Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Tatsuniyar Wani Ɗan Talaka Da Maciji
Gatanan – gatananku
Wani
talaka ne yana da ɗa wanda yake ji da
shi sosai, baya son abin da ya ɓata masa rai. Tallakan nan baya da wata hanyar samun
abinci sai ya je daji ya yo itace, kullum sai ya je wurin yin itace, idan ya
dawo sai ya sayar kwabo biyu, idan ya sayar sai ya ba yaron kuɗin don ya sayo masu
abinci. Koyaushe yaron ya tafi wajen sawo abincin sai ya sawo na
kwabo sannan ya kashe kwabon.
Wata rana da ya je kasuwar don
sayen abinci sai ya ga wani bagarde yana ta wasa da wani maciji, sai ya tambaye
shi ya ce; “ko kana sayar mani da macijinka?” Sai ya ce “eh” “nawa ka saye?” Sai ya ce “kwabo”, sai Bagarden ya sallama masa, sai yaron ya biya ya ɗauki maciji sai gida.
Daga
nan duk lokacin da ya sayo abinci uku ake kasawa, shi guda Ubansa guda , maciji
guda. Bayan an ɗauki lokaci sai
wata rana macijin nan ya ce “Maigida, ina son ka raka ni, in gano gida” sai kuwa yaron nan ya amince, aka sa ranar tafiyarsu, da
lokaci ya yi, sai suka kama hanya, suna ta tafiya
a cikin daji, ko da suka
kai wani wuri sai macijin ya ce “Maigida runtse idonka”! Ko da ya runtse sai macijin ya yi masa addu’a, daga nan sai ya ce “buɗe idonka”, da buɗewarsa sai kawai ya ga macizai iri-iri gasu nan ko’ina ya duba, wani baƙi, wani fari wani ja,
wani shuɗi kai har da irin wanda bai taɓa gani ba. Sai kuwa macizan nan
suka yo kansa za su sare shi! Amma wannan macijin ya hana har dai suka isa
gidansu.
Kafin su isa gidansu sai ya bashi
shawara cewa; “idan muka kai gidanmu babana zai
nemi ya yi maka kyauta, to komai ya baka ka ce baka so sai zoben da ke saye ga
hannunsa”.
Ko da suka isa sai ya ga ashe uban
macijin nan shi ne sarkin macizai aljanu, aka yi masu tariya mai kyau ana murna, duk dai macijin da ya taso
zai sari yaro, sai nasa macijin ya hana, har dai
ubansa ya tambaye shi dalilin da ya sa yake kare wannan yaron, sai ya ce wa
babansa “na kasance a hannun wani maƙetacin Bagarde, wanda
yake saka ni a cikin wani ɗan gora yana yawo da ni kasuwa-kasuwa, yana aje ni cikin rana a kowace kasuwa
ya je, in sha rana har in galabaita,
wani lokaci har wasu ruwan munafurci yake watsa mani, don zafin ranar ya ƙara bugu na har ma
idona sun fara mutuwa”, ya cigaba da cewa “ana nan haka sai wannan yaron ya saye ni ya kai ni gidansu, a gidansu ne na sami ‘yancin kaina, muka yi daula,
bai taɓa cuta ta ba sai shagali iri-iri
da yake ba
ni, shi ne na ce ya rako ni in gane ku”.
Wannan bayani ya yi wa uban macijin nan daɗi, har ya ce wa yaron “je ka buɗe wani ɗaki gashi can ka ɗebi duk abin da kake so”, koda ya buɗe ɗakin sai ya ga suturu na alfarma iri-iri, sai ya ce wa uban “na gode amma bani so”, sai uban ya sake ce wa yaron “buɗe wani ɗakin a wani gefen”, ko da aka buɗe sai dukiyoyi ir-iri, yaron dai ya sake cewa “na gode amma bani so!” Nan take sai uban ya tambaye shi cewa “to me kake so?” Sai ya ce “ba ni son komai sai zoben nan da ke sanye ga hannunka”, kamar dai yadda maciji nasa ya ba shi shawara. Bai ɓata wani lokaci ba sai ya cire zoben ya ba yaron, yaron ya yi godiya, yana cewa “Allah ya bar zumunci”.
Da suka tashi dawowa sai suka yi
bankwana da uban da sauran dangi da abokan arziki na macijin, sai shi da macijin
suka kamo hanyar gida. Ko da suka kawo wurin nan da ya yi masa addu’a, sai ya sake cewa “rutse idonka”, ya ƙara yi masa addu’a sai ga su sun ɓullo inda ya sani, kuma ya daina ganin macizai. Sun cigaba da tafiya sai ya ce ma maigidansa “ai shi wannan zoben komi kake so a duniya in Allah ya so
yana sa ka same shi”. Da jin haka sai ya ƙara gode wa macijin nan, kuma ya ce; “maciji ka san dai ni na saye ka a kasuwa ko?” Ya ce “eh”, sai ya ce “to ka koma gidan ubanka na yafe maka” “kuma na gode da wannan taimako da ka yi man”.
Maciji ya koma garinsu, shi kuma
yaro ya nufo gida. Kafin ya iso gida sai ya ce “bari in gwada zoben nan in gani”, to ka san Ɗan talaka babu abin da ya fi so ban da gida lafiyayye, ginanne. Ai kuwa sai
ya ce “zobe in gaskiya ne ina son in iske
gidanmu ginanne kuma zagaye da katanga”, yana gama faɗi sai gidansu ya koma kamar ba shi ba, an gine shi tsaf, an kuma zagaye shi
da katanga! Sai yaro ya ƙara cewa “zobe in gaskiya ne ina son gidanmu ya zama ginanne gidan bisa hawa goma sha
biyu, da motoci suna ƙugi a ƙofar gida a ce duk nawa ne”, ai nan take sai ya ga gidan ya koma bene hawa goma sha biyu kuma ga
motoci iri-iri suna ƙugi a ƙofar gida.
Dukiya ta zauna ga yaron nan kuma
duk garin babu mai gida irin nasa, daula ta samu talauci ya gushe. Jama’ar gari
kuwa sai tururuwa suke yi zuwa gidan Ɗan talaka don neman abin da suka ci, wani ya je neman
alfarmar zama direban yaro, wani a ba shi motar haya, wani a buɗa masa shago, da dai sauran buƙatu daban-daban.
Ganin haka ya sa wani bafaden
sarkin garin ya kai wa sarki shawara ya ce “Rankaidaɗe irin dukiya da motoci da kayayyakin jin daɗin da ke a gidan Ɗan talakan nan ko a
gidanka babu su”, “don haka ina ganin ya kamata ‘yarka wance a wanke ta a haɗa aurenta da wannan Ɗan talaka, ka ga
arzikin sai ya mamaye gidanka”. Nan take sai sarki ya amince da wannan shawara ta haɗa auren ‘yarsa da Ɗan talaka, wannan
yarinyar da ma wani Ɗan sarki ne ke nemanta har an kusa
yin auren amma aka sake shawara aka bar wa Ɗan talaka.
Wata rana wancan Ɗan sarkin mai neman
yarinyar
ya zo garinsu yarinyar don hira, ko da ya tunkari
garin su yarinyar nan ‘Yar sarki, sai ya hangi bene hawa goma sha biyu, kuma
bai san da shi ba. Kafin ya isa gidan sarki sai ya tsaya gidan wata tsohuwa ya
tambaye ta “wannan bene hawa goma sha biyu da na gani ban san da shi ba wa ke da shi?”, tsohuwa ta ce masa “yaro ba kai ba ko mu haka muka tashi muka ga wannan al’amari!
Babu wanda ya san lokacin da aka gina wannan gida” Ta cigaba da cewa; “wani yaro ne Ɗan talaka Allah ya yi wa arziki a dare ɗaya” “Ga tarin dukiya, ga kadarori ga motoci na hawa da na haya barkatai” “Har ma yarinya Sarkin garin ya ce zai ba shi wance, har an sa ranar bukin” Wannan yarinyar kau ita ce wannan Ɗan Sarkin ya zo zance wurinta! Da jin haka sai Ɗan Sarkin ya yanke
jiki ya faɗi, hankalin tsohuwa ya tashi don
kar Ɗan Sarki ya mutu gidanta a ce ta kashe shi, don haka sai da ta zuba mai
ruwa tulu ɗari don ya farfaɗo. Da ya farfaɗo sai ya ce mata “Tsohuwa wai me
wannan Ɗan Talaka ya taka?”
Sai ta gaya masa cewa; babu wani
abin da ya taka in ba wani zobe ba da yake amfani da shi don samun duk abin da
yake buƙata. Sai ya ce “wannan yaro ya buwaya domin da aljanu yake amfani”. Daga nan ya yi sallama da tsohuwa bai ko wuce a gidansu
ba don kar ya ga ƙwam![1]
Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya
tsamo ni.
Tambayoyi
1.
Mene ne dalilin da ya
sa maciji bai ciji Ɗan talaka ba?
2.
A ina yaron ya sadu da
maciji kuma ta yaya?
3.
Waɗanne irin darusa ne aka koya daga
wannan tatsuniyar?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.