Wakar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Danguzuri

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

    Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

    Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Shehu Ajilo Ɗanguzuri

    An haifi Alhaji Shehu Ajilo a garin ÆŠanguzuri ta Æ™aramar hukumar MaÆ™arfi a jihar Kaduna, babu takamammar shekarar da kwanan watan da aka haifi Shehu ajilo, saboda a cewarsa ba a rubuta ba, kuma duk waÉ—anda ya kamata ya tambaya sun riga mu gidan gaskiya. A wata hira da na yi da shi a ranar Laraba goma ga watan goma sha É—aya shekarar dubu biyu da ashirin da É—aya (10/11/2021) ya Æ™iyasta mani shekarunsa cewa saba’in zuwa tamanin ne a halin yanzu. Ajilo ya yi sana’o’i da dama daga ciki har da koyarwa da tuÆ™in mota da yankan farce da É—aukar hoto wadda ita ce sanadiyar sunan Ajilo da sauransu.

    Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

    Alhaji Shehu Ajilo É—anbaiwa ne, domin duk waÉ—annan sana’o’in da ya yi babu wadda aka koya masa sai dai kawai ya yi, ko ma waÆ™a da ya fara bai yi zama yaron kowa ba sai kawai ya fara abarsa.

    Asalin iyayensa daga Kano suke a wani ƙauye da ake kira Rikadawa ta ƙaramar hukumar Madubi, kakansu ya zo ne tare da mahaifinsa domin yawon nema irin na Kanawa, sai ya auri Bazazzagiya a nan, kuma aka haife shi a nan tare da sauran danginsa.

    An ba shi auren ‘yar Shata wadda ake kira Hajjaju a sakamakon wani kiÉ—a da ya yi  a lokacin bukin yayarta Sadiya wadda ta yi aure a Kano. Mata ne suka gayyace shi ya yi wasa a can a lokacin Shata ba ya gida ya je Maiduguri yana yi wa Abdulmuminu Aminu waÆ™a. To da ya fara waÆ™ar nan daga cikin matan Shatan sai wata ta ce ta bashi fuloti[1], wata ta ce ta ba shi bulo, wata ta ce ta ba shi siminti, É—aya kuma ta ce ai sai a ba shi mace. Sai kuwa Hajjaju ta ce tana sonsa, sai kuwa aka buga masa waya cewa ai an ba Shehu Ajilo Hajjaju, sai kawai ya ce wannan masoyina? To tana sonsa?  Aka ce eh, shi yana son ta aka ce eh, shi kenan sai aka yi auren. Allah ya yi mata rasuwa da kimanin shekara goma sha biyu da auren, ta riga mahaifin nata rasuwa da sati biyu, domin ta rasu bayan sati aka zo addu’ar bakwai, sai sati mai zuwa Shata ya rasu. Allah ya gafarta masu bakiÉ—aya.

    Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

    Alhaji Shehu ajilo ya fara yin suna ne a kiɗan gangar noma, wadda ya ƙware sosai a kansa har ake kiransa aljanin kiɗa ƙanen Ɗanbinta.

    Waƙar Noma Tushen Arziki Ta Alh Shehu Ajilo Ɗanguzuri

    Musamman a lokacin siyasar NEPU da PRP a lokacin su Sardauna ya yi kiÉ—a ‘yammata na rawa suna amshi. A halin yanzu dai yana da mata biyu bayan waÉ—anda suka rasu da waÉ—anda suka rabu da shi.



    [1]  Wato filin da ake gina gida a kansa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.