Wakar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

    Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

    Taƙaitaccen Tarihin Sani Sabulu

    Haihuwarsa Da Ƙuruciyarsa

    An haifi Sani Sabulu a garin Kanoma da ke cikin Æ™aramar hukumar mulki ta Maru ta jahar Zamfara a shekara ta 1952, a wata unguwa da ake kira ‘yar kuka. Sunan mahaifinsa malan Abubakar Kanoma. Mahaifin nasa ya rasu tun yana yaro Æ™arami (Kafin ya yi auren fari). A lokacin da yake Æ™arami Sani Sabulu ya koyi sana’ar noma da kiyon dabbobi kuma ya zamo mutum mai Æ™wazo da juriya. Duk daÉ—ewar da aka yi a gona ba ya nuna gazawarsa. Haka kuma Allah ya bashi fasaha ta yadda duk abin da ya gani zai iya yin irinsa, ko ya kwaikwaye shi. Har wa yau yakan yi farautar namun daji, musanman ma Æ™anana irin su kurciya da É“eraye[1].

    Neman ilminsa

    Sani Sabulu ya fara karatun AlÆ™ur’ani mai tsarki a hannun mahaifinsa malan Abubakar. Bayan rasuwar mahaifin nasa ne, sai ya koma wajen wani malami da ke nan unguwarsu mai suna malan Hamisu. Daga nan kuma ya koma wata unguwa da ake kira Jauri inda ya cigaba da karatunsa a wajen wani malami mai suna Malam Abdu a nan cikin Kanoma. Bayan ya bar Kanoma ya koma Zariya, ya ci gaba da karatunsa na Addinin Musulunci. A taÆ™aice dai Sani Sabulu ya sauke AlÆ™ur’ani hizifi sittin, har kuma ya karanci wasu daga cin littattafan fiÆ™ihu kamar su Ƙawa’idi da Ahalari da Ishmawi da Risala.

    Wannan ilimi da ya samu, shi yake taimaka masa wajen gudanar da waÆ™oÆ™insa na baka. Don a kodayaushe in zai fara waÆ™a yakan soma ne da Basmallah tare da ambaton Ubangiji. Ta fuskar ilmin zamani kuwa, Sani Sabulu bai halarci makarantar boko ba, amma ya halarci ajin yaÆ™i da jahilci a garin Kanoma. Sai dai duk da haka bayanai sun tabbatar da lokacin da Sani yake yawon sa na duniya ya tsinci wasu ‘yan kalmomi na ingilishi. Wannan ma shi ne dalilin da ya sa idan yana waÆ™a lokaci-lokaci za a ji yana jejjefa ‘yan kalmomin ingilishi a cikin waÆ™arsa. Kamar inda yake sa kalmar silolin-silolin a wata waÆ™arsa. Ya aro ne a cikin harshen Ingilishi, wadda ake rubuta ta kamar haka: slowly-slowly, wadda ma’anar ta ke nufin “a hankali a hankali” ko “sannu-sannu”. 

    Aure  da iyalinsa

    Sani Sabulu ya auri mata guda huÉ—u ne a rayuwarsa, matan su ne:

    i.                    Amina

    ii.                 Hajara(Haja)

    iii.               Sa’a

    iv.               Masa’uda

    Ya kuma haifi ‘ya’ya guda shida (6) maza biyu mata huÉ—u da suka haÉ—a da:

    i.                    Hashimu

    ii.                 Jamila

    iii.               Nafisatu

    iv.               Hindatu

    v.                  Balkisu

    vi.               Abubakar (Baban gida),

    Sai dai ya mutu ya bar matan aure guda biyu wato:

    i.                    Hajara

    ii.                 Masa’uda.

    WaÉ—annan su ne yawan iyalin Sani Sabulu.

    Sana’oinsa

    Sani Sabulu bai gudanar da wasu sana’oi da dama ba, baya ga sana’ar gama-gari wato noma, sana’ar da ya fi ba fifiko ita ce makaneza (facin tayoyi), wadda ya koyo daga zariya, kuma ya kawo ta garinsa na haihuwa wato Kanoma. Wannan ya nuna cewa Sani Sabulu bai gaji sana’ar da ya iske mahaifinsa kanta ba, wato dukanci da malanta. WaÉ—annan su ne sana’oin da Sani Sabulu ya yi a lokacin rayuwar sa.

    Baya ga sana’oin gargajiya, Sani ya taÉ“a yin aikin gwamnati a lokacin da yake zaune a Æ™aramar hukumar Koko/Besse da ke jihar kebbi a Æ™arÆ™ashin raya al’adun gargajiya na Æ™aramar hukumar[2].

    Fara waƙarsa

    A fagen kiÉ—a da waÆ™a, Alhaji Sani Sabulu É—an haye ne, wato bai gaji kiÉ—a da waÆ™a daga iyaye da kakanni ba. Don haka a iya cewa, ya tsiri wannan sana’a ne da rana tsaka. Wannan  zance ya tabbata a cikin É—aiÉ—aikun waÆ™oÆ™insa.

    Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

    Sani Sabulu mutun ne da Allah ya sa Æ™auna da sha’awar waÆ™oÆ™in baka na Hausa a Æ™waÆ™walwarsa, tun lokacin yana yaro Æ™anÆ™ane. WaÆ™oÆ™in makaÉ—a irin su Hussaini jikan boka da na Dr. Alhaji Mamman Shata na daga cikin waÆ™oÆ™in da suka fi kwanata masa a rai. Saboda kusan duk lokacin da yake gudanar da wani aiki a gona ko a wurin makaneza , za a ji shi yana ta Æ™oÆ™arin rera su. Ta haka ne Sani Sabulu ya Sami gambara ya fara kwaikwayon irin waÉ—annan waÆ™oÆ™i[3].

    Bayan Sani Sabulu ya baro zariya ya dawo Kanoma, Allah (S.W.A.) ya jarrabe shi da kamuwa da ciwon kurkunu, Inda ya share watanni  a zaune. To, bayan Allah ya kuÉ“utar da shi daga cutar ne, sai ya ga ya dace ya shirya wa wannan ciwo waÆ™a domin ya bayyana irin wahalar da ya sha tare da fito da illolin cutar a fili. Daga nan sai ya É—auki gambararsa tare da abokinsa mai yi masa mabanci da rikoda da kaset suka fita cikin daji ya shirya waÆ™arsa tare da  É—aukar ta kaset

    A lokacin da jama’a  suka ji wannan waÆ™a, sai hankalinsu ya raja’a gare ta. Kuma a dalilin haka ne duk gidan da wata hidima ko sabga ta samu ta aure ko haihuwa, sai su kira Sani Sabulu domin ya shirya masu waÆ™a[4]

    Waƙar Noma Ta Alhaji Sani Sabulu

    Ana cikin haka ne sai Sani Sabulu ya bar garin Kanoma zuwa garin Koko Æ™aramar hukumar Koko/Besse da ke cikin jihar Kebbi. A nan ya sami shiga cikin kungiyar al’adun gargajiya ta Æ™aramar hukumar .bayan da suka fahimci fasaha da hikimar da Allah ya yi masa, Sai suka É—auke shi a matsayin ma’aikaci a gefen wasannin al’adun gargajiya. Duk lokacin da aka sami wani buki, sai su tafi a Æ™arÆ™ashin Æ™ungiyar, suyi raye-raye na gargajiya. Bayan an Æ™are raye-raye sai Sani Sabulu ya fito fili domin ya waÆ™e bikin. Haka kuma a daidai wannan lokaci ne ya waÆ™e Æ™aramar hukumar Koko/Besse[5].

    Sani Sabulu a Matsayin makaÉ—i

    Alhaji Sani Sabulu, ya zama cikakakken makaÉ—I, wanda ya É—auki kiÉ—a da waÆ™a a matsayin sana’a bayan ya bar aikin gwamnati aÆ™aramar hukumar Koko/Besse. Dagan an sai ya haÉ—a Æ™ungiyarsa wadda ta Æ™unshi makaÉ—a da ‘yan ma’abba. Wato dai yana gudanar da san’ar sa ta kiÉ—a da waÆ™a ne a Æ™ungiyance. A daidai wannan lokaci ne ya daina amfani da gambara.

    Duk da cewa yana gudanar da kiÉ—an sa a Æ™ungiyance, Sani Sabulu shi kaÉ—ai yake aiwatar da waÆ™arsa ba tare da amshi ba. Sai dai akwai wasu É—aiÉ—aikun waÆ™okin sa ake yi wa amshi kamar waÆ™ar Alhaji Isah Mayana. Wato dai yana  daga cikin rukunin makaÉ—an jama’a da ke amfani da tsarin nan na kiÉ—a da waÆ™a ba tare da amshi ba.

    Hausawa na cewa: “Hannu É—aya ba ya É—aukar jinka”. Sani Sabulu yana da Æ™ungiya wadda ta Æ™unshi  mataimaka ko yara da ke gudanar da ayyuka daban-daban awajen sana’ar sa ta kiÉ—a da waÆ™a.

    Akwai wasu masu kiÉ—an kalangu, akwai masu kaÉ—a É—an kurkutu kuma akwai sanÆ™ira wato É—an ma’abba da masu shirya filin wasa, kai harma da direba. A taÆ™aice dai ga yadda tsarin Æ™ungiyar tasa take:

    i.                    Alhaji Sani SabuluJagora

    ii.                 Haruna KokoKaÉ—a kalangu

    iii.               Musa ÆŠangarewa“ “

    iv.               Mamman ÆŠan Æ™addara““

    v.                  Shehu ÆŠan Ruwan Gora““

    vi.               Garba kalangeta““

    vii.             Haruna BirgediyaKiÉ—a kurkutu

    viii.          Ado Rano KanoSanÆ™ira

    ix.                ÆŠan Abu ya yi““

    x.                  Shu’aibu Cali““

    xi.                Malan Sani““

    xii.             Sama’ilaShirya filin wasa

    xiii.           Auta Direban mota

    Rasuwarsa

    A ƙarshe dai Allah ya yi wa Alhaji Sani Sabulu rasuwa a ranar tara ga watan bakwai shekarar dubu biyu da tara 9/7/2009, a sanadiyyar wani hatsarin mota daya haɗu dashi a kan hanyarsa ta dawowa gida daga wajen yawonsa na waƙa.



    [1]  Sankalawa (1994:9-10).

    [2]  Inuwa da wasu (1993:35-36).

    [3]  Inuwa da wasu 1993:35-36, Sankalawa 1994:19-20.

    [4]  Inuwa da wasu 1993:35-36, Sankalawa 1994:19-20

    [5]   Inuwa da wasu: 1993:36.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.