𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Miji ne ya saki matarsa alhali
tana haila har saki uku, ba laifin-tsaye ba na-zaune. To yanzu idan ta gama
wanka za a sanya shi cikin idda ne, ko sai ta ƙara uku?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Saki uku cikin kalma guda ko a mazauni guda
malamai sun sha bamban a kan hukuncinsa. A lokacin da waɗansu suke ganin cewa bai auku ba, waɗansu kuma suna ganin cewa ya auku ne a
matsayin saki uku, wanda kuma babu daman yin kome har sai ta auri wani mijin da
ba shi ba. Amma maganar da muka amince da ita saboda ingancinta ta fuskar
dalilai ita ce: Saki uku a cikin kalma guda yana aukuwa a matsayin saki guda ne
kawai, wanda kuma yana iya yin kome kafin ta gama idda.
Sannan kodayake saki a cikin haila sakin bidi’a ne
a wurin malamai, sai dai duk da haka ya auku, a maganar da ta fi ƙarfi a
wurin malamai. Amma yadda gyaran ya ke shi ne: Ya dawo da ita, ta gama wannan
hailar da take yi, ta sake yin wata. Idan ta gama, watau ta yi tsarki daga
haila ta biyu, sai ya sake ta tun kafin ya kusance ta in ya so, a matsayin saki
na biyu, ko kuma ya cigaba da zama da ita da sauran igiyar aure biyu. Haka ya
zo a cikin mashahuriyar ƙissar Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa).
Watau, ba za ta fara maganar idda ba sai a bayan
ya yi mata saki na Sunnah.
WALLAHU
A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aƘZbZ1Vx
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.