idan ya mayar da mutun jaki sai ya sa igiya ya ɗaure shi. Da haka nan-da haka nan har ya tara jakai masu yawa, ya riƙa kai wa kasuwa yana sayarwa yana samun kuɗi. Wannan sana’ar tasa ta sa mutanen garin suka shiga taitayinsu, ba a sake rena shi ba, har tsoransa ake ji, duk abin da ya ce ko ba gaskiya ba ne dole a ce gaskiya ne don tsoron kar ya mayar da mutum jaki. Ya zama babban mutum a cikin garin, ko sarkin garin ba ya gardama da shi bare ya kwatse shi. Duk lokacin da sarki ya ce kaza, idan sarkin raggaye bai aminta ba sai sarkin ya ce ƙarya nike yi! Likkafar sarkin raggaye sai gaba take yi babu abin da za a yi a garin sai ya yarda da shi, har maroƙa suna yi masa kirari suna cewa “kaway yi ba da kai ba ta tashi! Shi ya sa har yanzu Hausawa suke amfani da wannan karin maganar.
Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.
Tambayoyi
1.
Me ya sa duka jama’ar
gari suka rena sarkin raggaye?
2.
Wace riba ya samu ga
wannan halayya tasa?
3.
Waɗanne irin darusa ne aka koya daga
wannan tatsuniyar?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.