Ticker

‘Yan Arewa Mu Koma Gona

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

 ‘Yan Arewa Mu Koma Gona

 

G/Waƙa: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza[1].

 

 Jagora: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza.

 ‘Y/ Amshi: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: ‘Yan Arewa ku koma gona.

: Kar ku yadda da harkab banza.

 ‘Y/ Amshi: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: Mu hwa forojet ta kyauta muna,

: Inda ba mu da titi ta yi, x2

 ‘Y/ Amshi: Don saboda muƙamin noma.x2.

 

  Jagora: Rancem kuɗɗi tare da taki,

: In kana da bukata an bai.x2

 ‘Y/ Amshi: Don saboda muƙamin noma,x2

: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: Sai ka kwashi hura mai nono,

: Sannan ka tadda kanka sama’u,.

 ‘Y/ Amshi: Sannan kake tuna Allah Sarki.

 

Jagora: Mayunwaci ko ibada yay yi,

  ‘Y/ Amshi: Ba zai cika tat a zo daidai ba.

: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: Kowac ce rana na ƙuna,

: To yunwa bat a kokkozai ba

 ‘Y/ Amshi: Ta maida yaro ya koma tsoho.

: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza.

 ‘Y/ Amshi: ‘Yan Arewa mu koma gona

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: Ƙaddamas sidƙi rahamatul bushra,

: Rabban Jalla am kama min,

: Gani nan za ni waƙar aiki.

 ‘Y/ Amshi: Dum manoma su zan jin daɗi,

: ‘Yan Arewa mu koma gona

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: Masu noma ka samun gero,

: Masu noma ka samun maiwa,

: Masu noma ka samun dawa,

: Masu noma ka samun masara.

 ‘Y/ Amshi: Da alkama da buhun shinkahwa.

: ‘Yan Arewa mu koma gona

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: Ko daga Musa hay yaranai,

: In dai damana ta kama,

: Dug gida muka komawa can..

 ‘Y/ Amshi: Mu ɗauki hauya mu koma gona.

 

  Jagora: Dug gida muka komawa can.

 ‘Y/ Amshi: Mu ɗauki hauya mu koma gona.

: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: ‘Yan Arewa ku koma gona

: Kam mu yadda da harkab banza.

 ‘Y/ Amshi: ‘Yan Arewa mu koma gona.

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

 Jagora: Dum mai noma kowanene,

: Ya san su Mai zuma na noma,

: Alhaji Shehu ɗan Ibrahim.x2

 ‘Y/ Amshi: Yadda yai mana ya kyauta man.x2

 

  Jagora: Alhaji Bawa Baturen gona.x2

 ‘Y/ Amshi: Yadda yai mani ya kyauta man.x2

: ‘Yan Arewa mu koma gona

: Kam mu yadda da harkab banza.

 

  Jagora: ‘Yan Arewa mu koma gona

: Kam mu yadda da harkab banza.

 ‘Y/ Amshi: ‘Yan Arewa mu koma gona

: Kam mu yadda da harkab banza.



[1]  Zaman banza ba tare da yin noma bas hi ne harkar banza.

Post a Comment

0 Comments