Ticker

Wakar Na Dadada

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Waƙar Na Dadada

Sunan Nadada Ali a garin gidan bisa yake, wato garin da mahaifin Amali ya koma da zama. Shi ma Amali ya yi masa waƙar ne saboda shahararsa ga aikin noma.

 

    G/Waƙa : Ya biya,

: Mai kiɗin manoma,

  : Mu kai duman,

: Mu gidan Nadada.

 

  Jagora: In kai duma,

: In gano na Nadada.

   ‘Y/Amshi: Mu samu gero,

: Abin dakawa,

 

   Jagora: Goɗiya yay,

: Yi man ta kaina,

  : Ya ba ni do..,

: Ki na hwan tamanin,

: Ya ba ni sirdin,

: Da zan azawa,

   ‘Y/Amshi: Amali sai,

: Godiya ga Ƙwazozo[1],

  : Ta yi sir..,

: Din zanen atanhwa,

  : Taho-taho,

: Ba ta sa ni in zo,

  : Wuce-wuce,

: Ba ta ɓata raina,

  : Da hankalina,

: Ina da wayau,

  : Amali na san,

: Idon masoya,

  : Ina ganin,

: masu son kiɗina,

  : Ina ganin,

: Wanda ba ya so na,

  : Wahabu Allah,

: Ka ceci ɗan Jijji,

  : Inda shegen,

: Da ba ya sona.

  : Gadauniya[2],

: Mai sabatta burgu,

  : Ina gani nai,

: Da rege-rege,

  : Ina gani nai,

: Da kutce-kutce,

  : Ya ɗora yawo,

: Cikin gidaje,

  : Ya ɗora yawo,

: Cikin riheni[3],

: Ya ɗora yawo,

: Cikin mutane,

  : Ku daƙile,

: Ƙaddara ta shahe shi,

  : Tunda yac,

: Ce yana iyawa.

 

   ‘Y/Amshi: Nadada mai,

: Lahiyag gizago,

  : Cikin gida,

: Ba ka jin hwaɗa nai,

  : Cikin gari,

: Ba ka jin hwaɗa nai,

  : Amma a ko,

: Ma cikin mazaje,

  : A ɗauki kal..,

: Me a ɗaura walki,

: A ɗaura walki,

: A kama gabce,

  : Ka iske ƙa..,

: To yana hawaye.

 

    ‘Y/Amshi: Dabaibaya,

: Mai tsayad da jaki,

  : Ta kinkime,

: Ta hana shi motci,

  : Kai had da do,

: Ki tana riƙewa,

  : Ga rijiya,

: Nan gaba tamanin,

  : Mutum ya hwa,

: Ɗa ta anshi rainai,

  : Maza ku sake,

: Shiri na ‘ya Ali,

  : Sai mutum wan,

: Da yaj ji kainai.

 

    ‘Y/Amshi: Nadada a..,

: A ka kai da Jatau?

  : Amali ya kwa..,

: Na ba ta gari[4],

  : Ya koma ya,

: Tashi bai kara[5] ba,

  : Inda kamab,

: Ba ka taka kimshe,

  : Da sai mu ce,

: Ma halin rashi ne,

  : Amma da yaz,

: Zan kana da kimshe[6],

  : In baka ‘yam..,

: Man ka ba ni ɗauke,

: Mu samu gero abin dakawa.

  : Ya biya,

: Mai kiɗin manoma,

  : Mu kai duman,

: Mu gidan Nadada.

 

  Jagora: Nadada ya,

: Ba ni bai hana ba,

  : Ya koma ya,

: Ba ni ya daɗa man,

  : Nadada a,

: A kakai da taro,

  : Gida yana,

: So dawa tana so,

  : Waɗanga na,

: So waɗanga na so,

  : Waɗanga na,

: Son ka ba su ɗauke[7],

  : Waɗanga na,

: So ka ba su rance,

   ‘Y/Amshi: Waɗanga na,

: So ka ba su kyauta.

  : Ya biya,

: Mai kiɗin manoma,

  : Mu kai duman,

: Mu gidan Nadada.

 

   Jagora: Da arziki,

: Na irin na yanzu,

  : Da arziki,

: Na ina da raina,

  : Ina da ƙan..,

: Ne ina da yanne[8],

  : Ina da ‘ya..,

: ’Ya irin na kaina,

  : Akwai riko,

: Da ina da keke,

  : Ina da sha,

: Nu ina da jakkai,

  : Ina da do,

: Ki ina da mashin,

  : Ina da ge,

: Ro abin dakawa,

  : Akwai tuhwa,

: Hin da  za ni sa wa,

  : Ina da kuɗ,

: Ɗi abin kashewa.

   ‘Y/Amshi: Amali sai,

: Godiya ga Jabbaru,

  : Shi da yac,

: Ce hakanga Jatau.

  : Ya biya,

: Mai kiɗin manoma,

  : Mu kai duman,

: Mu gidan Nadada.

   

  Jagora: Allah ubana Ubangijina,

  : Ubangiji,

: Wanda adda sheɗa,[9]

  : Yana gani,

: Ba da ijjiya ba,

  : Shi ne ka ji,

: Ba da kunnuwa ba,

  : Sarkin da ba,

: A kiɗa ma ganga,

  : Sarkin da ba,

: A kiɗa ma kotso,

  : Sarkin da ba,

: A kiɗa ma goge,

  : Sarkin da ba,

: A ganin naɗinai,

  : Sarkin da ba,

: A ganin hito nai,

  : Sarkin da ba,

: A gani da riga,

  : Sarkin da ba,

: A gani da wando,

  : Balle agogo,

: Da sa tabarau,

  : Ikon ka shi,

: Ne abin ruhwanka,

  : In Ya yi hannu,

: Yana ƙahwahu,

  : In Yai hwarut,

: Ta Yana akaihu,

  : In Ya yi hanci,

: Yana idanu,

  : In Ya yi hal,

: She Yana haƙori,

  : In banda Shi wa,

: Ka yin hakanga?

  ‘Y/Amshi: Mu san da Allah,

: Mu gyara gobenmu,

  : Kam mu saɓa,

: Ma lahirarmu,

  : Ya biya,

: Mai kiɗin manoma,

  : Mu kai duman,

: Mu gidan Nadada.

Jagora: Mahaukaci,

: Bai ci duniya ba,

  : Mahaukaci,

: Bai ci duniya ba,

  : Ku gane ko,

: Ya ci bai sani ba,

  : Abin da ak,

: Kyau ga ɗan musulmi,

  : In ka ji da..,

: Ɗi tuna da gobe,

  : In ka ji ɗwa..,

: Ci tuna da gobe,

  : Tuna da sar,

: Kin da yay yi ranka,

  : Ka san da shi,

: Yah halicci ranka,

  : Ka gane shi,

: Ne marar iyaka,

  : Ka hangi ramen[10],

: Da za a sa ka,

  : Kowa ka di,

: Bin hakanga Jatau,

  : Ai bashi gurin,

: Ya tanka ɓanna,

  : Koway yi ɓan..,

: Na tana ga kainai,

  : In ya yi gya,

: Ra shina ga kainai.

: Ya Rasulu,

: Ya kyauta,

   ‘Y/Amshi: Ƙarshenmu,

  : Inji Ɗan,

: Iro mai tahwashe,[11]

  : Ya biya,

: Mai kiɗin manoma,

  : Mu kai duman,

: Mu gidan Nadada.

 

  Jagora: In kai duma,

: In gano Nadada.

  ‘Y/Amshi: Mu samu ge..,

: Ro abin dakawa.

 

  Jagora: Rijiya,

: Ce gaba tamanin,

  : Mutum ya hwa,

: Ɗa ta anshi rainai,

  : Maza ku sake shiri.

  ‘Y/Amshi: Na ‘yar Ali,

  : Sai mutum wan,

: Da yaj ji kainai,

  : Ya biya,

: Mai kiɗin manoma,

  : Mu kai duman,

: Mu gidan Nadada.



[1]  Sunan mace ne.

[2]  Tafiya a ruɗe kamar ba a san inda za a je ba.

[3]  Rumbuna.

[4]  Dawa ta dakawa – wato wadda ake mayarwa gari don yin tuwo,

[5]  Cin abincin safe wato kari.

[6]  Tsara dawa ko gero ko dai wani amfanin gona a cikin rumbu.

[7]  Gudummuwa.

[8]  Yayye.

[9]  Numfashi

[10]  Kabari

[11]  Gangunan kiɗa

Post a Comment

0 Comments