Wakar Noma Ta Danbalade Morai

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Waƙar Noma Ta Ɗanbalade Morai 

     

    Taƙaitaccen Tarihin Ɗanbalade Morai

    An haifi Ɗanbalade Morai a garin Morai, sunansa na yanka Garba Morai. Garin Morai yana cikin ƙaramar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara. Sunan mahaifinsa Ibrahim, shi ma ɗan asalin Morai ne, nan aka haife shi kuma nan ne ya koyi sana’ar kiɗa da waƙa a cikin garin Morai da ƙauyuka. An haifi Ɗanbalade Morai a shekarar alif da ɗari tara da talatin da shida (1936), ya tashi a cikin gidan makaɗa saboda babansa makaɗI ne, ya gaji kiɗan daga babansa wato Ibrahim, babansa makaɗin sarauta ne da kuma noma, yana kuma amfani da kayan kiɗa kamar taushi da kalangu. Ya yi ta biyar mahaifin nasa ne wajen waƙa har sai da ya tuba ya daina waƙa.

    Bayan mahaifinsa ya tuba ya bar waƙa kasancewar shi mai sha’awar kiɗa da waƙa ya rasa yadda zai yi sai ya koma yana biyar wani makaɗin ‘yanmata wanda ake kira Abdullahi Morai, kodayake ba ita ya koya ba a wurin ubansa,  bayan ya yi biyar Abdullahi ya kuma yi biyar ƙanen ubansa wanda ake kira Amadu Ɗanbaƙi, shi ma Amadu Ɗanbaƙi kamar yadda bayani ya gabata tare da Ɗanbalade suka yi biyar ubansa wato Ibrahim. Ɗanbalade Morai mutum ne mai basira kuma mai hazaƙa, haka suka cigaba yana biyar ƙanen ubansa wato Amadu Ɗanbaƙi suna kiɗa da waƙa tare, shi ne tauraron wajen waƙoƙin, a kan haka Ɗanbalade Morai yana nan yana biyar ƙanen baban nasu sai Allah ya yi masa rasuwa don haka sai ya zama magidan kansa.

    Waƙar Noma Ta Ɗanbalade Morai

    Ɗanbalade Morai bai gadi wani kiɗa ba ga bababnsa in banda kiɗan noma da na sarauta, sai daga baya ne ya haɗa da kiɗin dambe. Allah ya yi masa rasuwa 14,2,2003. Ya rasu ne a sanadiyar rashin lafiyar da ya yi fama da ita ta ciwon awazzu (Haƙarƙari). Ya rasu ya bar matan aure biyu da ‘ya’ya uku da jikoki da dama. Daga cikin ‘ya’yansa akwai Murtala da Mu’awiyya Ɗandumbuje da kuma Hassana. Allah ya jiƙansa da rahamarsa, amin.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.