Ticker

    Loading......

Wakar Noma Ta Sale Sarkin Makadan Bungudu

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Waƙar Noma Ta Sale Sarkin Makaɗan Bunguɗu 

Waƙar Noma Ta Sale Sarkin Makaɗan Bunguɗu

Taƙaitaccen Tarihin Sale Sarkin Makaɗan Bunguɗu

An haifi Sale sarkin makaɗan Bunguɗu kimanin shekaru sittin da uku (63) da suka wuce, wato wajen shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da hamsin da tara (1959) kenan a wannan shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu (1922). Sunan mahaifinsa Muhammadu amma ana kiransa Maidabo, shi ma makaɗi ne wanda ya shahara a kan kiɗin noma da farauta, amma daga baya wani mutuminsa makaɗi daga garin Ruwan ɗoruwa mai suna Abashi ya ja hankalinsa zuwa ga kiɗin fawa, sun cigaba da wannan kiɗin ne na fawa har ƙarshen rayuwarsu. Ita kuma mahaifiyarsa sunanta Inno.

Sale ya tashi a cikin kiɗi tun yana ƙarami, kuma ƙwararre ne wajen kiɗin nomad a fawa ya iya kiɗin kalangu da gangar noma da duman girke da kotso har da taushi kuma kowane ya riƙa kamar don shi aka yi shi. A halin yanzu yana da matan aure guda biyu, Amina da Inno ‘Yar Isah, da ‘ya’ya goma sha shida a raye maza shida duka sauran mata ne. daga cikin mazan akwai Kabiru Ɗanmande da Ibrahim da mu’azzimu da Abdullahi da Musa da Abubakar. Su kuma mata akwai Rabi da Hauwa’u da Maryam da Zainabu da Hindatu da Saratu da Mariya da Rakiya da Saudatu

Bayan sana’ar kiɗi yana da wasu sana’o’i kamar noma da ginin tukwane, kuma har yanzu bai daina ba.

Daga cikin yaransa waɗanda yake yawon kiɗi da su akwai Lawali Hona da Ali da Kabiru Ɗanmande da Mu’azzimu da kuma Musa Furfuri. Ya ziyarci wurare a gida da waje wajen kiɗinsa na sarauta da na noma ko kuma na fawa misali ya kai kiɗi a Suleja da sauran wasu wurare.

Post a Comment

0 Comments