Ticker

Waƙar Hausa Ta Duniya Ta Malam Imrana Hamza

AMSHI:

 'Yan Hausa a yanzu mun zaburo,. Ba za mu bari mu zam baya ba.

1. Bismillah Ilahi mai gaskiya,

Kai ne ka halicci duk duniya,

Da abin da yake ciki bai ɗaya.


2. Tsira da aminci baki ɗaya,

Daɗo su ga Annabin gaskiya,

Manzon da ya zo ga duk duniya.


3. Ni ban hikimarka Allahumma,

Baitoci ni a yau zan yi ma,

Harshenmu na Hausa baki ɗaya.


4. 'Yan Hausa a yanzu mun zaburo,

Da kowa yau mukan yo karo,

Mu buge mu wuce su baki ɗaya.


5. Ni na yi riƙo a kan gaskiya,

Duk wanda ya sami Kan Saniya,

Wai mai zai yo da 'yar kurciya.


5. Da mun zauna sahun baya can,

Ana zunɗen mu "kun gan su can,

Su ne 'yan Hausa ba tankiya".


6. Ja baya da kunga Rago ya yi,

Dabarar shirya yaƙin ya yi,

Ba wai tsoro ba ne gaskiya.


7. Amma kuma ga shi yau ya fito,

Kalmarsa Kule yake ambato,

In sun isa sai su ce Cas ɗaya.


8. Sun raina gudun da Zomo ya yi,

Da Barewa in gudun za a yi,

A tsawon ƙafa za ta mai zarciya.


9. Wasu na lilo a kan Ceɗiya,

Wasu ko sun kama Tumfafiya,

Mu kau mun hau icen Tsamiya.


10. Wata ta yi ciki da ɗa ba Uba,

Mu kau da uwarmu kuma ga Uba,

Ai kun san dole mu yi fariya.


11. Zan saurara a nan 'yan uwa,

Jama'armu mu daina yin ɗimuwa,

Mu yi kishin Hausa baki ɗaya.


12. Nai roƙon Rabbi Sarki ɗaya,

Ka ɗaukaki harsunan duniya,

Amma kuma Hausa ta yi zarciya.


13. Na sanyo Maluman Hausa duk,

Allahu ka ƙara kare su duk,

A yini da dare zuwa safiya.


14. In an maka tambaya wa ya yi?

Ce " Imran Hamza shi ne ya yi"

Mai kishin Hausa kan gaskiya.


Kafar Intanet Ɗin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

Post a Comment

0 Comments