Ticker

Yabon Annabi

 

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Yabon Annabi

 Jagora: To bisimilla Rabbi zan fara waƙa,

 Amshi: To

 Jagora: In yi yabon Rasulu in samu lada

 Amshi: To

 Jagora: Kway yi yabon Rasulu ya bi Allah Ta’ala

 Amshi: To

 Jagora: To daɗa zuciyarsa ta samu tsalki

 Amshi: To

 Jagora: Kaza ta hito da ‘ya’yanta goma,

 Amshi: To

 Jagora: Shaho na faɗin ba ki je da ɗai ba,

 Amshi: To

 Jagora: Annabi ya hito da haske da kyawo,

 Amshi: To

 Jagora: Kowa ya gane shi ya ɗora murna

 Amshi: To

 Jagora: Ke ko kin gane shi kin ɗora kuka,

 Amshi: To

 Jagora: Ba kukan rashin ɗiya niy da shi ba

 Amshi: To

 Jagora: Don ƙamnar Rasulu Manzo fiyayye

 Amshi: To


Post a Comment

0 Comments