Ticker

Tatsuniyar Wata Kyakkyawar Yarinya Mai Masoya Da Yawa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Tatsuniyar Hausa

Tatsuniyar Wata Kyakkyawar Yarinya Mai Masoya Da Yawa

Gatanan - gatananku

A wani gari an yi wata yarinya kyakkyawa wadda ta shahara a kan kyawo, tun kafin ta girma duk wanda ya gane ta sai ya yi maganarta saboda kyawo. Saboda haka ne ma sai iyayenta suka yanke shawarar kai wannan yarinya riƙo a wani gari mai nisan gaske, wanda yake da wani daji mai hatsarin gaske a tsakaninsa da garinsu, akwai dabbobin daji kowaɗanne iri da kuma iskoki.  Lokacin da ta girma sai masoya suka taso mata daga ko’ina a cikin yankin, samari da dama sun shiga neman aurenta amma sun kauce, sun kauce ne ba don komai ba, sai don ƙa’idar da ta sa, ƙa’idar ita ce duk wanda zai aure ta sai ya raka ta ganin gida!

Tatsuniyar Wata Kyakkyawar Yarinya Mai Masoya Da Yawa

Ba raka ta ganin gidan ne matsala ba, sai dai irin haɗarin da ke cikin dajin, akwai sheɗanun aljanu da kuma miyagun dabbobi irinsu kuraye da damisa da zakuna, su kuma macizai ba maganarsu ake yi ba. Ita kuma wannan yarinyar ta ce “dole sai an ratsa wannan dajin an raka ni na gano gida”, gashi kuma lokacin babu abin hawa sai dai a tafi a ƙasa. Manema aurenta duk suka kauce don tsoron aljanu da sauran tashin hankalin barazanar dabbobi irinsu zaki da kura da damisa da sauran irinsu.

Sai wasu samari su uku suka ce “mun yarda zamu rake ki komai rimtsi”, yarinya ta yi murnar jin haka, sai aka sa ranar tafiya, an ba su shawara aka ce kowanensu ya shirya, don su yi tanadin laƙunna irinsu; dagumma da layu da addu’o’i. Da lokacin tafiya ya yi sai samarin suka shirya suka yi bankwana da danginsu suka tasam ma gidansu budurwar saboda a can ne za a tashi. Ko da suka isa yarinyar ta kimtsa, babu wani ɓata lokaci sai suka fita. Sun kama hanyar suna ihu, suna kirari, suna bugun ciyayi da ‘yan ƙananan itace, sun wuni sun kwana suna tafiya a cikin dajin, sai ga wasu zakuna guda uku sun taso masu don su sami abin kalaci! Nan take sai wannan yarinya ta ɗora hannu a ka ta fara kuka, sai samarin suka ce “me ya sa kike kuka?” Sai ta ce; “abin da zai halaka mu na gani” sai suka ce ai kuwa babu abin da zai taɓa ki muddin muna nan raye, sai suka fara karafkiya[1] da zakunan uku,

Tatsuniyar Wata Kyakkyawar Yarinya Mai Masoya Da Yawa

Suna ta ɗauki ba daɗi, sai wani irin rugugin zakuna kake ji suna wata ƙara suna gunza! Su kuma samarin sai kibau ke tashi tsutsul! Tsutsul! Tsutsul! Suna cikin haka sai kuma yarinyar ta sake ɓarkewa da kuka! Sai guda ya sake tambayarta cewa “me aka yi har kike kuka?” Sai ta ce “Ni wallahi ƙisa nike ji kamar in mutu!” da ya ji bayaninta sai ya tambayi dangin cewa “ko kuna iyawa da zakunan nan uku ku biyu don in je neman ruwan?” Sai suka “eh”, nan take ya tafi wajen neman ruwa, ya bar su suna ta faɗa da zakunan, sai rugugin zakunan kawai kake ji “Gurrrrrr!, Guuuuur!! Gurrrrrrrr!!!.”

Duk faɗin dajin nan ya yawace shi bai sami ruwa ba, sai can ya hangi wata tsohuwar rijiya, inda yake tunanin ya sami ruwan don ya kai mata, ta sha don rayuwarta ta dawo. Da isarsa wajen rijiyar sai ya ga har ta fara yana-yana, ya leƙa bai hangi ruwa ba, sai ya samu wani dutsi ya jefa, sai ya ji dutsin ya faɗa kandam! Sai kuma ya ji an ce “wane ka samu?” Sai wani ya ce “shi kenan na samu kuma na haɗe!” ashe aljannun ruwa ne suke jiran rabonsu ya faɗo! Sai ya ce “kai!kai!kai!” “dutsi kenan ina ga ni mutum?” Sai kuma ya tuna da irin halin da yarinyar nan take a ciki na tsananin ƙisa, ai kuwa sai ya raba ƙafafuwansa ya shiga rijiya! Yana riƙe da ɗan ƙoƙonsa. Ya yi ta yin ƙasa har ya kai inda ruwan, ya ɗebo ya yo sama, ai kuwa sai aljanun ruwan nan suka ce “da wa aka haɗa mu ba da kai ba?” Shi kuma sai sama yake yi, daga mai katse masa layu, sai mai katse masa warki, har dai ya fito wajen rijiyar da ɗan ruwansa kacal-kacal a cikin ƙoƙo.

Tatsuniyar Wata Kyakkyawar Yarinya Mai Masoya Da Yawa

Su kuma waɗancan samarin biyu da suka rage da zakuna uku suna ta artabu[2] da su, sai ta sake fashewa da kuka, sai gudan ya tambaye ta “mene ne?” sai ta ce “wallahi ɗari (sanyi) nike ji kamar in mutu!” Sai ya ce wa gudan “kana iyawa da zakunan don in je in nemo mata wuta don kar ta mutu?” Ya ce “ina iyawa”, shi kuma ya tafi ya bar shi suna ta karafkiya da zakukin nan guda uku. Ya faɗa cikin daji bai san inda zai nufa ba don ya samo wuta! Duk inda ya nufa sai ya ga babu wuta, sai can ya hangi hayaƙi yana tashi, da ya matsa sai ya ga wuta, to ashe aljanu ne su goma suke gashin mutum tara da suka kamo! Yana ji sai ɗaya daga cikinsu ya ce “ina jin warin mutum”, sai wani aljanin ya ce masa “bayan waɗannan guda tara da muke kawa?” Sai ya ce “shi wannan mai rai ne”, sai wancan ya ce “to Allah ya kawo shege don mu cika goma, kowa ya ɗauki guda mu huta da rabo”. Shi dai yana ɓoye yana jin su, har ya ji kamar ya koma, sai kuma ya tuna halin da yarinya take ciki, sai kuwa ya fara jan ciki har ya matse wutar, sai kuwa ya yi wuf! Ya ɗauki bakin wuta ya juyo da gudu. Da ganin haka, sai aljanun nan suka biyo shi aguje, sai sun yi kamar su kama shi, ya bauɗe masu, a sake notawa da gudu, har ya tsare masu fintinkau, suka koma.  

Tatsuniyar Wata Kyakkyawar Yarinya Mai Masoya Da Yawa

Lokacin da ya isa wajen yayinya ya tarar mai ɗibar ruwa ya kawo ruwa, shi kuma wancan ɗayan ya kashe zaki guda sauran biyun sun ranta cikin na kare. Ita kuma yarinya har ta galabaita saboda matsalolin da suka addabe ta! Su ukun suka tayar da ita suka bata ruwa ta sha, suka haɗa mata gwami ta ji ɗumi duk dai rayuwarta ta dawo daidai. Ta dubi waɗannan samari nata ta ga irin wahalar da kowa ya sha don ceto rayuwarta, sai ta tambayi kanta cewa “shin daga cikinsu wa zan aura?”

Ƙungurus kan kusu, kusu baya ci na, sai dai in ci kan ɗan banza, na yi tun tuɓe da gurun kaza, na faɗa rijiyar zuma na dabshe baki da man shanu, alkaki ya tsamo ni.

Tambayoyi

1.                  Saboda me mutane suke son yarinya kyakkyawa?

2.                  Waɗanne matsaloli ne masoyan yarinyar nan suka shiga a kan hanyarsu ta rakiyarta ganin gida.

3.                  Waɗanne irin darusa ne aka koya daga wannan tatsuniyar?




[1]  Faɗa babu ƙafƙtawa.

[2]  Gwabza faɗa.

Post a Comment

0 Comments