Ticker

6/recent/ticker-posts

Turke A Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Turke A Waƙoƙin Amali  Sububu
2.1.1 Ma’anar Turke

Kalmar turke[1] asalinta kalma ce ta Hausa wadda take nufin wani abu da ake kafawa a ƙasa domin a ɗaure dabba kamar jaki ko doki ko kuma tumaki da awaki. CNHN (2006:446) sun faɗa a ƙamusun Hausa “ Turke shi ne guntun iccen da ake kafawa don a ɗaure dabba a jikinsa. A fagen nazarin waƙa kuwa turke daidai yake da jigo. Ana kiransa jigo idan a rubutattun waƙoƙi ne, a waƙoƙin baka kuwa sai a kira shi turke. Kasancewar wannan littafi a kan waƙoƙin baka ne, zai mayar da hankalinsa, Musamman na Amali Sububu waɗanda mafi yawansu na noma ne, sai kaɗan waɗanda ba na noma ba, za a kira su da sunan “turke” idan tilo ne ko “turaku” a matsayin jam’i, ba jigo ko jigogi ba. Masana waƙoƙin Hausa sun bayar da ma’anoni a kan turke gwargwadon yadda kowa ke kallon kalmar da ƙumshiyar ma’anarta kamar haka:

    Gusau (2003) cewa ya yi:

“Turke shi ne abin da waƙa take magana a kansa wanda ya ratsa tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta. Gusau (2003: 28). 

Shi wannan malami ya bayar da ma’anarsa inda ya ambaci turke wato sunan turke a waƙar baka a matsayin wani abin da waƙa ke zance kansa tun daga farko har zuwa ƙarshe, wato har da ƙananan batutuwa da waƙar ta ƙunsa. Ya kwatanta wanan da silalin zare na tunani, wato wanda ke tafiya ba tare da tsinkewa ba.

Shi kuma Yahya (1994) yana ganin cewa:

Turke a fagen waƙa yana nufin saƙo ko manufa ko bayani ko ruhin da waƙa ta ƙunsa wanda kuma shi ne abin da waƙar ke son isarwa ga mai saurare ko karatu ko nazarinta, Yahya (1994:75).

Masanin ya mabaci kalmomi masu makusanciyar ma’ana kamar saƙo da manufa da ruhi wanda ke ƙunshe cikin waƙa a matsayin turke (wato turke kenan a waƙar baka) da sharaɗin wannan ya kasance shi ne mawaƙi ke son sadarwa ga mai saurare. Wato ke nan ko da mai saurare ya fahimci wani abu saɓaninabin da mawaƙi ke nufi, to ba zai kira wannan turke/turke ba, domin ba shi ake son ya fahimta ba.

Ta la’akari da ma’anonin da masana suka ba kalmar turke a nazarin waƙa ana iya cewa turke shi ne ƙudurin zuciyar mawaƙi da yake son ya bayyanar ga mai sauraro ko kuma karatu da nufin su fahimce shi su amince da shi.

 

2.1.2 Nau’o’in Turaku A Waƙoƙin Amali  Sububu

Masana da manazarta da dama sun bayyana cewa turke ya kasu kashi biyu, kamar dai yadda Bunza (2009) da sarɓi (2007) suka bayyana cewa turke ya kasu kashi biyu, wato ‘Babban turke’ da ‘ƙaramin turke’. Yanzu bari mu zo da su ɗaya bayan ɗaya don ganin yadda abin yake a cikin waƙoƙin Amali  Sububu.



[1]  Kamar a ce jigo a rubutacciyar waƙa, idan a waƙar baka ne sai a ce turke. Dukansu suna nufin manufa.

Post a Comment

0 Comments