Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Tatsuniyar Hausa

    Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

    Gatanan – gatananku

    Wani malami ne yake zaune a wani gari wanda yake da rufin asiri, kuma kowa yana mamakin wannan rufin asirin nasa saboda shi dai ba ya yin aikin komi, kuma ba ya da wata sana’a sai karance-karancensa kawai. Abinci kuwa a gidan malam sai kowa ya ci ya bari. Babban abin mamakin mutanen wannan gari shi ne; malam ba ya saye, balle sayarwa, ba ya zuwa ko’ina balle ya biÉ—o abinci.

    Wannan lamari na malam ya cigaba da ba kowa mamaki. Ashe malam wata addu’a ce yake yi sai abinci ya faÉ—o masa daga sama kowane iri yake so! Da zarar ya so tuwo sai ya ce “Tuwo tutui-tutui” sai ko tuwo ya yi ta saukowa har sai ya ishi kowa.

    Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

    Idan kuma ya sake buÆ™ata sai ya yi haka, babu wata matsala da ta dami malam sai dai ya yi ta karatunsa. Ko da ya gaji da wannan sai wata rana ya je a rafin da ke bayan garin ya faÉ—a ya tsamo wani yaro ya zo da shi gida, amma kafin ya je gida da shi sai ya tambaye shi “mene ne sunaka” yaro ya ce “suna na girgiza mani” sai ya ce “ya ya kake da wannan sunan?” Sai yaro ya ce ai da mutum ya ambaci sunana sai kawai in riÆ™a girgza kaina hatsi na zuba! Nan take sai malam ya ce “girgiza mani” sai kuwa ya fara girgiza kansa dawa ta fara zuba! Sai da malam ya tsayar da shi.

    Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

    Sai malam ya tambaye shi cewa; “mice ce al’adarka idan ana son a ajiye ka?” Sai ya ce idan ana so a aje shi, sai an sami yashi mai kyawo, a sa shi a wuri mai kyawo, a riÆ™a jiÆ™e shi da ruwa mai kyawo sannan a sa ni ciki in zauna”, sai malam ya É—auke shi ya kai shi gidansa, ya sami wani É—aki mai kyawo ya sa shi, ya bi duk Æ™a’idojinsa. Duk lokacin da ya so hatsi sai ya shiga É—akin ya ce masa “Girgiza mani” sai shi kuma yaron ya yi ta girgiza kansa dawa tana zuba! Sai ya kwashe ya tara, abinci ya samu.

    Ana nan-ana nan sai labarin wannan malami ya kai ga sarkin garin cewa ga hidimar da yake yi wa yaro, shi kuma yaro yana samar masa da abinci kowane iri yake so, sai sarki ya sa aka É—auko masa shi, ya tambaye shi cewa wannan maganar da ya ji ko gaskiya ce? Malam ya ce “haka ne,” sai sarki ya ce “to a zo da yaron in gani da idona”, aka kawo yaron a Æ™ofar gidan sarki, malamin ya ce masa “Girgiza mani” sai kuwa sarki ya ga tsaba na zuba babu Æ™aƙƙautawa[1]! Da ganin haka sai sarki ya kwace yaron ya ce a gidana ne ya fi dacewa, ya sa aka kori malam!

    Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

    Sarki ya sa aka gina ma yaro sabon É—aki ya sa shi a ciki amma bai bi Æ™a’idojin yaro ba kamar yadda malam ya yi. Da farko yaro ya fara girgiza ma sarki har ya huta da sayen dukan kayan abinci, amma da zafi ya dame shi wata rana sarki na buÉ—e Æ™ofa sai kawai yaro ya fito aguje! Sarki bai yi wata-wata ba sai ya biyo shi da gudu.

    Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

    Da zuwa rafi sai kawai yaron ya faÉ—a a ciki, sai kuwa sarki ya ce da wa aka haÉ—a ni ba da kai ba? Shi ma ya faÉ—a ruwa ya bi shi don ya kamo shi, bai daÉ—e da shiga ba sai ya lalabo yaro, amma kash! Ba wancan da ya gudo ba ne. Ko da ya fito da shi bai tsaya koina ba sai cikin É—akinsa, ya yi, ya yi amma yaro ya Æ™i yin komai! Sai ya sa fadawansa da su nemo masa malam duk inda yake. Fadawa suka bazama wajen neman malam har suka gano shi, suka zo da shi gaban sarki.                          

    Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

    Sarki ya ce wa malam ya gaya masa yadda ya yi a lokacin da ya sami yaron nan. Malam ya ce masa, lokacin da na tsamo shi cikin ruwa sai da na tambaye shi sunansa, sannan na tambaye shi al’adarsa. Da jin haka sai sarki ya gane kuskurensa na rashin binciken yaron, sai ya ce a saki malam, aka sake shi ya tafiyarsa.

    Sarki ya tafi wajen yaronsa, ya ce “kai yaro mene ne sunanka?” sai yaro ya ce “sunana Ƙwaƙƙwala mani” Sarki ya ce “To yaya al’adarka take?” sai yaro ya ce “ÆŠaki ake sa mu ni da wanda ya tsamo ni a kulle kar a buÉ—e sai mun Æ™are da shi, komai aka ji yana faruwa” Sarki ya Æ™ara gyara zama, ya ce wa fadawansa “a rufe mu ni da yaro a cikin É—aki, komai aka ji kar a buÉ—e sai mun buÉ—e da kanmu”.

    Bayan an yi hakan sai sarki ya ce “Ƙwaƙƙwala mani” ai kuwa sai yaro ya sa kulki ya yi ta Æ™wala ma sarki, sarki yana ta ihu amma yaro ba ya kula jibgar[2] sarki kawai yake yi! Tun fadawa suna jin Æ™arar sarki har suka ji shiru!

    Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

    Sai da yaro ya ga sarki ya bar motsi sannan ya buɗe ƙofa ya ruga aguje ya faɗa ruwa a inda sarki ya tsamo shi.

    Shi kuma malam da ya wuce sai ya koma rafi ya sake kamo yaronsa na farko, ya kuma koma gidansa na da, ya cigaba da yi masa kamar yadda ya saba. Sarki ya mutu saboda jibgar da yaron ya yi masa! Sai mutanen gari suka ce; wa za su ba sarautar garin ba malam ba?

    Tatsuniyar Tsintuwar Yaron Malam

    Malam ya zama sarkin garin ya kuma cigaba da kyautata ma jama’ar garin kamar yadda yake yi a da, kowa ya yi murna, har wasu talakawa da fadawa sukan ce sun haÉ—u da lailatul Æ™adari, don ya hi tsohon sarki!

    Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

    Tambayoyi

    1.                  Mene ne sunan yaron da malam ya tsinto? Kuma mece ce al’adarsa?

    2.                  WaÉ—anne dalilai kuke ganin suka sa yaro ya gudu daga gidan sarki?

    3.                  WaÉ—anne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?




    [1]  Saurarawa/dakatawa.

    [2]  Duka da wani babban abin bugu.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.