Waƙar Kiran Sallah: Ta Maharazu Mudi Kwasare

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Waƙar Kiran Sallah: Ta Maharazu Mudi Kwasare

1. Ya arhamar rahamani bani abin nufi,

Zancen da zan yi kas shi faɗi ga banza.

2. Kai mai kiran sallah ka san wada zaka yi,

Ka yi hattara don ba a yi nai banza.

3. Ka bi malamai ka yi tambaya su faɗa maka,

Don kak ka yarda da ƙaƙarakon banza.

4. Don shi kiran sallah da ilmi nai shike,

Juhala’u kas su jiya su ɗauka banza.

5. Don kas su iske ana kiran sallah da kyau,

Basu tambaya ba su yamutse shi ga banza.

 6. Don na ga ƙattan ƙauye wasa ɗai su kai,

Sai sun gaza suka fasa kuwwar banza.

 7. Sannan su tashi su ce kiran sallah sukai,

Abu dai kamar mai bambaɗancin banza.

 8. Aikin ibadah jahalu shaiɗan anka wa,

An taimake shi ga nashi aikin banza.

 9. Juhala’u na dubin kiran sallah sukai,

Ulama’u sun ga suna ta ɓannar banza.

10. Su ce sukai wada anka so hakana akai,

Wai ko ibada kaito sun yi banza.

11. Sun zo biɗal ladasu ɗaw zunubi tuli,

Basu ko kula ba suna ta aikin banza.

12. Wani ko shina son yi da kyau ƙaƙa shikai,

Tun can ga baki adda dolgen banza.

13. Waƙafi da izhari da ijlali akai,

Had dai ga mai sauti mutum yar’yaza.

14. Kuma mai sanin waƙati da kyau natsuwa sani,

Don ka a sa wani yamutsatssen banza.

15. A lah da ashhadu da haya alal salah,

Sun wa kiran sallah kalamin banza.

16. Allahu akbar in kiran sallah ka kai,

Don kak ka ce Ala ka faɗi ga banza.

17.Wannan alihin ɗamre kablasan shikai,

Kak ka ce akabar a bar ka ga banza.

18. Akubar da akabar wanga dud dulginku na,

Juhala’u kau da ka buɗe baki banza.

19. Kuma ba a keɓe bar, ga kowace kabbara,

 Bar, uzanan halaka balidin banza.

20. Kuma ba a cewa bar, batun Akbar akai,

Don kakka tashi ka buɗe baki banza.

21. Ashahadu ɓannata kaɗai ce ashadu,

Ka iyas da ijlali kabar jan banza.

22. Shaidun ka in ka shaida Allah ag guda,

To kak ka ja anla’ilah jan banza.

23. Ga akhirataini nan da kacce ash, hadu,

Ce anna ko ce aana ya yi ga banza.

24. Kuma kak ka ambaci dara canga Muhammada,

Kumma kakka ce ɗan dangararren banza.

25. Ka ce Rasulallah rasulullah shike,

Ɓannakka sai kai wanga samnan banza.

26. Kuma kakka ce ha can ga hayya ala sallah,

Jaki ka cewa ha garurat banza.

27. Kuma kakkace sala can ga hayya alal salah,

Kam mai kiran sallah shi ƙuna ga banza.

28. Kuma kakka ce ya fala canga hayya alal falah,

 Don kakka ce a taho ga dajin banza.

29. Kuma kabbarori ba a yin su kimi-rimis,

 Yi guda-guda dai ba a miƙon banza.

30. Kalimat cikon azanu lam ja nai a kai,

 Farko da ƙarshe babu ƙaulin banza.

31. Kowaj jiya in ya ƙiya shi yas sani,

 In ya riƙa ya bar jidalin banza.

32. Ayi ba ta sa a yi ko da tankan manfa’a,

 Bari ba ta sa a bari ga aikin banza.

33. Ko ni da niyyi ta bani cewa na iya,

 Amma fa na ɗara masu rurar banza.

34. Waƙag ga na yita malamai kowar riƙa,

 Inya ga ɓanna kas shi bar ta ga banza.

35. Kowa ka talifi shi tsira ga kuskure,

 To ƙallama ni bam jidalin banza.

36. Sannan bi hamdillahi summa salatuhu,

 Wassalamuhu sannan ina da azazza.

37. Ince su dawwama ga annabinmu Muhammadu,

Walawwalu Wal, As’hab kun ji magarza.

Post a Comment

0 Comments