Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
TATSUNIYAR WANI MAGIDANCI DA KWARTO
Gatanan - gatananku
Wani
mutum ne wanda talauci ya dame shi har ya rasa wata hanyar da zai sami sauƙi!
Ita kuma matarsa Allah ya yi mata arziki babu abinda ta rasa. Ya nemi matar da
ta ranta
masa kuɗi ko da fam biyar
ne, amma ta ƙi ranta masa, wai don
gudun kar ta bashi ya ƙi biya, ka san halin mata masu kuɗi. Amma akwai wani kwarto wanda ya matsa ma
wannan mata (matarsa), an yi ta gaya masa cewa kwarto yana zuwa gidansa duk
lokacin da baya nan, amma dai bai kula ba. Wata rana ya yi sallama da matarsa
zai yi tafiya wajen cin rani, da jin haka sai ta sanar da kwartonta
cewa “maigida zai yi tafiya”, mai gidan ya ɗaure kayansa ya bi jama’ar unguwarsu da na
garin yana gaya masu cewa zai yi tafiya, duk suka ce Allah ya kiyaye hanya.
Ko da ya bar garin sai ya sami
wani loko ya ɓoye, sai da ya bari dare ya raba
sannan ya dawo gidansa, yana shiga cikin gidan sai ya iske matarsa tare da
kwarto, sai ya ja da baya ya ce; yau kwananka ya ƙare, sai kuwa ya danƙara masa kulki tim! Kwarto ko wani
motsi bai yi ba ya mutu! Daga nan sai ya ce wa matar “ni na tafi”, sai ta ce
don Allah ka tsaya! Shi kuma sai ya ce “Ni yanzu zuwa nike yi wajen Maigari in
shaida masa cewa kin fara kashin mutane” ba sai hankalinta ya tashi ba? Ta ce
don Allah ka bari in baka hwanɗari, ya ce a a shi hwan ɗari ba ta sa ya yi ɓoyon mutum matacce,
ta ce ina ba ka hwan ɗari biyu, ya ce “a
a”, sannu-sannu dai har suka shirya da kuɗi masu yawa, sannan ya amince, ya ce
mata “to wance kar fa in ji wannan magana ko ga wani”, ta ce “ga wa zaka ji?” “Ko
ga wa zaka ji?”
Sai ya duƙa ya ɗauki gawar ya fita da ita, bai
tsaya ko’ina ba sai wajen wani mai ganin[1]
zuma, a lokacin
maigidan ya aikin yaronsa gari don ya samo masu abinci, ya
jingine gawar a gindin bishiyar da suke ganin, shi kuma ya ɓoye, bayan wani ɗan lokaci da yaron ya dawo sai ya
lura da mutum a laɓe a gindin iccen, sai ya gaya wa maigidansa wanda ke sama yana ganin, ya ce
“kai wane ai ka ga wani mutum nan a laɓe yana shan zuman da kake jehowa” shi ko maigidan sai ya ce “baka buge
shege?” “Sami
kulki ka buge shi ni na ce” ai kuwa sai ya sa sandarsa ya bashi tim! Ba sai
mutum ya faɗi ba? Yaron yana
ganin haka sai ya ce “maigida, wai ka ga mutumen da ka ce in buga wai ya faɗi ya mutu!” To ka
san mai ganin zuma da zuciyar tsiya sai ya ce “ƙyale shegen cigaba
da aikinka” suna cikin haka sai wancan mutumen ya fito ya ce “a gaishe ku, wannan mutum fa?” Sai suka ce
masa “wai ya zo ne ya laɓe muna gani yana shanye
zuman, don ɗai yaro ya buge shi
sai ya mutu!” Sai mutumenku ya yi farat ya ce “to! Ni kam na tafi zan je in
gaya wa Maigari”, “ashe ba banza ba zumanku ya fi na kowa zaƙi”
“ni kam na tafi”, sai maigidan ya ce “don Allah ka bari in baka hwanɗari”, ya ce a a shi
hwan ɗari ba ta sa ya yi ɓoyon mutum matacce,
ya ce “ina baka hwan ɗari biyu”, ya ce “a
a”, sannu-sannu dai har suka shirya da kuɗi masu yawa, sannan ya amince, ya ce masu “to
su wane kar fa in ji wannan magana ko ga wani”, suka ce “ga wa zaka ji?” “Ko ga
wa zaka ji?” Nan take ya karɓi kuɗinsa ya adana.
Sai ya ɗauki gawar ya nufi gidan saraki wato sarkin maƙera, don ya san maƙera zuciya garesu, ya
sami wani wuri ya aje gawar nan da ya ɗauko, sa’annan ya ce “assalamu alaikum saraki, fito kai yi man ɗwaɗi” sai saraki ya ce “wane shege ne
ke son ɗwaɗi yanzu cikin tsakar dare?” Sai ya ce “duk mai
son ɗwaɗi ya bari sai da
safe ni ba zan fito ba”, sai mutumen ya ce “idan baka fito
ka yi man ɗwaɗi ba ina mutuwa!”
Wannan maganar ta ƙara ɓata ma saraki rai, sai ya ce “ka daɗe in baka mutu ba”
daga nan sai mutumenka ya ɓoye. Da saraki ya ji shiru sai ya leƙo
don ya ga ko wane irin mutum ne, sai ya taras wai har ya mutu! Sai ya fara
tashe shi yana cewa “kai mai son ɗwaɗi[2], tashi
in gyara maka ka tafi gida”, shi kuma sai ƙara langaɓewa yake yi, da ma
kun san yadda abin yake. Ai sai mutumenku ya ɓullo ya ce “Allah dai ya sa lafiya
saraki a tsakar dare da wani” ko da saraki ya ji shi, sai ya ce “kai ni wani
mutum ne mai shegiyar zuciya ya zo wai in yi masa ɗwaɗi, na ce ban fitowa
cikin dare, sai ya ce in ban fito ba zai mutu, kuma na ce ban fitowa sai kuwa
ya kwanta ya mutun!” Sai mutumenku ya yi ajiyar zuciya ya ce “to!” Ni kam na
tafi zan je in gaya wa Maigari, “ashe ba banza ba ƙirarka
ta fi ta kowa kyawo” “ni kam na tafi in gaya wa Maigari”,
Sai saraki ya ce “don Allah ka
bari ina baka hwan ɗari”, ya ce “ina baka hwan ɗari biyu”, ya ce “a a”, sannu-sannu dai har suka shirya da kuɗi masu yawa, sannan ya amince, ya
ce masu to su wane kar fa in ji wannan magana ko ga wani, suka ce “ga wa zaka
ji?” “Ko
ga wa zaka ji?” Nan take ya karɓi kuɗinsa ya adana.
Ko
da ya ɗauki gawarsa bai
tsaya ko’ina ba sai a masallaci, da zuwansa sai ya iske irinladanan
nan masu sakkon kiran sallah, ladanin masallacin har
ya hau wurin kiran sallah, ya fara kiran sallah sai ya ce “ga wata sadaka ta hatsi ko a yi maka gumba”. Sai kuwa ladan ya sauko ya yanke kiran sallar ya karɓi sadakar ya juya ya kai gida ya
ajiye sannan ya dawo ya yi wani kiran sallar. Ladan
bai koma ba sai da aka ƙare sallah. Yana zuwa sai ya gaya wa matarsa
cewa “wai wani bawan Allah na haɗu da shi ya ba ni sadakar hatsi, ai
kuwa sai ta taso ta kama masa aka kwance. Shi kuma mutumen yana laɓe har ya ji sun fara sallallami sai ya shigo, ya ce
sannunku ladan injin dai lafiya? Sai ladan ya yi masa bayanin cewa “wai wani bawan Allah ne ya ba ni sadakar
hatsi sai yanzu da muka kwance ashe ba hatsin ba ne gawa ce!”
Sai mutuminku ya ce “to ni dai sai an jima, ashe ba banza ba ka fi kowane ladan zaƙin murya,” “na tafi in gaya wa Maigari”. Sai ladan ya ce “don Allah ka tsaya”, sai shi kuma “ya ce in tsaya mi zaka ba ni?” ya ce ina ba ka hwan ɗari biyu”, ya ce a a, sannu-sannu dai har suka shirya da kuɗi masu yawa, sannan ya amince, da ladan ya ce ma matarsa ta kawo kuɗin adashin da suke yi don a haɗa a sallame shi, aka tattaro duk kuɗin gidan nan aka biya. Daga nan ya ce masu “to su wane kar fa in ji wannan magana ko ga wani”, suka ce “ga wa zaka ji?” “Ko ga wa zaka ji?” Nan take ya karɓi kuɗinsa ya adana. Da ya ɗauki gawar bai tsaya ko’ina ba sai bakin gulbin garin saboda haske ya fara an fara buji-buji, ya kuma yi sa’a gulbin ya ɗebo ruwa, sai ya jefa gawar tsundum! Gawar Kwarto ta nutse ruwan ya tafi da ita. Sai mutumen ya koma gidansa ya cigaba da tafiyar da rayuwarsa kamar kowa, cikin walwala kuma babu mai biyarsa bashi.
Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.
Tambayoyi
1.
Wane dalili ne ya sa
mijin matar nan ya yi tunanin fita ya je wurin cin rani?
2.
Mutum nawa ne wannan
mijin matar ya zalunta a cikin wannan tatsuniyar?
3.
Waɗanne irin darusa ne aka koya daga
wannan tatsuniyar?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.