Ticker

Wakar Isah Mai Kware

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Waƙar Isah Mai Kware

Isah Maikware a garin Dukkuma yake ta ƙaramar hukumar Sabonbirni yamma ga Adamawa[1] a cikin jihar Sakkwato. Shahararre ne ga noma don haka Amali ya kai masa kiɗansa.

 G/Waƙa : Zahin rana,

: Bai tauye[2] ka ba,

   : Sabon Goje[3],

: Isah Maikware.

 

   Jagora: Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

  ‘Y/ Amshi : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

     Jagora: Kurman doki,

: Isah ɗan Buwa,i x2

   : In ya dinga,

: Sai in an tare,

‘Y/Amshi: Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

     Jagora: Ranad damana,

: Ba ciwo ba ta,

    ‘Y/Amshi: In an daure,

: Komi ba ta yi,

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

     Jagora: Ku yi gona kui noma,

   : Bana gero za a yi,

   : Maiwa za a yi,

   : Wake za a yi,

   : Dawa za a yi,

   : Masara za a yi,

   : Gujiya[4] za a yi,

   : Rogo za a yi,

   : Shinkahwa za a yi,

   : Kuma duk kyawo sukai,

   : Kowa noma.

‘Y/Amshi: Samo wa yakai.

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

     Jagora: Allah Ubangijinmu,

: Hiyayye mai sama,

   : Jabbaru mai dare,

: Mai rana Haliƙu,

   : Na gode mashi,

   : Yai man lahiya,

   : Da hurata ya haɗa,

   : Suturata Mai sama,

   : Kuɗɗina Haliƙu,

   : Matana Mai sama,

   : Mui ta zaman duniya,

   : Kahin lahira ta ce masu,

   : Ta anshe masu,

   : Jatau  duniya!

    ‘Y/Amshi: Ba komi ba ce,

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

     Jagora: Na biyo cikin Ɓula,

: Hak Kuka tara,

   : Girnashe ni biyo,

: Nik kwan niw wuce,

   : Na biyo Tsabre,

: Na kwan na wuce,

   : Tsabren Citumu,

: Na kwan na wuce,

   : Tsabren ɓauna,

: Na kwan na wuce,

   : Tsabren sarki,

: Na kwan na wuce,

   : Na biyo Shalla,

: Na kwan na wuce,

   : Sai na lwaye[5],

‘Y/Amshi: Na kwan Dukkuma.

 

     Jagora: Sai na kwan nan,

: San nan zan wucewa.

‘Y/Amshi: Ko can an ce,

: Komi yi sukai.

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

   Jagora: Akwai ruwa,

: Akwai hatsi,

: Cikin duniya,

   : Akwai tuwo,

: Akwai hura,

: Cikin duniya,

   : Daɗin duniya,

: Kowa samu yakai,

   : In kana da gero,

: Gero za ka ci,

   : In ba ka da gero,

: Gero za ka ci,

   : Amma hwa lahira,

: Da wuyas samu take,

   : Ran kwa..,

: Na duniya ba kwa..,

: Na lahira,

   : Ran kwa..,

: Na lahira ba kwa..,

: Na duniya,

   : Duh halin da kay yi,

: Yana iske maka,

   : In tana da gyara,

: Rannan ji kakai,

   : Ko ba ta da gyara,

: Rannan ji kakai,

   : Sai tana da gyara,

: Aka gyara maka,

   : In ba ta da gyara,

: Gyara ba shi yi,

   : Dab bayan dangana,

   : Wayyo ni raina!

‘Y/Amshi: Baƙon duniya[6].

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

    Jagora: Raggo yana ganin,

: Mai kandu na daka,

   : Raggo kana ganin,

: Tcadadda na daka,

   : Sai ta yi rangaji,

: Ta yi yabƙi[7] nan haka,

   : Yabƙi ɗai takai,

: Yanga ɗai takai,

   : Yat tambaye ni yac ce,

: Yabƙin mi takai?

  : Yabƙi takai mijinta,

: Ta dai gane mashi,       

: Ta dai sami gaba nai,

: Rana ta dushe,

   : Bakin ƙarhe bakwai,

: Kaiwa ƙarhe takwas,

   : Bakin ƙarhe tara.

‘Y/Amshi: Kahin a kai ga sha biyu,

: Ya sha nakiya[8],

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

     Jagora: Ko kahin a kai ga sha biyu,

‘Y/Amshi: Duk an durmuya[9].

 

    Jagora: Ko kahin a kai ga shabiyu,

: Hay ya sa giya.

   : Raggo yay yi tagumi[10],

   : Yaz zura hannu baka,

   : Yac ce gaya ma kowa,

: Bana aiki nikai,

   : In na yi jijjihi,

: Sai rana ta dushe,

   : In nit taho gida,

: In riƙa saƙar kaba,

   : Wannan abin da kowa yaka so,

: In yi shi.

   : In ya yi macce,

: Ba ya da haushin runguma,

: Ta rungume shi.

 ‘Y/Amshi: Ya yi kamay ya tawwaha[11].

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

     Jagora: Dut ta adana shi,

‘Y/Amshi: Ya yi kamad,

: Dai bai da rai,

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

     Jagora: Damana ta dawo,

: Raggo na kuka,

   : Ya zo yai noma,

: Rana ta hana!

   : Ya dawo gida,

: Ba tsabad[12] daka,

   : Ba kuɗɗin awo,

   : Ya koma bara,

   : Mata sun hana,

   : Kowak kirɓa,

: Gona za ta yi,

   : Tsohon shegen,

: Kuka yat tcira,

   : Raggo yac ce,

: Wayyo Allah,

   : Wayyo Annabi,

   : Wayyo yunwa,

: Wai mi yai maki?

‘Y/Amshi: Koko yunwa jimai[13] za ta yi,

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

 

     Jagora: Yarinya tag ga Isah,

: Gona yana ta noma,

: Ya sha gangara,

   : Tay yi duƙe tac ce,

: Isah mi a kai?

   : Ya waiwayo ta,

: Yac ce mata aiki ni kai,

   : Ko kana kwaɗaina,

: Bana amre akai,

   : Ko ba ka kwaɗaina,

: Bana amre akai,

   : Abin da nih hi so,

: In riƙa ƙaton dame,

   : In yo sussuka,

   : In sheƙe da kyau,

   : In auna da kyau,

   : In surhe da kyau,

   : In wanke da kyau,

   : In kirɓe da kyau,

   : Sai na yi tankaɗe.,

   : In aza sanwad dawo,

   : In nig gamo daka,

: In yi zaman tankaɗa,

   : In dunhe da kyau,

   : In kirɓe da kyau,

   : In dame da kyau,

   : Kazo ka sha hura,

   : Mui ta zaman duniya,

   : Yac ce wuce-wuce,

   : Ga wata can ta wuce,

   : Waccan da ta wuce,

: Hakanan tac ce mani,

   : Ke ma da kit taho,

: Hakanan kic ce mani,

   : Dubu kamak ki sun,

: Ce hakanan sun wuce,

: In na biya ku,

: Ɓata biɗata  za ni yi,

: Dut mai biye ma macce,

: Shiga kunya ya kai,

: Sai ta yi zanne,

: Tac ce Isan Dukkuma,

: Sabon yaro,

: Mai kyawon shiri,

: Kai min gahwara[14],

: Kai min gahwara,

: Isah ɗan Buwai.

: Ya waiwayo ta.

‘Y/Amshi: Yac ce,

: Ya yahe[15] mata,

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje,

: Isah Maikware.



[1]  Sunan wani ƙauye ne a cikin ƙaramar hukumar Sabonbirni.

[2]  Hana shi noma ba.

[3]  Babban manomi wanda ya shahara.

[4]  Gyaɗa.

[5]  Sakankancewa

[6]  Mutum.

[7]  Yanga.

[8]  Ya sadu da ita.

[9]  Fara saduwa

[10]  Zama shiru mutum ya sa hannu ya tallabe fuskarsa.

[11]  Mutuwa.

[12]  Hatsi Musamman dawa ko gero

[13]  Yin rauni/ sabautawa.

[14]  Afuwa

[15]  Yin afuwa

Post a Comment

0 Comments