Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Waƙoƙin Noma Na Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun
Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya fara da zama makaɗin noma ne kafin ya zama makaɗin sarauta da na sauran jama’a. yana amfani da gangar noma ne wajen kiɗinsa ba kotso ba, amma dai an ce ya maimaita wasu waƙoƙin ta amfani da kotson.
Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun
An haifi Musa Ɗanƙwairo a shekarar 1907 a garin Ɗankado ta Bakura wanda ke tsakanin Bakura da Sokoto, akwai tazarar kilomita 105. Sunan mahaifinsa Usman Ɗanƙwanugga. Shi Usman Ɗanƙwanugga asalinsa mutumen garin Ɗankado ta ƙasar Bakura, saboda jituwarsu da sarkin ƙaya sai ya dawo garin Maradun da zama, ya rayu a ƙaya ne kuma yana yi wa sarkin ƙayan Maradun waƙa, Mahaifin Ɗanƙwairo da kakansa duk makaɗan Sarkin ƙayan Maradun ne. Musa Ɗanƙwairo ya tashi ya tarar da kakansa da mahaifinsa suna waƙa tare, amma ya fi rayuwa da mahaifinsa rayuwa ta haƙiƙa. Kuma tun yana ɗan shekara 6 zuwa 7 mahaifinsa yake zuwa da shi a cikin tsangaya ta waƙa, saɓanin irin su Ɗandada Aliyu mai-taushi da Na-rambaɗa da gaba ɗaya ba sa zuwa da ‘ya ‘yansu, su sun ɗauki waƙa ƙaddara ce ta shigar da su shi ya sa ba sa son ‘ya’yansu su gaje su.
Bayan rasuwar mahaifinsa sai ƙungiyar waƙar ta dawo hannun Aliyu Kurna wato yayan Ɗanƙwairo kenan, shi kuma Musa Ɗankwairo aka zaɓe shi ya zama mataimakin Aliyu Kurna, idan Aliyu Kurna ba ya nan sai Ɗanƙwairo ya zama shi ne shugaban tawaga.
Ya samu wannan laƙabi na Ɗanƙwairo tun lokacin da mahaifinsa na da rai. Mahaifinsa yana da wani yaro wanda ake kira Ɗanƙwairo, saboda yaron zaƙin murya gare shi da kuma ƙwarewa wajen karɓin waƙa, to sai Musa ya riƙa kwaikwayon sa tare da kwaikwayon muryarsa, to da aka ga Musan ya ƙware kamar shi Ɗanƙwairon na asali, sai shi ma ake kiran sa da wannan laƙabi na Ɗanƙwairo.
To da yake shi ma Ɗanƙwairo ya tarar da mahaifinsa ne yana yi kuma bayan rasuwarsa ya ci gaba, to su ma ‘ya’yan nasa babu shakka za su iya yin iyakacin ƙoƙarinsu, amma ba za a iya cewa za su iya ɗaukar matsayin sosai ba saboda kusan sarautun da ake yi wa waƙar sun ɗan yi rauni yanzu, tunda yanzu harkar mulki ta koma ga hannun ‘yan siyasa da sojoji masu mulkin kama karya in sun hau mulki.
Allah maɗaukakin sarki ya yi wa Alhaji Musa Ɗanƙwairo rasuwa a ranar Juma’a 13/9/1991, ya rasu ya bar ‘ya’ya 17 maza 10 mata 7. Mazan sun haɗa da Alhaji Muhammadu da Alhaji Abubakar da Alhaji Abdu da Alhaji Sani (zaƙin murya) da Alhaji Garba da Ummaru (babba) da Muhammadu Balarabe da Malam Musa da Alhaji Ibrahim da kuma Umaru (ƙarami), su kuma ‘ya’yansa mata sun haɗa da Hauwa da Zalihatu da Habiba da Amina (ta farko) da Aishatu da Sa’adatu da kuma Aminatu (ta biyu). Haka kuma a lokacin da ya rasu yana da jikoki 104.
Kafin Ɗanƙwairo ya zama makaɗin fada sai da ya fara zama makaɗin noma, inda ya yi amfani da gangar noma wajen waƙoƙin nasa na noman. Sai daga baya ne ya kasance makaɗin fada da sauran jama’a, inda ya yi amfani da kotso wajen yin sa.
Ga waƙoƙin
noma na Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun kamar haka:
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.