Tatsuniyar Tallar San Birai

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Tatsuniyar Hausa

    Tatsuniyar Tallar San Birai

    Gatanan – gatananku

    Wasu birai ne suke da wani Æ™aton sa, kuma suke son su sayar da shi, suna zagaye tunga-tunga suna tallarsu ga kowa da kowa. Duk inda suka je sai su ce kuna sayen sa? Idan an ce eh, sai a tambaye su nawa san yake? Sai su ce ai san baya da tsada, “kullun mu zo mu ba mutum kashi bakin sanmu”, sai mutanen su ce “kai don Allah ku tai ku ba mutane wuri, saboda sa kullum sai a ba mutum kashi?” Sai su wuce.

    Tatsuniyar Tallar San Birai

    Bayan sun ga cewa mutane sun Æ™i sayen sansu, sai su wuce wata tungar, suna ta yin haka har suka isa wata tungar, a can suka iske wata tsohuwa, wadda ta kira su ta tambaye su nawa ne kuÉ—in sansu? Sai suka ce; sanmu ba tsada, kullum sai mu zo mu ba mutum kashi mu tafiyarmu. Ita kuma tsohuwa babu wani abun da take tinÆ™aho da shi sai surukanta guda uku, masu auren ‘ya’yanta uku, babbar ‘yar Zaki yake aurenta, ta biyu kuwa damishi, ta ukun ce karen gida ke aure. Sai kuwa ta ce wa birai to na saye ku shigo ku É—aure man shi nan, na saye ku rinÆ™a zuwa kuna ba ni kashin kullum.

    Safiya na yi kuwa sai birai suka shiga daji suka yo damen buloli, babban ya É—auko ya shigo gaba, da zuwa kofar gidan tsohuwa bai tsaya ba sai kofar É—aki, ya aje damen buloli tim! ya ce “assalamu alaikun tsohuwa gamu mun zo”. Tsohuwa kuwa ta fito ta miÆ™a bayanta suka yi ta bugu har suka gama, suka ce to tsohuwa mun tafi sai gobe in mun dawo. Tsohuwa ta koma É—aka tana darzar kuka. Gobe ma suka sake zuwa da damen tsuma babban ya aje tim!

    Tatsuniyar Tallar San Birai

    Ya ce tsohuwa fito gamu mun zo, sai ta fito ta kuma sake miÆ™a masu bayanta suka yi ta zane ta har ta yi taushi, sannan suka tafiyarsu suka ce “sai gobe in mun dawo”.

    Wanshekare sai ga zaki ya zo wajen ganin surukarsa wato tsohuwa, sai ya iske ta a kwance tana nishi! Sai ya ce “tsohuwa lafiya kike Æ™unnai[1]?” Sai tsohuwa ta ce, “wai wasu birai ne suke zuwa kullum suna ba ni kashi don na sayi sansu!” Sai zaki ya ce “ko yau suna zuwa?” Sai ta ce ai kullum sai sun zo, sai zaki ya ce; “yi shurun ki, wannan matsala tamu ce”, “ke baruwanki, Æ™yale ni da su”.

    Tatsuniyar Tallar San Birai

    Can sai ga sallama ta babban birin nan, sai zaki ya tambayi tsohuwa “Wancan mai sallama da tsauri har cikin kai wane ne?” sai tsohuwa ta ce Birai ne, wannan muryar babbansu ce”, sai zaki ya ce wa tsohuwa, tsohuwa ba wata Æ™ofa a É—akinki? Ta ce “a’a”. Sai kuwa ya banki bangon Gabas na É—akinta, kun san zaki da Æ™arfi, sai ya buge bangon, ya yi Æ™ofa ya bi ya hurce ya tafiyarsa!

    Tatsuniyar Tallar San Birai

    Tsohuwa ta fito suka ba ta kashi suka gama suka ce sai gobe in mun dawo.

    Gobe kuma sai ga Damishi ya zo wajen ganin surukarsa wato tsohuwa, sai ya iske ta a kwance tana nishi! Sai ya ce “tsohuwa lafiya kike Æ™unnai?” Sai tsohuwa ta ce, “wai wasu birai ne suke zuwa kullum suna ba ni kashi a kan sansu!” Sai Damishi ya ce “ko yau suna zuwa?” Sai ta ce “ai kullum sai sun zo”, sai Damishi ya ce; “yi shirunki, wannan matsala tamu ce”, “ke baruwanki, Æ™yale ni da su mu za a yi wa shegantaka?” Can sai ga sallama ta babban birin nan, sai Damishi ya tambayi tsohuwa “Wancan mai sallama da tsauri har cikin kai wane ne?” sai tsohuwa ta ce “Birai ne kuma waccan muryar babbansu ce”, sai ya ce “waccan hanya tsohuwa wa ya yi ta?” tsohuwa ta ce “zaki ya yi ta”. Sai ya ce “ai ni ma ita zani biya, ya bi ta nan ya sulale!.

    Tatsuniyar Tallar San Birai

    Tsohuwa ta fito suka ba ta kashi suka gama suka ce sai gobe in mun dawo.

    Kafin lokacin zuwan birai kuma sai ga karen gida ya zo wajen ganin surukarsa wato tsohuwa, sai ya iske ta a kwance tana Æ™unnai! Sai ya ce “tsohuwa lafiya kike Æ™unnai?” Sai tsohuwa ta ce, “ba lafiya uwaka! ÆŠan neman mutumin banza”, Sai kare ya sake cewa “tsohuwa ki yi haÆ™uri ki gaya man yadda aka yi?” ita tsohuwa tana ganin cewa zaki ya kasa, damishi ya kasa to balle kare. Ya dai cigaba da rarrashin surukar tasa har ta gaya masa,   Sai ta ce; wai wasu birai ne suke zuwa kullum suna ba ni kashi a kan sansu! Sai Kare ya ce “ko yau suna zuwa?” Sai ta ce “ai kullum sai sun zo”, sai karen ya ce; “kwantar da hankalinki, wannan matsala tamu ce, ke baruwanki, Æ™yale ni da su, mu za a yi wa shegantaka?” Idan sun zo ko sun yi sallama kar ki amsa, kyale su. Can sai ga sallama ta babban birin nan, sai Kare ya tambayi tsohuwa “Wancan mai sallama da tsauri har cikin kai wane ne?”

    Tatsuniyar Tallar San Birai

    Sai tsohuwa ta ce Birai É—in ne, sai ya ce kar ki amsa kyale su, da birai suka ji sun yi sallama ba a amsa ba, sai suka ce ko tsohuwa ta mutu? Sai wasu daga cikinsu suka ce “ai ko ta mutu sai mun buga”, suka ce ma babban “kai dai shiga ka fito mana da ita” Shi kuma kare da ma ya laÉ“e bakin Æ™ofa, babban birin nan ya miÆ™o kansa sai kare ya cafke wuyansa a daidai maÆ™ogwaronsa, sai suka yi gumu[2] a cikin É—akin tsohuwa, sai kokawa suke yi kowa na Æ™ara, su ko birai suna ta kirari (sun É—auka tsohuwa ce aka kamo), suna cewa “yawwa babba jawo ta, jawo mana mu buga”, shi kuwa ta Æ™watar ransa yake yi. Ai da suka dunkule da wata kokawar sai waje gaban sauran biran,

    Tatsuniyar Tallar San Birai

    Lokacin har babba ya yi taushi, amma kare bai sake shi ba, sai da rai ya yi halinsa (ya mutu). Da ganin haka ai sai sauran kowa ya ranta a cikin na kare! Sai tsohuwa ta ce ashe kare ya fi zaki da damisa zuciya. Tun daga nan tsohuwa ta sami lafiya, ba wanda ya sake zuwa balle ya ba ta kashi, ta É—auki kare da mutunci fiye da sauran.

    Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

    Tambayoyi

    1.                  Daga wannan tatsuniyar nawa ne kuÉ—in san birai?

    2.                  Daga cikin surukan tsohuwa wane ya fi Æ™arfi? Wane daga ciki ya taimaki tsohuwa?

    3.                  WaÉ—anne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?



    [1]  Nishin wahala.

    [2]  Kokawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.