Wakokin Noma Na Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Waƙoƙin Noma Na Alhaji Musa Ɗan’ba’u Gidan Buwai

    Waƙoƙin Noma Na Alhaji Musa Ɗan’ba’u Gidan Buwai

    An haifi Musa Ɗanba’u a shekarar 1957 a wani ƙauye da ake kira Gidan Buwai, wanda ke a ƙaramar hukumar mulkin Raɓah ta cikin jihar Sakkwato. Ya tashi a wannan garin nasu ne na Gidan Buwai har zuwa girmansa a ƙarƙashin kulawar mahaifinsa mai suna Abu Mai ɗan jaki. Ya yi karatun muhammadiyya  gwargwadon hali tun yana ɗan ƙarami.

    Mahaifinsa wato Abu Mai ɗan jaki makaɗin goge ne, don haka muke iya cewa ya gaji kiɗa da waƙa ne gareshi. Ya fara kiɗa da waƙa tun a lokacin da yana ɗan saurayi. Da farko ya fara da kiɗan kokowa/kokawa har zuwa ƙarshe-ƙarshen shekarar 1970, inda ya gwama kiɗin da kiɗin sauran jama’a da kuma kiɗe-ɗiɗen siyasa da na sarauta. Wannan harkar ta kiɗin ya cigaba da ita har zuwa ƙarshen rayursa.

    Kusan duk garuruwan ƙasar Hausa babu inda bai sa ƙafarsa ba wajen waƙa, kuma ya yi wa kowa da kowa waƙa tun daga malamai da sarakai har ‘yan siyasa. Hasali ma tauraruwarsa ta fara haskawa ne a lokacin siyasar jamhuriya ta biyu. 

    Musa Ɗanba’u Gidan Buwai yana amfani ne da kalangu wajen kiɗinsa, da kalangun ne ya yi wannan waƙar noman da sauran waƙoƙinsa. Ita ma ya yi ta ne domin ya yi kira ga mutane da su dawo da hankalinsu wajen noma. Ya rasu a lokacin da yake da shekaru 58 a ranar Talata 07/04/2015. A sakamakon wata gajeruwar rashin lafiya. Ga mashahuriyar waƙar tasa:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.