Ticker

Wakokin Noma Da Wasu Mawakan Suka Yi Wa Manoma

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma 

Waƙoƙin Noma Da Wasu Mawaƙan Suka Yi Wa Manoma

A wannan babi za a kawo wasu waƙoƙin noma ne waɗanda wasu mawaƙan da ba ainahin mawaƙan noma ba ne suka yi su. Abin nufi a nan shi ne su waɗannan nau’in mawaƙa suna yin wasu waƙoƙin da ba na noma ba, ko ma a ce sun fi yin wasu waƙoƙin daban ba na noma ba, Misali kamar mawaƙan jama’a waɗanda kowa suna yi wa waƙoƙinsu da sauran irinsu, kamar yadda masanan adabin Hausa suka karkasa su. Dubi yadda makaɗa irinsu Alhaji Mamman Shata da Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Ɗan’anace da sauransu, suka yi suna a wasu nau’o’in waƙoƙin ba na noma ba, amma duk da haka sun yi wasu waƙoƙin na noma kamar yadda za a iya gani a wannan babin.

Post a Comment

0 Comments