Wakar Noma Ta Alhaji Sani Aliyu Dandawo

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo

    Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo

    Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo

    An Æ™iyasta cewa an haifi alhaji Sani Aliyu ÆŠandawo a wajajen shekarar dubu É—aya da É—ari tara da arba’in da uku (1943) a garin Argungu ta jihar kebbi, amma dai mahaifinsa É—an asalin jihar Sakkwato ne a garin Shuni. Alhaji Sani ya yi karatun boko amma bai yi nisa a cikinsa ba don iyakacinsa firamare, amma ya yi karatun muhammadiyya inda ya karanci alkur’ani da littatafai da dama. A shekarar 1959 ne suka tashi daga Argungu suka koma garin Yawuri da zama.

    A shekarar 1964 ne ya fara waÆ™a kuma ya fi bada Æ™arfi wajen waÆ™oÆ™in fada, amma daga baya ya riÆ™a yin waÆ™oÆ™i irin na siyasa da na sauran jama’a masu hannu da shuni[1] da kuma wasu fitattun mutane. Saboda kasancewarsa makaÉ—in fada, Alhaji Sani Aliyu ÆŠandawo ya yi wa sarakuna da dama waÆ™a, kuma bai da wata waÆ™a da ke zaman ba kandamiyarsa.

    Alhaji Sani Aliyu ÆŠandawo yana da matan aure biyu da ‘ya’ya fiye da ashirin maza da mata. Allah ya karÉ“i rayuwarsa watan Afirilu na shekarar dubu biyu da goma sha shida (2016).



    [1]  Masu arzikin dukiya.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.