𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Don Allaah Malam, ina son a yi
mini cikakken bayani a kan: Wanene fasiƙi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Cikakken bayani sai manyan Malamai, amma ni ɗan abin da na sani ne kawai zan faɗa:
FASIƘANCI shi ne: Kangarewa ko taurarewa ko ficewa daga
dokokin Ubangiji a fili ƙarara, ma’ana: Duk wanda wata doka ta Allaah a cikin Alƙur’ani ko Sahihiyar Sunnar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ta
je masa, wadda kuma take ƙunshe da wani umurni ko hani, amma kuma sai ta
taurare, ya yi ƙememe, ya ƙi aikata wannan umurnin, ko kuma ya ƙi
nisantar wannan hanin, to ya zama fasiƙi kenan, mai fita daga yi wa Allaah Ta’aala ɗa’a da biyayya.
Malamai sun yarda cewa Fasiƙanci iri biyu ne, kamar
yadda Kafirci da Mushirikanci da Munafunci da Zalunci da Bidi’anci kowannensu
iri biyu ne, akwai babba akwai kuma ƙarami.
Babban fasiƙanci shi ke fitar da mai aikata shi daga
cikin musulunci gaba-ɗaya,
ya shigar da shi cikin tawagar kafirai.
A cikin ƙissar Annabi Adam (Alaihis Salaam) game da
umurnin a yi sujada ga Annabi Adam (Alaihis Salaam) Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:
فَسَجَدُوا إِلَّآ إِبْلِيسَ كَانَ مِنَ الْجِنِّ ، فَفَسَقَ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِ
Sai dukkansu suka yi sujada, sai dai Iblis kaɗai, shi ya kasance daga aljani ne, don
haka sai ya yi fasiƙanci game da umurnin Ubangijinsa
Watau: Sai Iblis (La’anahul Laah) ya kangare, ya
fice daga bin wannan umurnin na Ubangijinsa, kangarewa irin na kafirci, kamar
yadda ya zo a wata ayar:
فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ أَبَى وَاسْتَكْبَرَ ، وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ
Sai duk suka yi sujada in ban da Iblis, ya ƙi kuma
ya yi girman-kai, kuma ya kasance daga kafirai ne.
Amma ƙaramin fasiƙanci wanda bai kai girman babban fasiƙanci
ba, shi kam ba ya fitar da mutum daga musulunci, kamar inda Allaah Ta’aala ya ke magana a kan waɗanda suka yi harama da aikin Hajji sai ya ce:
فَلَا رَفَثَ وَلَا فُسُوقَ وَلَا جِدَالَ فِي الْحَجِّ
To, babu batsa kuma babu fasiƙanci kuma babu jayayya a
cikin Hajji
Haɗa
kalmar fasiƙanci da batsa da jayayya da aka yi a nan ya nuna
ma’anarta ita ce: Saɓo kawai, amma ba babban kafirci mai fitar
da mutum daga musulunci ba.
Don haka, abin da ya ke wajibi a kan kowannenmu
dai shi ne: Ya nisanci dukkan nau’ukan fasiƙanci babba da ƙarami
domin neman samun tsira a Gobe Ƙiyama.
Allaah ya taimake mu.
WALLAHU
A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.