Ticker

Wakokin Noma Na Abu Dan Kurma Maru

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

 Waƙoƙin Noma Na Abu Dan Kurma Maru

Waƙoƙin Noma Na Abu Dan Kurma Maru

Taƙaitaccen Tarihin Abu Ɗankurma Maru

An haifi Abu Ɗankurma a garin Talatar Mafara a ranar Alhamis 22 ga watan Yuli 1931sunan mahaifinsa makaɗa Alu ɗan makaɗa Ibrahim Gurso. Ya sami laƙabinsa ne a sakamakon wata ziyara da wani abokin kakansa ya kawo a gidansu a Talatar mafara mai suna makaɗa Zumul kakan makaɗa Sa’idu Faru. A lokacin da ya zo sai ya ga abokin nasa makaɗa Ibrahim tare da wani yaro, sai ya tambaye shi cewa; shin wannan ɗanmu ne? koko abokinmu? Sai makaɗa Ibrahim Gurso ya ce ai wannan abokinmu ne (yana nufin jikansu ne, kamar yadda kakanni sukan kiran jikokinsu) sai shi makaɗa Zumul ya ce zai sa masa suna daga cikin sunayen da ake kiransa da su, don a cigaba da kiransa da shi, daga nan ne ya kira shi da sunan Ɗankurma.[1] To daga nan ne aka fara kiransa da sunan. Sunansa na asali dai shi ne Abubakar, ya tashi a garin Talatar Mafara. Tun yana ɗan shekara goma sha biyu yake bin kakansa wato Ibrahim Gurso wajen yawon kiɗi da waƙa. Makaɗa Ibrahim Gurso ya yi wa sarkin Mafara waƙa da Sarkin Musulmi Abubakar na uku.

Alhaji Abu Ɗankurma Maru ya fara karatun allonsa ne a garin Talata mafara wajen limamin garin, sai dai bai sauke Alƙur’ani ba a wurinsa sai suka taso daga garin suka komo garin Maru da zama, a nan ne ya cigaba da karatunsa a hannun wani shahararren malamin da mahaifinsa ya kai shi mai suna malam Musa na bakin gebe. A wannan makarantar ne Ɗankurma ya sauke Alƙur’ani mai girma, har ma ya karanci waɗansu littatafan addinin Muslunci kamar su ƙawa’idi da ahallari da sauran irinsu. Saboda ilmin da ya samu har makarantar allo yake da ita a gidansa, wadda shi yake karantarwa a duk lokacin da yake gida, idan bai je wajen yawon kiɗinsa ba, ko kuma bayan ya dawo. Amma bayan rasuwarsa ba a cigaba da karantarwar ba saboda shi ne malamin kuma ya rasu!

Kasancewar a wancan lokacin ana ƙyamar boko ya sa makaɗa Alu wato mahaifinsa bai sa shi a makarantar boko ba, amma dukan abokansa suna yin karatun bokon, sai suka riƙa koya masa a lokacin da suka dawo daga makarantar har ya iya karatu da rubutun Hausa.

Yaran Ɗankurma Maru wato ‘yan amshinsa guda goma sha biyu ne kuma mafi yawa jininsa ne (ko dai ‘ya’yansa ko ƙannensa ko kuma jikokinsa) daga cikinsu biyar ƙannensa ne uwa ɗaya uba ɗaya. Ga sunayensu kamar haka:

1.                  Gado Marke

2.                  Mani Dange

3.                  Hamza Ɗanduna

4.                  Ɗandange

5.                  Abu Rankancam.

 

Biyar daga cikinsu ‘ya’yansa ne na cikinsa waɗanda ko da suka tashi sun tarar da shi yana kiɗa, su kuma sun haɗa da:

1.                  Nuhu

2.                  Murtala

3.                  Alhasanu

4.                  Adamu Dila

5.                  Umar.

 

Sauran biyu daga cikin ‘yan amshinsa jikokinsa ne kodayake ba su dade suna biyarsa wajen waƙa ba sai Allah ya karɓi abinsa, amma dai har yanzu suna bin iyayensu wajen kiɗin. sunayensu su ne:

1.                  Haruna Mani Dange

2.                  Shehu Adamu.

A halin yanzu Mani Dange ne ke jagorantar ƙungiyar waƙar tun bayan rasuwar Alhaji Abu Ɗankurma Maru wato mahaifin nasa.

Rasuwarsa

Bayan dawowar su Alhaji Abu Ɗankurma Maru ne daga wata gayyata da aka yi masu a Sakkwato a shekara ta dubu biyu (2000) wajen wani bukin ɗaurin auren alhaji Shehu Sakkwato wanda shi ne babban jami’in bincike na jihar Sakkwato (Auditor general) sai ya kamu da wata rashin lafiya wadda ta zama sanadiyyar mutuwarsa. Ya rasu ne a ranar alhamis ashirin da biyu ga watan goma sha biyu shekara ta dubu biyu miladiyya, (wato 22/12/2000). Allah ya jiƙansa da rahamarsa amin.



[1]  An samo wannan bayani ne daga kundin digirin Aliyu Ashiru Maru, wanda ya yi a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a shekarar 2008.

Post a Comment

0 Comments